Taskar Arewa TV

Taskar Arewa TV

Share

26/06/2026

Breaking news!!! Breaking news!!!

English version:
Chief of Staff to President Bola Tinubu, Hon. Femi Gbajabiamila, has said the Federal government will review the minimum wage of government workers to meet up with the current economic situation when the time comes.

Hausa version:

Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa ga Shugaba Bola Tinubu, Hon. Femi Gbajabiamila, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta sake duba mafi ƙarancin albashin ma'aikatan gwamnati saboda ya dace da halin tattalin arziƙin da ake ciki a wannan lokacin..

Taskar Arewa TV

Follow, like, comment and share

Photos from Taskar Arewa TV's post 26/06/2026

Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo tare da tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin Shugaban Ƙasa a jam'iyyar NDC Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da kuma ɗan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar Comrade Aminu Abdulssalam Gwarzo a daren jiya a Kano, a ziyarar aiki da Obasanjo ya kai jihar inda s**a hadu domin su gaisa tare da tattaunawa kan lamuran siyasa da ci gaban ƙasa.

Taskar Arewa TV

Photos from Taskar Arewa TV's post 19/06/2026

Mai Girma Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar SAN Ya Gana da Mai Girma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa dake Babban birnin tarayya Abuja.

​Mai Girma Mohammed Abdullahi Abubakar, SAN, tsohon Gwamnan Jihar Bauchi kuma Dan Takarar Gwamna na jam'iyyar APC, a yau tare da Daya daga cikin jigogin jam'iyyar na jiha, Farfesa Muhammad Ali Pate, Mai Girma Ministan Lafiya da Jin Dadin Jama'a na Kasa, sun gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

​Wannan muhimmiyar ganawa ta mayar da hankali ne kan batutuwan da s**a shafi kasa, ci gaban Jihar Bauchi, da kuma al'amuran da s**a shafi ci gaba da jin dadin jama'a. Haka kuma, tattaunawar ta mayar da hankali kan karfafa shugabanci na gari, inganta ci gaba mai dorewa, da kuma ciyar da tsare-tsaren da za su taimaka wa ci gaba da habakar Jihar Bauchi da ma Najeriya baki daya.

​Ganawar ta nuna irin jajircewar shugabannin wajen dorewar tattaunawa da hadin gwiwa domin mara baya ga sabon tsarin (Renewed Hope Agenda) da kuma burikan 'yan Najeriya baki daya.

​Shamsuddeen Lukman Abubakar
Ya rubuta cikin Harshen turanci.

Moh'd Alkasim ya fassara zuwa Harshen Hausa.

19/06/2026

Taskar Arewa TV

17/06/2026

Shahararran mawaki a Kudancin Najeriya Davido ya bayyana cewa da Rarara na da Ilimi da sai ya tsaya ya yi magana dashi.

Ya Kuma bayyana Dauda Kahutu Rarara a matsayin sakarai wanda bai San komai ba. Hakan dai na zuwa ne sa'oi kadan bayan mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya caccaki Davido a shafinsa na Facebook.

Davido ya bayyana hakan ne a shafinsa na X Wanda a baya aka fi sani da twitter.

Me za ku ce?

Taskar Arewa TV

17/06/2026

Da ɗumi-ɗumi: Ana tsaka da shari’a Bayan hukumar DSS sun kai Sowore Kara kotu kan kiran Tinubu da kalmar Criminal Sowore Yanzu Ya Sake kiran Tinubu “Ɗan Ta’adda” kuma ɗan bindiga A Zanga-Zangar Rashin Tsaro.

Dan gwagwarmayar siyasa kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, ya sake tayar da kura bayan ya kira Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sunan “ɗan ta’adda” yayin wata zanga-zangar nuna rashin jin daɗi kan matsalar rashin tsaro a Najeriya.

A cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Sowore ya bayyana cewa dalilin da ya sa yake ganin dole ne Shugaba Tinubu ya sauka daga mulki shi ne saboda, a cewarsa, shugaban “ɗan bindiga ne, ɗan ta’adda ne kuma ɗan rashawa ne.”

Kalaman na Sowore sun sake haifar da cece-kuce a tsakanin ‘yan Najeriya, musamman duba da cewa tuni yake fuskantar shari’a da Hukumar Tsaro ta DSS kan wasu kalaman da ya yi a baya inda ya bayyana Shugaba Tinubu da sunan “criminal” (mai laifi).

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa ko DSS kan sabbin kalaman da Sowore ya yi.

Shin waɗannan kalamai za su ƙara jefa Sowore cikin wata sabuwar matsala ta shari’a? Lokaci ne kawai zai bayyana hakan.

Taskar Arewa TV

Want your business to be the top-listed Media Company in Wuse?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Wuse