Imamiyya

Imamiyya

Share

01/12/2025

YAUSHE AKA DAUKI MATAKIN?

Da farko k**ar kullum ban cika son yin magana kan irin wadannan abubuwan da ke faruwa ba, amma taba janibin jagora abu ne da bai k**ata ayi shiru a kansa ba. Duk da haka na yi kokarin kaucewa yin magana don abinda ke iya zuwa ya komo, amma wani bawan Allah da yayi rubutu a kokarinsa na barranta Shaikh Yakubu Yahaya daga wannan rubutun shi ya tilasta ni ba don ina so ba ince wani abu. A kan haka nake rokon Allah (T) ya sa Yan uwa su mini kyakykywan fahimta, su fahimci sakon da nake son isarwa da budadden zuciya, su fahimci manufan rubutun nan ba jinginawa Shaikh Yakubu ko wani alhakin rubutun da Abu-Taliyyah yayi ba ne, su fahimci manufan rubutun shine gamsar da wani bawan Allah da ya yi rubutu da nufin kore hannun Malam Yakubu daga Abu-Taliyyah cewa hujjojinsa ba gamsassu bane.
Audio da ya kawo na saurari audion amma kuma banga alakansa da abinda ya faru ba, a cikin Audio din Shaikh din yana kokarin kore abubuwa da ake jingina masa na yabo ne, yana nuna shi matsayinsa bai kai nan ba, wannan Shaikh ya sha magana a kai musamman da yake duk wanda ya san shi, ya san yana da tawadhi'u k**ar yadda mai rubutun yace haka yaran suke fada in ya kobe su a kan sakin bakinsu da sukeyi. Wannan kadai zai nuna maka cewa ana taka musu birki ne a kan abinda ya shafi abinda Shaikh din yake gani sun kai shi matakin da bai kai bane kawai, kuma duk misalan da shi wannan bawan Allah ya kawo a kan su ne k**ar cewar wata rana yaran su na fadin Labbaika Ya Shaikh Yakubu, take ya taka musu birki ya ce musu nima Labbaika Ya Elzakzaky nake cewa. Bama haka ba duk hujjojin da mai rubutun ya kawo har da audio din ba abinda suke magana a kai illa kokarin Shaikh din wajen kore jingina masa matsayin da shi yake ganin bai kai shi ba. Babu wani abu banda wannan.
Alhali abinda ake magana a kai kuma shine a kan yaran da suke yima Shaikh din biyayya su na taba janibin Jagora da iyalan Jagora amma ba a taba jin Shaikh din ya yi jawabi a kan su ya barranta kansa da su, ya kuma nuna bacin ransa a kan abinda s**a yi, bare kuma ya kiraye su a kan lalle su tuba su sake rubutu su nemi gafaran Yan uwa. Babu yadda za a tuhumeka da rashin Akhlak sai wani da yake son wankeka ya kafa hujjah da cewa kai mai ilimi ne, ka koyar a waje kaza, yayi ta kawo hujjoji a kan iliminka. In an tuhumeka a kan rashin Akhlak sai wani yana son wankeka k**ata yayi ya kawo hujjoji ne a kan yadda kake muamala da mutane, da yadda mutane suke yabon hakayenka da sauransu ba ya buge da kawo hujjoji kan iliminka ba, in yayi haka bai gamsar da masu tuhuma ba. Kamar haka ne wannan rubutun ba yadda zai gamsar da masu tuhuma. In ana son gamsar da masu tuhuma to wajibi ne a kawo audio inda da aka taba janibin Jagora Shaikh din yayi jawabi ya nuna bacin ransa har kuma ya barranta kansa da masu s**an, kuma da misalan matakan da Shaikh din ya dauka. In anyi haka to tabbas za a gamsar da masu tuhuma.
