Modu Sirrin Forex
ME AKE NUFI DA "FOREIGN EXCHANGE"?
Yanzu bari mu warware kalmar da kanta.
Kalmar "Forex" ta fito ne daga kalmomi biyu na Turanci.
Wato Foreign da Exchange.
Foreign na nufin "wata ƙasa/kasar waje".
Exchange kuma yana nufin "musanya" ko "canji".
Saboda haka idan muka haɗa su tare, zasu bada maana Kamar haka Foreign Exchange kuma yana nufin musayar kuɗin wata ƙasa da na wata ƙasa.
Shi ya sa aka taƙaita sunan zuwa Forex da daukar harafi uku daga k**ar farko ta Foreign dakuma harafi biu daga k**a ta biu wato Exchange, harwa yau wasu suna kiranta FX a daukar farko da karshen kalmar Forex din.
Ka lura, ba a ce Trading ba tukuna.
Saboda shi trading ya shigo ne lokacin da mutane s**a fahimci cewa farashin waÉ—annan kuÉ—aÉ—e ba ya tsayawa wuri guda.
Yana hawa.
Kuma yana sauka.
Idan farashi yana motsi... to akwai damar samun riba daga wannan motsin.
Daga nan ne aka haifi Forex Trading.
Saboda haka akwai bambanci tsakanin Foreign Exchange da Forex Trading.
Foreign Exchange shi ne canjin kuɗi saboda buƙata.
Forex Trading kuma shi ne amfani da wannan motsin farashi domin neman riba.
Mutane da yawa suna haÉ—a abubuwan biyu wuri guda... amma a zahiri ba abu É—aya ba ne.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Address
Kano
Maiduguri