Zaria Daily Post
08/10/2024
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un lallai duniya ba matabbata ba ce, Allah yasan da zuwan ka bawan Allah mutumin kirki na al'umma (Dan isan zazzau) Dan-Isan Zazzau Alh. Umar Shehu Idris.
Zaria Daily Post
31/10/2023
07/10/2022
Wannan ita ce JYOTI AMGE. Yar shekara ashirin da takwas 28 years, saura wata biyu ta shiga shekara ashirin da tara 29 years.
Ta fi kowacce mata kankanta a duniya, gaba daya tsawon ta befi 2ft ba, wato tsawon qafa biyu hakan ya nuna bata kai yaro dan shekara biyu tsawo ba a daidai lissafi na tsayi. Bincike ya nuna bazata kara tsawo ba.
Nauyin ta kuma befi 5kg ba
Ita dai jyoti amge an haifeta 16th December 1993 a Nagpur na kasar India 🇮🇳
Ta shiga cikin littafin guinness book of record na duniya a shekarar 2011, wanda aka tantance ta a matsayin matar da tafi kowace mata gajarta da qanqanta a duniya.
Sabuda yanyin tsawon ta, komai sede a qirqiri daidai nata, kamar kayan sawa da sarka da su awarwaro. Hatta chokalin ta da farantin cin abincin ta daidai nata ake yi, sabuda bazaa ta yi amfani da na yara ba tunda ba yarinya bace, sanan kuma babu na manya daidai ita, duk sun mata girma, to saida a mata nata a kampani.
Ta shiga makaranta tun tana da shakara hudu a duniya 4 years, tayi makarantu kala kala, sede ana mata kujera da table daidai ita, amma yanda ake yiwa kowani dalibi dan shekarunta haka ake mata.
Kamar dai yanda yanmata suke son ado da kwalliya, rike waya me kyau, haka ita ma jyoti amge take.
Bata da wani mafarki kamar tazama yar wasan kwaikwayo kuma burin ta ya cika.
Likitoci sun bayyanar da dalilin rashin tsawon ta, sabuda wata chuta da ake kira primordial dwarfism.
A wannan shekarun nata har yanzu ko qirgen dangi bata fara ba b***e Al’ada.
Fatana gare ta Allah kawo miji na kwarai🙏
Wani fata zakuyi mata?
Sannan
Wai ita wannan me zaa kira ta? wada ce ko qanwar wada?
Fulani maryam
6/10/2022
02/10/2022
ABINDA YA FARU GA SIYAMA MAI SHEKARU 3 A DUNIYA
Siyama ta rasu ranar Alhamis 29-09- 2022 kimanin karfe 4 na yamma a dalilin Fyade da wanda ake tuhuma wani Idi (Baba Idi) mai shekaru kimanin 40 zuwa sama, dake Zaune a Lungun Alhaji Halliru a unguwar Gama, karamar hukumar Nassarawa ya yi mata ranar Talatar da ta gabata.
Kimanin kwana shida da ya gabata, Idi ya dauki Siyama zuwa dakinshi ya bata alewa inda ya yi lalata da ita kuma ya tsoratar da ita cewa in dai ta fadawa Abbanta sai ya kasheta da Almakashi kuma ya hadata da magen gidansu ta cinyeta (kasancewar ta mai tsoron mage) ta kwatanta mana yadda ya dora mata almakashi a wuya yace sai ya yankata da shi idan ta fadawa Abbanta.
Bayan ta shigo gida an cire mata kaya za ayi mata wanka aka ga jini yana fitowa daga jikinta, aka ce me ya sameta tace "Baba Idi ne yake mun wani abu yauma ya ciremin wando ya yi min ya bani alawa kuma yace idan na fadawa Abbana ze kasheni, Umma don Allah kar ki fadawa Abba". Daga nan aka dauketa aka kaita asibiti inda likitoci s**a tabbatar da 'Pe*******on' kuma s**a fadi hanyoyin da za a bi a kula da lafiyarta.
Bayan jami'an tsaro sun kamashi an kaishi CIID ana cikin bada statement aka fito dashi da ankwa, tana ganinshi ta rude da firgici tana cewa "Umma yace kasheni zai yi da Almakashi, me yasa ki ka fadawa Abba? Kasheni ze yi kuma ze hadani da mage" daga nan zazzabi ya kamata aka dawo da ita gida, har zuwa washe gari da ta rasu tana ta maimaita kasheni zeyi da Almakashi.
Yau kwanan Siyama uku da rasuwa sakamakon Zalunci da cin zarafin da wannan la'anannen Allah ya yi mata, Allah ya gafarta mata yasa mai ceton iyaye ce shi kuma Allah ya kare Al'umma da sharrin mutane irinsa yasa ya girbi abinda ya shuka.
Ga hotunan Siyama nan a kasa.
Daga Bilya Abubakar Muhammad
14/09/2022
Guguwa da Goyon Jariri, Jama'a Don Girman Allah Mu Taimaka Wannan Mata Ta Samu Keken Guragu
Don Allah duk mai hali ya taimakawa wannan baiwar Allah wadda gurguwa ce, tana da yara biyu, yaro namiji yana da shekara biyar shi yake rike kanwar sa duk inda mamar za ta tafi.
Don Allah idan akwai wanda zai iya taimaka mata da keken guragu, tana a garin Maiduguri ne.
Duk mai neman karin bayani akan ta zai iya kiran wadannan lambobin;
07031203022
08067620342
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
No 10 Zaria City
Zaria
KOFANDOKA