Masu tuhuman nan cewa sukeyi wadannan yaran masoyan Shaikh ne na sosai kuma suna s**an nasun ne ma don kare Shaikh din. Cewa sukeyi idan mutum masoyinka ne ya san kana son babanka babu yadda zai koma yana s**an babanka da iyalan babanka sannan ya dawo ya zauna tare da kai, dolensa in dai ya san har yanzu kana tare da baban naka baka bar shi ba, to sai dai ya yaba mishi, in ma yaga wani abu na ba daidai ba a tare da baban naka, ba zai yarda yayi maganan a fili inda ya san maganan zai koma maka ba, sai dai yayi s**ansa a boye. Amma in zai fito a duniya ya soki babanka kai tsaye sannan washegari a gan shi a gunka kuna tare dole Yan uwanka su yi zargin anya kana son baban nakun nan kuwa. Za su ce in kana son sa to fa dole ko wanda ya soki babankun yayi mursusi yazo wajenka za ka koreshi, don ba masoyinka bane.
Cewa masu tuhumar suke yi me ya sa ba aji daga sauran amirai masu son su suna taba janibin Jagora da iyalansa ba sai mabiya Shaikh din? Cewa sukeyi ai sauran amiran ma akwai yan gani kasheninsu amma ko kusa ba a taba jin wani ya soki Jagora ko iyalan Jagora ba, saboda sun san malamin nasu ba zai taba barinsu ba, sannan kuma ma kullum yana dora su ne a kan bin Jagora da girmama iyalansu, shi ya sa ba za su iya suna masoyan amiri din kuma suna s**an Jagora ko iyalan Jagora ba.
Cewa sukeyi su ba sun ce Shaikh ne yake saka su ba, amma kuma wajibi ne ga Shaikh in akwai son Jagora ko da digo daya ne a ransa ya fito ba sai an yi ta kiraye kiraye ba ya nuna bacin ransa ga maganan da sukeyi ya barranta da su, ya ambaci sunansu ya fada cewa daga yau ba shi ba su in har ba su tuba ba, in yayi haka gobe wani ba zai sake yin mak**ancin hakan ba daga cikin masoyansa.
Cewa sukeyi a baya Hamza Lawan da haka aka fara, almajiransa masu nuna masa soyayya sosai su s**a fara s**an Jagora, a lokacin Hamza Lawan baya hana su, anyi ta kiraye kiraye a kan lalle in ba ya tare da su to ya hana su, Amma shiru shima sai dai a kafa hujjah da cewa ai ba shi yakeyi ba kuma ba ya tare da raayin su alhali kuma ana ganinshi tare da su, aka gagara gane hikiman cewa ba ka tare da raayin masu s**an malaminka alhali kuma su masoyanka ne za su soki malaminka kuma su kasance da kai, baka taba barranta kanka da su ba, baka taba hana su ba amma kuma kana cewa kai almajirin malamin da suke zagin ne. Wace kwakwalwace za ta iya yarda da hakan. Haka aka yi ta yi shi Hamza Lawan din bai hanasu ba ba a ji a bayyane yayi zagin ba shi, bai kuma hana su zagin ko rabuwa da su ba. A lokacin an tuhumi Hamza Lawan da cewa shima yana da raayin zagin don in ba sun san yana da raayin hakan ba da ba yadda masoyansa za su zagi masoyinsa jagoransa, don a bayyane yake makiyin masoyinka makiyanka ne, in kuma ka dauki makiyin masoyinka a matsayin masoyinka to tabbas a bayyane yake ka dawo makiyin wannan da ya kasance masoyin nakan. A karshe me ya faru? Hamza Lawan ya bayyana ya bi sahun almajiran nasa na yin zage zage ga Jagora.
A kan wadannan tuhume tuhumen mai rubutun ya k**ata ya kawo hujjojinsa ba kan tawadhi'un Shaikh ba.

