AHMAD Assalafiy

AHMAD Assalafiy

Share

04/06/2025

Shin kun san addu'ar da aka fi son yi a ranar Arfa? To gata nan:
لاَ إلَهَ إلاَّ اللَّهُ وحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Ita Annabi SAW da sauran Annabawa s**ayi.

26/09/2023

LABARI MAI CIKE DA DARASI!

WANI DOCTOR NE zaune a office din shi (cikin asibiti) ya na shan A.C yana danna laptop din shi.
Kwatsam sai aka kirawo shi, cikin hanzari ya fito. Koda yazo sai ya tarar Accident ne akayi. Wani mutum ne aka kawo kwance cikin jini ko fuskar sa ba'a iya ganewa.
Nan take doctor yayi rubuce rubuce ya miqawa wadanda s**a kawo mutumin sannan ya ce musu; "Ku je ku nemo wadannan magungunan sannan ku biya kudin aikin da za ayi masa naira dubu100".
Sai mutanen su ka ce: "Mu matafiya ne, munzo wucewa ne muka tarar da mutumin yayi hadari a motarshi shine muka taimaka muka kawo shi nan, kuma wallahi ba mu da kudin nan don Allah doctor ka taimaka".
Cikin tsawa da fushi ya ce musu: "Lallai bazan ta6a shi ba har sai ankawo abubuwan, in kuwa ba haka ba to kubarshi ya mutu".
Kawai sai ya ja tsaki ya fice.
AFTER_2HOURS
Sai yadawo ya duba idan ankawo abubuwan da ya ce musu, koda ya zo sai ya tarar da mutanen su na kuka sun rufe mutumin da qyalle (alamar ya mutu kenan).
Da doctor ya ga haka, sai ya dauko wayar shi (ya na cewa bara na kira daddy naji ko ya sauka lafiya?). Koda wayar ta shiga, sai yaji qarar ringing din ya na tashi a cikin jikin mutumin da aka rufe da qyalle (mai Accident din).
Cikin alamun mamaki Doctor ya tsinke wayar, sai ya sake kira a karo na 2 kawai sai ya sake jin sautin ringing din a jikin mutumin.
Sai ya janye qyallen, koda ya dauko wayar a jikin gawar sai yaga ashe gawar ta mahaifinshi ce (ya samu Accident din ne kafin ya je inda ya nufa) bai gane shi bane sak**akon jinin da ya 6ata ilahirin jikinsa.

DARASI:
Yana da kyau matsalar mutane ta zama tamu, haqiqa shi taimako ba ya faduwa qasa banza ga duk wanda yayi shi, Sakayyar shi na gun Allah. Kuyi amfani da lokacin ku, dukiyar ku, qarfin ku don taimakon junan ku ko don gyaran goben ku. Allah yasa mudace duniya da lahira.

Copied.

16/08/2023

KHAIRUL KALAM MA QALLA WADALLA

ANNABI SAW yace=
"idan bawa yatashi yin salla sai azo da dukkan Zunubbansa a azata akan kafaɗarsa, aduk lokacinda yayi ruku'i ko yayi sujada sai su zubo daga kansa"

(SILSILATUL AHADEETSIS SAHEEHA-1398)

DARASI:
Gorgodon daɗewarka a ruku'i ko sujada shine gorgodon kankare maka zunubbanka, dalili kuwa shine wannan Hadisin, domin ga yadda sababin Hadisin yake=
= ABDULLAHI IBN UMAR yaga wani saurayi yana tsawaita sallarsa sai yace- wa yasan wannan saurayin?
Sai wani mutum yace- na sanshi
Sai IBN UMAR yace= da na sanshi da na umurceshi da yawaita ruku'i da sujada domin naji ANNABI SAW yana cewa=
"idan bawa yatashi yin salla sai azo da dukkan Zunubbansa dukkanta a azata akan kafaɗarsa, aduk lokacinda yayi ruku'i ko yayi sujada sai su zubo daga kansa"

KIRA:
Muyawaita yin ruku'i da sujada don rabuwa da zunubbanmu
Murika ruku'i da sujada yadda ANNABI SAW yakoyar domin irinnasanne zai zubar mana da zunubbanmu
Amma fa zunubbanda ake kankarewar bata shafi KABA'IRAI ba hakanan bai shafi taɓa hakkin waniba, na farkon sai da tuba, nabiyun sai da mayarda hakki zuwa ga maishi,

YA ALLAH KAJARƁI RUKU'INMU DA SUJADARMU DA DUKKAN IBADOJINMU KUMA KAYAFE MANA ZUNUBBANMU,
AMIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIN.

*✍🏽SHEIKH ABUBAKAR BN MUSTAFA BIU.*

21/07/2023

*ILLAR KAMBUN-BAKA*

Wata yarinya ce jaririya yar wata 1 da haihuwa, tana ta yin kuka sosai ba kakkautawa har tsawon kwana biyu, sai Mahaifiyarta ta kaita asibiti aka aunata aka gwada akaga babu abinda ke damunta, likita yace: Lafiyarta kalau fa ba ta da matsalar komai.

Sai s**a dawo gida, amma kukan bai tsaya ba bata daina yin kukan ba, sai wata mata tace: To kuyi mata wankan Ruqya mana... Aka samo ganyen magarya da na tazargade da na garafuni aka zuba a ruwa daidai wankanta, sai aka karanta Fatiha, Farkon Baqara Ayoyi 5, Ayatul Kursiyyu, karshen Baqara Ayoyi 2, Ikhlas, falaqi da Nasi duk kowanne sau X3 ko 7, sai aka tofa a ruwan, aka bata kadan tasha sai aka yi mata wanka da sauran.

Aka samo Man zaitun aka karanta masa Irin wadancan Ayoyin a ciki aka shafe mata jikinta da shi, aka dafa kirjinta da bayanta ana ta maimaita karanta wannan Addu'ar: *_"A'UZU BIKALIMATILLAHI ATTAAMAAT MIN GADABIHI WA IQABIHI WA MIN SHARRI IBADIHI WA MIN HAMAZATISSHAYATYN, WA AN YAHDURUN."_*

Sai kawai akaga yarinya tana tayin hamma bini-bini ta yi hamma ba qaqautawa, sai akace Kambun-baka ne yak**a yarinyar.

Sai uwar tace: Kwarai kuwa biri ya yi maka da mutum, domin a shekaran jiya wata mata ta zo min barka da taga yarinyar sai tace: "Kai amma idanuwan wannan yarinyar suna da girma kuma suna da kyau gwanin sha'awa."

GARGADI:

Ya k**ata bakunanmu su saba da yin addu'a ga abinda muka gani har ya burge mu sbd gudun kar mutum yajazawa kansa, domin nan take sai a iya laqaba maka Maita ace kai Maye ne. Allah Ya tsare mana imaninmu.

Iyaye kuma sai a kiyaye a zage damtse wajan yiwa yara Addu'a ba dare ba rana sbd tsaro da neman Allah yabada kariya daga sharrin dukkanin halittunSA.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Mubi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address


Main Market
Mubi