Comrd Bashir Labaran Ahmad
22/12/2020
KUKA KURCIYA.....
Shin menene amfanin yin kalaman tun Zara matasa da shugabannin da suke mulkar al'ummah sukeyi???
A tinanina yin hakan babban kuskure neh, sabida duk Wanda akace shugabane kullum tinaninsa ya za'ayi al'umma ta zauna lafiya shine tinaninsa amma abin takaici a wannan lokacin da muke ciki wasu mutane suke kokarin mayar damu gidadawa wajan sakamu yin abinda zamuzo muyi Danasani daga baya, ayki da zamuyi muce dama bamuyi bah.....
Idan mukayi waiwaye baya Zaben da aka gudanar anyi amfani da kalaman da s**ai kokarin tayar da tarzoma amma Allah ya tsare al'ummarsa amma kuma a wannan lokacin da muke neman zaman lafiya ruwa a jallo wasu bata garin shugabanninmu suke qara tarbiyyantar don biyan bukatar kansu....
Haka a wannan lokaci akwai Wanda yayi kalamai wayan basuyiwa al'umma dadi bah Don kuwa kalamaine na tunzura matasa, Wanda masana sunyi bayani cewa shi matashi musamman Wanda shekarunsa bai wuce 18 zuwa 30 bah, idan kace a mutu gobe zaice a mutu yau don shi yanajinsa kamar zaki a wannan yanayin da yake ciki akwai karancin tinani a gareshi....
Yanzu haka acikin wannan satin muka qara tsinkayar wani sabon video kusan guda biyu Wanda wasu mutane wayanda suke jagorantar al'umma suke kalamai wayanda yakamata hukumomin tsaro Su kirasu domin yiwa abun garanbawul kafin faruwar hakan, Don abune Wanda zai haifar da gaba ko kuma zazzafar mu'mala tsakanin al'ummarmu.....
Shin Mai yasa duk shugaba da zai mulkemu baza'a bamu damar muyi masa screening sabida Mu zab'i mutannan da s**a chanchanta Su mulkemu a ko wane mataki, misali tun daga matakin Monitor na class zuwa matakin da Allah ya Ara mana anan gidan duniya.....
Lallai al'umma tana cikin matsala matuqar zamu dunga Bari wayanda suke kokarin tayar mana da hankali suna zama shugabanninmu a matakai daban daban da muke dasu
Allah ubangiji ya bamu shugabanni nagari masu son zaman lafiya da kwanciyar hankali ka bamu zaman lafiya a kasarmu lanjeriya...
Rubutawa ✍️ Comrd Bashir Labaran Ahmad
22/12/2020
Kungiyar Arewa media Writers Reshen jihar kano Zata Shirya "Gasar Rubutu" A yunkurin da muke na Zaburar da Membobin Kungiya da Shuwagabanni Kungiyar Arewa media Writers Reshen Jihar Kano ta shirya Kayatacciyar Gasa ta Marubuta , Wacce zata baiwa duk wani member na kungiya damar Shiga Wannan Gasa
YADDA GASAR ZATA KASANCE:-
Kungiya zata Fitar da Kwamiti da zai Jagoranci Wannan Gasa
Kowanne member ko Shugaban kungiyar na Wani sashe yanada damar Shiga wannan Gasa
Gasar Zata Kasance Duk sati za'a Ringa fitar Da Zakaran Da ya lashe Wannan Gasa
Duk wanda ya Lashe Gasar kungiya zata Karramashi da " Certificate"
Sannan zata Tura Labarinsa zuwa ga Shafin kungiya na kasa domin A saka a gidan Jaridu da kafafen sadarwa
Labaran da kungiya zata saka Gasa akansu sune ;
* Nasiha/Fadakarwa
*Fashin baki kan abubuwan da suke faruwa a yankin Arewa
*Rubutun wayar da kan al'ummar Arewa
*Halin matsin rayuwa da wasu al'ummar Arewa suke ciki
*Rahoton sahihin abunda ke faruwa a yankin Arewa.
Wadannan Sune Labaran da zamu saka Gasa akansu
Za'a fara Wannan Gasa Nan bada jimawa ba InshaAllah ,da Zarrar An kanmmala Tsara kwamiti za'a Sanar dan haka kowa ya Wasa Alkalaminsa ✍🏻 da kuma Basirarsa 😎 Domin Zamu Fitar da Zakakuran Marubutan Mako 👌
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Nasarawa
700223