- Miji Naseer -
13/03/2025

Photos from Imamiyya's post 28/10/2024

JAGORA YA RUFE TADRIB NA ƳAN UWA MATA A ABUJA

Daga Ofishin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)

Da yake jawabin rufe Tadrib, wanda ƴan uwa mata na Harkar Musulunci s**a gabatar na kwanaki biyu a Abuja, a ranar Lahadi 24 ga Rabi’ut Thani 1446 (27/10/2024), Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya jawo hankali akan manufar shirya irin waɗannan tarurrukan.

Yace: “Manufar irin wannan taron shi ne kwakkwafe tunani, don shi mutum wanda Allah Ta’ala Ya saka masa hankali da tunani, to yana bukatar kuma a rika kwakkwafa masa, a rika tunatar da shi a na masa ‘taujihi’ a ko da wane lokaci, don in ba haka ba, sai ya manta, ko kuma ya yi sanyi.”

Shaikh Zakzaky ya bayyana tunatarwa a matsayin muhimmin abu, wanda za a yi ta maimaita yinsa ga mutum. Inda yace, hatta Alkur’ani an kira shi da haka ne saboda abu ne wanda ake yawan maimaita shi. “An kira shi da Qur’an, ma’ana ‘sha-karatu’, (saboda abu ne da za) ai ta karanta shi. Kullum ka karanta Alkur’ani, za ka ji k**ar sabon abu kake ji, gashi abu daya ne, yana da iyaka daga bango zuwa bango, da adadin surori da ayoyi, amma kullum sabo yake zama, kullum tunatar da mutum yake yi, kullum kuma wanke masa zuciya yake yi, ya kwantar masa da zuciya, (don haka) kullum (mutum) yana bukatan ya karanta Alkur’ani.”

Jagora ya bayyana takaicinsa akan yadda yanzu makiya addini kullum suke yawo da hankulan mutane, da yin hujumi akan al’umma ta hanyar abin da ake kira ‘software’ da kuma ‘hardware’. Inda ya bayyana mak**an makiya na ‘hardware’ a matsayin mak**an da suke jefawa su kashe mutane k**ar yadda suke yi a Palasdinu da Lebanon, a yayin da mak**an ‘hardware’ din makiya shi ne tura ma al’umma wadansu miyagun tunaninnika.

Yace: “Don mu tunatar da junanmu da’iman, mu gane cewa, muna fa gidan gwaji ne, mun fito ne daga Allah, za mu koma izuwa ga Allah, matsayinmu a nan doron kasa na zaman gajeren lokaci, lokaci ne na gwaji, na ‘yan shekaru ‘yan gomomi, ba a daruruwa, don in mutum ya kai dari ma za ka ga yana zaune ne kawai amfaninsa qalilan ne, amma gomomin (shekaru) ne qalilan kuma, in s**a kai shida, bakwai, takwas, shikenan, iyakanta kenan ‘yan shekarun gwajin, a gwada ka a doron kasa a ga me za ka yi, sannan ne za a gane wane makoma za ka koma a rayuwar da bai da iyaka.”

Ya cigaba da cewa: “Gida biyu ne komawa ga Allah; imma wuta, imma Aljanna. Saboda haka, (ka yi kokari ka ga) me ka aikata a wannan rayuwar? Yana da kyau ka san kai me ya kawo ka? Kai me kake yi? Kuma ina za ka? Me ya kawo ka nan (duniya), ina za ka? To me ya k**ata ka yi domin inda za ka?

“Wannan shi ne abin da ya kawo mu nan, kuma shi yasa wadanda s**a san wannan, s**a san cewa su sun zo gidan gwaji ne, za ka ga sun dage suna abin da ya k**ata su yi ne a rayuwarsu don su tsira gobe kiyama. Wadanda basu san haka nan ba kuwa, su sun dauka an zo ne a rayu a more a ji dadin rayuwar, shikenan, illa iyaka kenan.”

Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “Su wadanda suke fada da mu, galibansu basu tunanin makoma, sam basu san da wannan makoman ba, suna tunanin iyakanta nan ne rayuwarsu, duniya. Kuma suna tunanin duk da duniyar nan la-muhalata za su barta ne, amma suna jin abin da ya dame su kawai su gina duniya, ko da basu rayu ba ya zama ta rayu ma wasunsu.”

Ya kara jawo hankali da cewa: “(Ya k**ata) ya zama kai akan manufar (zuwanka wannan gidan gwajin) ka rayu, akanshi kake aiki, akanshi kuma za ka bar duniya. Kuma muhimmin abu shi ne, ya karshe ya kasance gare ka? Ya karshenka ya kasance? Ya ka karata ma’ana. Ka yi kyakkyawan karshe? Alhamdulillah. Ka dake akan abin da ka zo akai, ka kuma tsaya kyam? Shikenan.”

Jagora ya tunatar da wata magana da Imam Ali (AS) yake fadawa dansa, cewa: “idan ka tsai da wajibi, ka guji haram, to kar ka damu mutuwa ta fada maka ne, ko ka fada mata ne, duk daya ne.” Ya cigaba da cewa; har Amirulmumin (AS) yake “Dan Abidalib ya fi son mutuwa fiye da yadda jariri ke son nonon uwa.”

