Labaran kasa

Labaran kasa

Share

09/08/2024

Haske NEWSPAPER daily MAGAZINE

29/07/2024

'YAN SIYASA SUNA KARA ZUBAR DA KIMAR RUNDINAR SOJIN NIGERIA

Jiya Babban Supeta janar na 'yan sandan Nigeria yace zasu bawa masu zanga-zanga kariya matukar ta lumana ce

Yau kuma sanarwa daga Babban Hafshin Sojojin Nigeria yace ba zasu bari masu zanga-zanga su wargaza kasa ba (amma kuma an bari 'yan ta'adda suna cigaba da wargaza mana kasa ai) abin kunya kawai

Abu na farko: Zanga-zanga ba laifi bane a tsarin mulkin Demokaradiyya, kuma ya zama wajibi ga 'yan sanda su bawa masu zanga-zanga kariya kamar yadda yake a doka

Abu na biyu: Rundinar 'yan sandan Nigeria ita ne wanda kundin tsarin mulkin Kasa na Constitution ya daura mata alhakkin kula da harkokin tsaron cikin gida, sai idan lamarin tsaron cikin gida yafi karfinta kafin nan sai Sojoji su kawo mata agaji

Idan an fahimci wannan, to bai kamata rundinar Sojin Nigeria tayi wannan gargadi ga masu shirya zanga-zanga ba domin ba huruminta bane, zanga-zanga civil matter ne, sam bai kamata a shigo da Sojoji ba cikin wannan hayaniya

Yanzu da Sojoji s**a fitar da wannan sanarwa, sai kuma ya kasance masu zanga-zanga sun fito, shin hakan ba zubar da kima da kwarjinin rundinar Sojin Nigeria bane?

Ko da wasa bai kamata rundinar Sojin Nigeria ta bari 'yan siyasa suna rage mata mutunci da daraja ba a idon 'yan kasa saboda biyan bukatun 'yan siyasar, wannan yana kara dagula harkokin tsaron kasa gaba daya

Ita rundinar Sojin Nigeria itace rundina mafi karfi, an samar da ita ne don tayi yaki ta kare Kasa ta sama da kasa da ruwa daga mahara ketare ko kasashen waje, itace last hope a fannin tsaro, shiyasa bai kamata soja yayi mu'amala da fararen hula ba

Kuma bai kamata Soja ya shiga harkokin tsaron cikin gida ba, domin ba akan haka ya samu horon aiki ba, abinda aka horar da Soja shine yayi harbi ya kashe abokin gaba, 'yan sanda kuma aikin su shine su kare rayukan 'yan kasa da dukiyoyinsu, sannan suyi bincike kan masu aikata laifuka

Amma abin takaici yau mun wayi gari miyagun 'yan siyasa sun lalata mana rundinar Sojin Nigeria,

29/07/2024

Da Dumi-Dumi

Za mu bijire wa duk wani yunkuri na kawar da gwamnatin Bola Tinubu da sunan zanga-zanga - Shugabannin jam‘iyyar APC na jihohi 36 na Nijeriya
FOLLOWING HASKE NEWSPAPER DAILY MAGAZINE

27/07/2024

YANZY-YANZU: Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC mai mulki sun ce basu san dalilin da yasa ake shirin,shirya ząɲga-záɲga ba a kasar

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi bayan wani taron na kungiyar gwamnoni Progressives’ Governors Forum (PGF) da aka gudanar a Abuja,in da yace ba mu san masu shirya záɲga-ząɲgar me suke shirin yi ba,muna kira da su zo muzauna a tattauna domiɲ samun mafita.

Yace mu a matsayinmu muɲ himmatu wajen tabbatar da hadin kan kasar nan, mun himmatu ga duk wani abu da zai inganta rayuwar 'yan Nájeriya, ya kawo wadata, samar da ayyukan yi ga matasa maza da mata wadaɲda s**a kammala karatunsu domiɲ a sámar musu aiki yi.

Gwamnaɲ Uzodimma ya ci gaba da cewa bai dace a halin yanzu kasar nan ta yi wata záɲga-ząɲgar da wata kungiya za ta yi ba, inda ya bukáaci ‘yan Nąjeriya da su yi watsi da wanna záŋga-zâɲgar.

Ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su yi hakuri da gwamnati, yana mai cewa ana ci gaba da kokarin ganin an daidaita matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita a kasar.

ya kara da cewa: “Muna ganin ba hikima ba ne a halin yanzu duk wata zanga-zangar da wata kungiya ta mutane za ta yi ta kowace irin salo.

Muna amfani da wannaɲ dama don mu shawarci matasaɲ mu maza da mata da su daina tuɲzura su su haddasa rikíci ko hárgitsi a kasar nán.

Me zaku ce?
Following Haske NEWSPAPER "multimedia

Want your business to be the top-listed Advertising & Marketing Company in Maiduguri?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Maiduguri
Maiduguri