IBee Assalafiy
Lallai abin alfahari ne da farin ciki a zuciya ganin yadda Khalifofin Sheikh Albaniy Zaria (Rahimahullaah) s**a tsaya tsayin daka wajen cigaba da tafiyar da aiyukan alkhairi da da’awa da Marigayi Sheikh ya assasa.
Bayan rasuwar sa, ba su bari alkhairi da ya fara ya mutu ba, sai s**a ɗauki amanar da ya bari da gaske da amana, s**a cigaba da gudanar da manyan ayyuka da projects da bai samu damar kammalawa ba. Wannan ya nuna tsantsar biyayya, jajircewa da kuma fahimtar muhimmancin da’awa da hidimar addini.
Hakika, wannan aiki nasu shaida ce ta gaskiya cewa sun fahimci manufar Sheikh, kuma suna ƙoƙarin ganin an cika burinsa da yardar Allah. Cigaba da aikin da ya bari ba ƙaramin aiki ba ne, amma sun nuna jarumtaka da himma wajen ɗaukar wannan nauyi.
Muna roƙon Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya saka musu da alkhairi, Ya ƙara musu ƙarfi da basira, Ya sa ayyukansu su zama masu albarka, Ya kuma jikansa Sheikh Albaniy Zaria da rahama mai faɗi, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Address
Zaria