Yace: “Saboda mene? Shi yana ganin in ta zo, farkon jin dadi kenan, karshen wahala kenan, shaukinta ake yi, saboda in ta zo karshen wahala kenan. Saboda haka wanda ya san ga abin da ya kawo shi, yake kuma raye a kan wannan, shi baya damuwa, zai tsaya ne kyam, abin da ya dame shi shi ne yaya ya cika? Meye karshensa? Ya yi kyakkyawan karshe, abin da ake so kenan.”

Jagora ya bayyana nasarar mai da’awa a matsayin tsayuwarsa kyam har ya koma ga Allah Ta’ala yana kan abin da yake yi. Yace: “Babu wani Annabin da bai yi nasara ba. Aikin Annabi shi ne isar da sako… Kafa Daula Musulma da iko, in wannan shi ne nasaran Annabi, to da yawan Annabawa ba su yi nasara ba, don su ba su kafa daula ba. Har Abul-Anbiya Ibraheem (AS) bai kafa Daula ba, amma manufarsa kenan kafa daula din ko da bai kafa ba. Haka nan kuma ko wane Annabi ko da bai kafa daula ba, manufarsa (da hankoronsa) kenan ya kafa daula ya zama al’umma ta dauru a kan koyarwar addini. Al’umma ta doru a kan koyarwar addini, wannan wajibi ne.”

Shaikh Zakzaky ya yi martani ga wadanda suke ganin komawa ga addini abu ne da ba zai yiwu ba, kuma ya k**ata a yi shiru a kame baki daga zalunci da barnan azzalumai, inda y aba da misali da Ashabul Sabt da kissarsu ya zo a cikin Alkur’ani mai girma dangane da kamun kifi ranar Asabar, wanda Allah Ta’ala ya hallakar da masu barnan, da wadanda basu yi tare da su ba amma s**a zura musu ido suna yi, sannan ya tseratar da wadanda s**a tsawatar akan hakan.

Ya kuma yi martani ga masu ganin haduwa da azzalumai ne mafita don a kubuta daga cutarwarsu. Inda ya kawo fadin Allah Ta’ala da ke cewa: “Wala tarkanu ilal lazina zalamu fatamassakumun naar.” Yace: “Kar ma ku karkata izuwa ga azzalumai. Karkata kawai! Ba a ce ku zama azzalumai ba, karkata (ma kar ku yi gare su). To amma ace wai ku hada kai tare da su, ku tafi tare da su don ku zauna lafiya, wai dabara ne?” Ya tambaya.

Jagora ya yi dogon bayani akan dalilin kasanewar Annabi Yusuf (AS) da Imam Ridha (AS) a cikin hukumar zamaninsu. Yace: “In ka duba cikin littatafanmu, musamman Imam Khomaini (QS) ya yi doguwar magana akan wannan, kan cewa, za a iya tunkude sharri da jawo alkhairi a karkashin wani azzalumi? Yace, in zai yiwu ka yi wannan, ba tare da kai ma ka taimake shi akan zaluncinsa ba, za ka iya yi.”

Yace: “Amma fakam da yawa ba abin da mutane suke yi ba kenan, suna taimakon (azzaluman) a zaluncinsu ne, sai su fake da Annabi Yusuf ko Imam Ridha (AS). (Alhali su mutanen da suke wannan) tare da azzaluman suke, kuma suna taimako azzaluman ne, kuma gobe kiyama ba za a raba su ba.”

Ya kawo fadin Amiruluminin (AS) da ke cikin Nahjul Balagha, wanda yace ya ji Manzon Rahma (S) yana cewa; “Duk wanda ya ga wani ma’abocin hukuma yana zaluntar al’umma, bai yi amfani da harshensa da hannunsa wajen hanawa ba, to ya sani ya rage ga Allah Ya hada shi da wannan azzalumin ya kai su makoma daya.”

