Alancy Comedy Tv

Alancy Comedy Tv

Share

Photos from Alancy Comedy Tv's post 21/02/2026

muna rokon Allah Duk wata rahama da gafara da jin ƙai da farin ciki da jin daɗi dayake rabawa s wannan wata me albarka na Ramadana Allah kasamu acikin sa Allah kabamu 🤲 Allah ka amsa muna ibadummu ya hayyu ya qayyum 🤲

16/01/2026

AN BAR AREWA A BAYA

Matatar sarrafa Zinare ta fara aiki a jihar Lagos, yayin da masana’antar Lithium ta dala miliyan 600 kimanin Naira Biliyon dari tara ke dab da fara aiki duk a jihar Lagos

Kar a manta fa, Zinaren nan daga Arewa za'a dinga diba ana kaiwa Lagos domin a sarrafashi a can, me yasa ba za'a gina masana'antar anan Arewa ba? ba laifin kowa bane laifin mutanen Arewa ne

Sannan kamfanin sarrafa sinadaren Lithium da za'a gina a Lagos shima daga Arewa ne za'a dinga diban sinadaran ana kaiwa Lagos domin a sarrafashi, ana amfani da sinadarin Lithium wajen kera makamai masu linzami, batira da gilasai da kera magunguna masu warkar da cutar kwakwalwa

Jama'ar Arewa kun dai ga yanda Yarbawa suke ta gina yankin su ko domin su tsaya da kafafunsu?
Kun dai lura da yanda suke ta karkatar da arziki zuwa wurin su, don su gyara tsarin rayuwarsu?

A yankin Arewa da suke da ma'adinan ya kamata a gina kamfanonin, amma ina, an barmu da su Bello Turji da 'yan B0k0 Har@m/ISWAP da rikici akan banbancin akida na addini da bakin ciki da hassada wa juna

Marigayi Sheikh Albaniy Zaria yace ba sai an raba Nigeria za'a nakasa Arewa ba, idan an bar Arewa da matsalar tsaro kadai shikenan, kudin da ya kamata a gina Arewa dashi sai aka sa don maganin tsaro, to shikenan yankin ba zai cigaba ba

Tabbas makomar Arewa tana hannun mutanen Arewa, sai mun yi hankali mun gyara kafin mu samu mafita

Allah Ya sa mutanen Arewa mu hankalta mu gyara

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Wuse II?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Wuse Ii