Mafitaa

Mafitaa

Share

20/03/2023

MISALIN RASHIN RABO.

Wanine yaje wurin walima sai ya zauna layin gaba yasan duk bala'i tagaba za'a fara raba abinci
Kafin ya ankara sai yaga anshigo da abinci a maimakon afara rabawa ta gaba sai aka fara raba abincin ta layin baya kafin azo wajensa abincin ya kare
Sai yatashi yakoma baya sai aka shigo da naman kaji a maimakon afara ta layin baya a tunanin gogan sai yaga aka fara raba naman kajin ta layin gaba kamin azo wajensa naman ya kare
Cikin haushi ya tashi yakoma layin tsakiya haushi ta kulle masa ciki yasa kansa a teburi yana karatun jaki kawai sai yaji ance "malam! Bismillah" yayi maza ya d**o kai yaga ana miko masa tsinken kwakwule hakori(toothpick) A tunaninsu har yagama cin abincin da naman kazan da aka bashine shine yakifa kansa a tebur yana hutawa
Cikin bacin rai yatashi ya shararawa mai rabon abincin mari a kumatunsa yace dashi " Uban waye ya gayamaka ni mayene da banci nama ba sai itacen kwakule hakwara zaka mikomin??? " 😂😂😂😂😂😂

Saboda haka idan abu ba rabonka bane ko ana hamaza hamata bazaka sameshiba dan haka kayi hakuri kawai rabonka bai wuceka indai kana a raye.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Mubi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Gra
Mubi

Opening Hours

09:00 - 17:00