Jagora yace: “Azzalumai ba za su taba kyale ka ba, sai dai in za ka mika musu wuya ne. In ka mika musu wuya ka zama nasu, ka zama kayan sarrafawansu to ya yi daidai (a wajensu), kuma ba ka da daraja a wajensu, ba za ka taba samun daraja a wajensu ba, kuma gobe kiyama tare da su kake ba abin da zai raba ka da su.”

Sannan ya sake jajjada cewa: “Babban nasararmu shi ne kowannenmu ya dake kyam har mutuwa ta same shi. In ya yi hakan ya yi babban nasara. Ba kafa daula ba. Ko da yake hankoron kafa daula ne, amma ba lallai a kafa daulan (mutum na raye) ba. Saboda haka nasararmu shi ne dakewarmu har izuwa karshen rayuwarmu, kuma kowannenmu zai dake ne.”

A karshen jawabinsa, Jagora ya yi kira ga mahalartan akan kara dagewa wajen neman ilimi da aiki da shi, kula da Mujahada, da karatun Alkur’ani, da sauran ayyukan samun lada, musamman kyautata mu’amala da yin komai saboda Allah. “Kyakkyawan mu’amala da mutane, shi ma babban darasi ne, wanda yake koyar da mutane su yi hulda da kai su ga addini, su ganka su ga addini, su ji maganar bakinka su ji addini, su yi mu’amala da kai su ga addini. Yauwa, addini kenan, har izuwa karewan ajali.”




24/Rabiʻ II/1446 AH
27/10/2024

09/10/2024

“Lokacin da muka karɓi saƙon hukunta Isra'ila, layin farko na dokar aikin shi ne a kula da jinin wanda basu ji ba basu gani ba, musamman Mata da Yara”
—Cewar Dakarun Iran

31/08/2024

RANAR ALHAMIS! KO KUN SAN WACE RANAR ALHAMIS CE WANNAR? It
Bukari da Muslim sun ruwaito wanda duk malaman hadisi sun hadu a kan ingancinsa daga Abdullahi Ibn Abbas ya ce: “Ranar Alhamis! Ko kun san wace ranar Alhamis ce wannar?”, sai Ibn Abbas ya k**a kuka har sai da hawayensa su ka jika duwatsun da ke gabansa, sannan ya ci gaba da cewa: “ciwon Manzon Allah (S) ya tsananta ranar Alhamis, sai ya ce: ‘Ku zo min da littafi in rubuta muku wani abu wanda in kun bishi ba za ku taba bata ba a bayana’. Sai Umar ya ce: ‘Annabi ciwonsa ne ya yi tsanani, ya na magana ne ba cikin hankalinsa ba, mu littafin Allah ya ishe mu’. Sahabban da suke wurin sai s**a saba wasu na cewa ku kawo wa Annabi abinda ya nema ya rubuta muku abinda ba zaku taba bata ba a bayan sa, wasu kuma na fadin abinda Umar ya fada na cewa ciwo ne ya yi wa Annabi tsanani kada a kawo. Lokacin da hayaniya ya yi yawa a gaban Manzon Allah (S) (wasu na cewa a kawo, wasu na cewa ba za a kawo ba), sai Manzon Allah (S) ya ce: ‘Ku tashi ku bani wuri”. Mai ruwaya ya ce Ibn Abbas ya kasance ya na cewa: ‘Iyakar masifa! karshen masifa!! Sabanin da ya hana Manzon Allah (S) ya rubuta wannar takardar’ (Bukhari, Juzu’i na 7, shafi na 9, karkashin Babin ‘kaulil Maridhu kumu Anni’. Da Juzu’i na 8, shafi na 161, karkashin Babin ‘Karahyatul Khlifai’, bugun Darul Fikri, Sahih Muslim, Juzu’i na 5 shafi na 75, karkashin Babin ‘Tarkul Wasiyya’, bugun Darul Fikri da kuma Musnad na Ahmad bin Hambal, Mujalladi na 3, shafi na 309, karkashin Musnadu Ibn Abbas, bugun Darul Hadis Alkahira).
A nan cewar Manzon Allah (S) ‘Ituni bi kitabin iktub lakum kitaban lan tadhillu ba`adahu abadan’, ku zo min da littafi in rubuta muku wani abu wanda in kun bishi ba za ku taba bata ba a bayana, umurni ne ko ba umurni ba? Na tabbata ba mai shakkan cewa ‘Ku zo min da littafi’ ba umurni Manzon Allah (S) ya yi ba. In kuwa har haka ne, ashe kenan tun da ba a kawo masa takardar ba, ba abi umurninsa ba. Wanda saboda bakin cikin wannan har Ibn Abbas ya kasance ya na cewa karshen masifa ya faru a wannar ranar ta alhamis da aka hana a kawowa Manzon Allah (S) abin rubutun da ya nema, kuma har ya kasance saboda haka yana yin kuka mai tsanani har hawayensa sai sun jika duwatsun da ke gabansa.
Wadannan da su ka hana a kawo wa Manzon Allah (S) abin rubutun Sahabbai ne, amma a gaban Manzon Allah (S) ba yi da lafiya su ka ce ba za a kawo ba wai ciwo ne ya yi wa Manzon Allah (S) tsanani har bai san abinda yake fada ba, wa`iyazubillah!
Abinda ya faru kenan a wancar ranar ta alhamis in da Manzon Allah (S) ya yi umurni da a kawo masa abin rubutu alhali kuma ba shi da lafiya amma duk da haka wasu su ka hana su ka ce ba za a kawo ba, a gaban Manzon Allah (S) !!!!

