BIN ALI

BIN ALI

Share

05/06/2026

KA TAƁA TUNANIN DALILIN DA YA SA AKE BA DA SHAWARAR A YI GWANIN LAFIYA KAFIN AURE?
Aure wani babban mataki ne na rayuwa da ke haɗa mutane biyu domin gina iyali mai cike da farin ciki da kwanciyar Sai dai kafin a shiga wannan tafiya, yana da muhimmanci a san matsayin lafiyar juna domin kauce wa matsalolin da za su iya tasowa a gaba.

Yin gwajin lafiya kafin aure na taimakawa wajen gano wasu cututtuka ko matsalolin lafiya da mutum zai iya ɗauke da su ba tare da ya sani ba. Daga ciki akwai genotype, cututtukan hanta (Hepatitis), HIV, matsalolin haihuwa, hawan jini, ciwon s**ari da sauran matsalolin da ka iya shafar rayuwar ma'aurata ko lafiyar 'ya'yan da za su haifa.

Sanin waɗannan bayanai tun kafin aure ba yana nufin a rabu da juna ba ne, a'a yana ba ma'aurata damar yin shiri, neman shawarar likitoci, da ɗaukar matakan kariya da s**a dace domin kare kansu da iyalinsu a nan gaba.

Iyali mai ƙarfi yana farawa ne da kyakkyawan shiri, kuma lafiya na daga cikin muhimman ginshiƙan wannan shirin. Kada a bari soyayya kaɗai ta jagoranci yanke hukunci; a tabbatar an haɗa da kula da lafiya domin rayuwar aure ta kasance cikin aminci da kwanciyar hankali.

💙 Gwajin lafiya kafin aure ba alamar rashin yarda ba ce, alama ce ta wayewa, kulawa da kuma son ganin an gina gida mai ɗorewa.

Want your business to be the top-listed Advertising & Marketing Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Kano