ECWA DAILY

ECWA DAILY

Share

18/01/2026

LITININ, 19 GA JANAIRU
NASSI: RUT 1:19-22

KAN MAGANA: DAGA YALWA ZUWA RASHI

RUT 1:19-22

19:Su biyu kuwa s**a k**a hanya har s**a isa Baitalami. Da s**a isa Baitalami, sai dukan garin ya ruɗe saboda su. Mata s**a ce, “Na'omi ce wannan?”

20:Ita kuwa ta ce musu, “Kada ku kira ni Na'omi, wato mai farin ciki, sai dai Mara, wato mai baƙin ciki, gama Mai Iko Dukka ya wahalshe ni ƙwarai.

21:Na tafi a wadace, ga shi, Ubangiji ya komo da ni hannu wofi. Don me kuke kirana mai farin ciki da yake Ubangiji Mai Iko Dukka ya wahalshe ni, ya kuma aukar mini da masifa?”

22:Haka Na'omi ta koma daga ƙasar Mowab tare da surukarta Rut, mutuniyar Mowab. S**a isa Baitalami a farkon kakar sha'ir.

DAGA YALWA ZUWA RASHI

Naomi ta koma Bai’talami tare da Ruth bayan shekaru da yawa a Mowab, suna fuskantar hasara da rashi.

Ta nemi a kira ta Mara, hakan ya nuna bacin ran ta a cikin mummunan asarar da ta yi.

Labarin Naomi ya ƙarfafa mu mu dogara ga Allah a cikin yanayi mai wuyar gaske.

Kuka na iya kasancewa har dare, amma farin ciki yana zuwa da safe.

TAMBAYA:
Shin kana jin ba kome ko kuma kana da wata boyayya da Allah?

ADDU’A:
Ka ba ni alherin da zan magance rikici ta hanyar da za ta girmama ka. Amin.

ABINCIN YINI - 2026

16/01/2026

ASABAR, 17 GA JANAIRU
NASSI: RUT 1:6-14
KAN MAGANA: DANGARTAKAR SURUKAI

RUT 1:6-14

6:Daga can Mowab, Na'omi ta ji cewa, Ubangiji ya taimaki mutanensa, ya ba su abinci, sai ta tashi daga ƙasar Mowab tare da surukanta.

7:S**a k**a hanya zuwa ƙasar Yahudiya.

8:Amma a hanya, sai Na'omi ta ce wa surukanta, “Bari ko waccenku ta koma gidan iyayenta. Ubangiji ya yi muku alheri k**ar yadda kuka yi mini alheri, ni da marigayan.

9:Ya sa kuma ko waccenku ta yi aure, ta sami hutawa a gidan miji.” Sa'an nan ta yi bankwana da su ta sumbace su. Sai s**a fashe da kuka,

10:s**a ce mata, “A'a, mā tafi tare da ke wurin mutanenki.”

11:Amma Na'omi ta ce musu, “Ku koma, 'ya'yana, don me za ku tafi tare da ni? Ina da sauran 'ya'ya maza a cikina ne da za su zama mazajenku?

12:Sai ku koma, 'ya'yana, gama na tsufa da yawa, ba kuma zan sami miji ba. Ko da a ce ina fata in yi aure, a ce ma zan yi aure a daren nan, in haifi 'ya'ya maza,

13:za ku yi ta jira har su yi girma? Ai, ba zai yiwu ba, 'ya'yana. Ina baƙin ciki ƙwarai saboda abin da ya same ku, da yadda Ubangiji ya yi gāba da ni.”

14:S**a sāke fashewa da kuka. Sai Orfa ta yi wa surukarta, sumba, ta yi bankwana da ita, amma Rut ta manne mata.

DANGARTAKAR SURUKAI

Dangantakar surukai mai tsami ta zama ruwan dare, duk da haka dangantajar Na’omi da surukanta Mowabawa, ta zama abar yabawa.

Duk da bambancin al’adu, haɗin kansu yana da ƙarfi.

Addu’ar da Na’omi ta yi wa surukanta ta nuna kauna da hadin Kai.

Surukai za su iya zama abokan tarayya masu ƙarfi.

TAMBAYA: Yaya zaki ƙwatanta da dangantakar ki da surukanki?

ADDU’A: Ya Ubangiji, ka nuna jinkai wajen kyautata danganta ta da surukana. Amin.

ABINCIN YINI - 2026

16/01/2026

FRIDAY, 16 JANUARY
TEXT: RUTH 1:1–5
TOPIC: TRANSFORMED BY TRAGEDY

RUTH 1:1–5 NIV

1:In the days when the judges ruled, there was a famine in the land. So a man from Bethlehem in Judah, together with his wife and two sons, went to live for a while in the country of Moab.

2:The man’s name was Elimelek, his wife’s name was Naomi, and the names of his two sons were Mahlon and Kilion. They were Ephrathites from Bethlehem, Judah. And they went to Moab and lived there.

3:Now Elimelek, Naomi’s husband, died, and she was left with her two sons.

4:They married Moabite women, one named Orpah and the other Ruth. After they had lived there about ten years,

5:both Mahlon and Kilion also died, and Naomi was left without her two sons and her husband.

TRANSFORMED BY TRAGEDY

Ruth’s story unfolds during a time of crisis in ancient Israel. Famine forces Elimelek and his family to Moab.

After experiencing multiple tragedies, Naomi loses her husband and sons, leaving her to wonder why God allowed such suffering.

Yet trials are part of life; Peter reminds us not to be surprised by difficulties. Tragedies lead us to depend on God.

QUESTION: What hardships have led to your most significant growth?

PRAYER: Help me focus on your plan, Lord, not my pain.

Food for the Day - 2026

Want your place of worship to be the top-listed Place Of Worship in Suleja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Suleja