-Miji Naseer-

31/08/2024

We condemn the forceful removal of Muslim sisters Hijab by the police and consider it blasphemy against Islam.

24/08/2024

PRESS RELEASE

RE: NOTIFICATION ON THE 2024 ARBAEEN SYMBOLIC TREK (INVITATION TO ATTEND AND PROVIDE SECURITY)

Our attention has been drawn to a paper dated August 22nd 2024, written to the Commissioner of Police, Nasarawa State Command, by one Hujjah Chambers purporting to be the “counsel of the Islamic Movement and the Shia Community in Nigeria”.

The letter was written to bring to the notice of the said Police Commissioner and to draw the attention of the Secretary of the Government of the Federation, the National Security Advisor (NSA), and other government agencies about the annual symbolic Arbabeen trek that will take place across various cities in Nigeria by the Islamic Movement under the leadership of his eminence, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H). It further requested that the security forces attend and provide security at the gathering.

For the avoidance of doubt, the legal outfit Hujjah Chambers is representing itself in this regard, and the written paper only reflects their stand, not that of the Islamic Movement or its leader (H). In all honesty, the Islamic Movement has nothing to do with this paper in any way whatsoever.

The annual Arbaeen trek is a religious event that is observed across the world to commemorate the 40th day of the martyrdom of the grandson of the Holy Prophet, who was martyred, alongside his family and companions, in the plain of Karbala some 1400 years ago. People from all walks of life trek in solidarity with Imam Hussein (as) for his exemplary sacrifice and being a great champion for truth and justice in human history.

It is a religious tradition, and therefore seeking permission from security agents or their approval before observing it is, to begin with, unnecessary. In addition, it is public knowledge that the Islamic Movement has always been observing this annual event and all its other activities peacefully and in an orderly manner, and therefore requesting the presence of the security forces under the guise of ‘providing security’ does not make sense.

The same security agents that are notoriously known for attacking peaceful and innocent civilians while exercising their constitutional and religious rights and, at the same time (they) woefully fail to provide security to a nation plagued by unprecedented insecurity, are not invited to our gatherings. The Islamic Movement has always been a victim of their brutality and lawlessness. They are instead advised to channel their attention to the worsening insecurity crisis ravaging the country.

The Islamic Movement would like to make it categorically clear to the general public that this paper written by Hujjah Chambers is not in its name. And the movement has dismissed it and distanced itself from it. It should also be known that all our activities are religious, a form of worship to Almighty Allah, and there is thus no reason to seek the permission or approval from any human being before observing them. That permission and approval automatically come from our creator, as He said in the Glorious Qur’an: “And I did not create the Jinn and Mankind except to worship me." (Q51:56). May peace of Allah be upon those who follow guidance.

Signed by

Sheikh Sidi Munir Mainasara Sokoto
For the Islamic movement under the leadership of his eminence Sayyid Ibraheem Ya’qoub El-Zakzaky (H).

Want your place of worship to be the top-listed Place Of Worship in Potiskum?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Potiskum
Potiskum
YOBESTATE