Danbaiwa Collection
19/07/2019
'Yan wasan Aljeriya lokacin da s**a yi sujada don murnar lashe gasar cin kofin kasashen Afirka ️⚽️
05/07/2019
YAUSHE ZA'A YANKE HUKUNCIN ZABEN KANO
A ranar Alhamis ne kotun mai sauraron kararrakin zaben gwamna ta fara zaman share-fage a kan karar da ke gabanta.
Abba Yusuf, wanda aka fi sani da "Abba gida-gida", ya sha kayi a hannun Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a karashen zaben da aka yi, duk da cewa shi ne kan gaba a zaben farko wanda bai kammala ba.
Sai dai masu sa ido na gida da waje sun soki yadda aka gudanar da karashen zaben suna masu cewa an tafka magudi, zargin da jam'iyyar APC da kuma hukumar zabe s**a musanta.
Kotun dai tana da kwana 180 ne ta yanke hukunci daga ranar da aka shigar da karar. A ranar 11 ga watan Afrilun 2019 ne Abba ya shigar da karar.
Ke nan kwanaki 97 ya rage ita wannan kotu ta kammala shari'ar domin yanke hukunci.
Zaman kotun na ranar Alhamis wanda mai shari'a Halima Shamaki ke jagoranta, ya mayar da hankali ne kan tantance bayanai da korafe-korafen da bangaren masu kara da na masu kare kai s**a gabatar.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Lagos
DEIRAHDUBAI