AID Multimedia Hausa

AID Multimedia Hausa

Share

Photos from AID Multimedia Hausa's post 08/07/2026

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙaimi wajen yi wa kowane ɗan Nijeriya rajistar shaidar ɗan ƙasa ta dijital

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da cewa an yi wa kowane ɗan Nijeriya rajistar shaidar ɗan ƙasa ta dijital a faɗin ƙasar, ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC).

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja yayin da ya karɓi baƙuncin Babbar Darakta kuma Babbar Jami'ar Gudanarwa ta NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote, da tawagar ta, waɗanda s**a kai masa ziyarar girmamawa domin gabatar da muhimman tanade-tanaden sabuwar Dokar NIMC ta 2026.

Ministan ya ce ingantaccen tsarin tantance shaidar 'yan ƙasa yana da matuƙar muhimmanci wajen kyautata shugabanci, tsara cigaban ƙasa, bunƙasa harkokin kuɗi, haɓaka sauyin fasahar zamani da kuma aiwatar da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce: “Tsarin tantance shaidar 'yan ƙasa shi ne ginshiƙin ajandar sauye-sauyen Shugaban Ƙasa. Domin idan za a aiwatar da gyare-gyare, dole ne a san waɗanda ake yi wa. Idan ba a san adadin jama'a ba, da tsarin yawan su da yadda s**a kasu, ta yaya za a tsara musu ingantattun tsare-tsare?”

Idris ya yaba wa shugabancin Dakta Coker-Odusote, yana mai cewa yi wa sama da mutum miliyan 136 rajista babban cigaba ne, amma har yanzu akwai kusan mutum miliyan 100 da ba a yi wa rajista ba.

Ya ce: “Mutum miliyan 136 da aka riga aka yi wa rajista babban cigaba ne, amma har yanzu akwai kusan 'yan Nijeriya miliyan 100 da s**a rage, kuma su ma ya kamata a yi musu rajista. Kowane ɗan Nijeriya ya cancanci a saka shi cikin tsare-tsaren cigaban ƙasa.”

Ministan ya ce cimma burin yi wa kowa rajista yana buƙatar ci gaba da wayar da kan jama'a, musamman a matakin ƙananan hukumomi da al'ummomi. Don haka ya buƙaci NIMC da ta ƙara haɗin gwiwa da Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), wadda ke da ofisoshi a dukkan ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan.

Ya ce: “Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa ita ce mafi dacewa wajen isa ga al'ummomin karkara. Ina roƙon ku da ku ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar ku da NOA domin mu duka mu tabbatar da cewa kowane ɗan Nijeriya ya fahimci muhimmancin tsarin shaidar 'yan ƙasa.”

Haka kuma ya yaba wa NIMC bisa yadda ta kiyaye bayanan jama'a, yana mai cewa babu wani rahoton kutsen da ya yi sanadin fallasa bayanan masu rajista.

Ya ƙara da cewa: “Na yi farin cikin jin cewa ba ku taɓa fuskantar matsalar kutsen bayanai ko da sau ɗaya ba. Kare sirrin bayanai, gudanar da aiki cikin gaskiya da kuma amincewar jama'a su ne ginshiƙan nasarar tsarin shaidar dijital, kuma za mu ci gaba da amfani da dukkan kafafen yaɗa labarai na Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai wajen tallafa wa shirye-shiryen wayar da kan jama'a.”

Tun da farko, Darakta Janar na Hukumar Wayar da Kan Jama'a ta Ƙasa (NOA), Mallam Lanre Issa-Onilu, ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da tallafa wa NIMC wajen wayar da kan jama'a ta hanyar cibiyoyin ta da ke faɗin ƙasar nan.

Ya ce: “Mun san muna aiki tare, amma ina fatan za ku ci gaba da tuntuɓar mu domin mu ga yadda za mu ƙara ba da gudunmawa. Muna da wakilci a wuraren da kuke son zuwa domin wayar da kan jama'a da faɗakar da su.”

A nata jawabin, Babbar Darakta ta NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote, ta ce sabuwar Dokar NIMC ta 2026 ta sabunta tsarin kula da shaidar ɗan ƙasa a Nijeriya, inda ta ƙunshi tanade-tanade kan kare bayanai, tsaron intanet, inganta tsarin bayanan gwamnati na zamani da kuma ƙarfafa amincewar jama'a da tsarin dijital.

Ta ce: “Shugaban Ƙasa ya umurce mu da mu fara rajistar jama'a daga unguwa zuwa unguwa, domin yana son tabbatar da cewa mutanen karkara da na matakin al'umma ba a hana su cin gajiyar duk wani shirin tallafin gwamnati ba.”

Ta bayyana cewa hukumar ta fara gangamin rajista a dukkan unguwanni 8,809 na Nijeriya domin tabbatar da cewa an yi wa kowane ɗan ƙasa rajista, ciki har da mata, yara, masu naƙasa, mazauna karkara, 'yan gudun hijira, baƙin da ke zaune bisa doka da kuma 'yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje.

A nasa jawabin, Shugaban Sashen Hulɗa da Jama'a na NIMC, Dakta Kayode Adegoke, ya ce sabuwar dokar ta sauya tsarin kula da shaidar ɗan ƙasa a Nijeriya baki ɗaya.

Ya ce: “NIMC ta wuce matsayin mai adana bayanai kawai, ta zama babbar hukuma ta ƙasa da ke da alhakin kula da tsarin shaidar dijital. A yanzu, NIMC ita ce kaɗai hukumar da aka ba ikon kula da tsarin shaidar dijital a Nijeriya.”

Ya ƙara da cewa dokar ta samar da tsarin doka na Digital Public Infrastructure (DPI) da Public Key Infrastructure (PKI), tare da ƙarfafa kariyar bayanan jama'a da faɗaɗa amfani da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) a ayyukan gwamnati da kamfanoni masu zaman kan su.

A cewar sa, NIMC ta haɗa tsarin ayyukan ta da fiye da ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati 250, tare da ƙaddamar da sababbin fasahohi da s**a inganta ayyukan rajista tare da rage lokacin da ake ɗauka wajen yi wa jama'a rajista.

Ziyarar ta samu halartar Darakta Janar na NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu; Babbar Darakta kuma Babbar Jami'ar Gudanarwa ta NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote; Daraktan Sashen Samarwa, Wallafe-wallafe da Adana Takardu, Mista Ibidapo Okunnu; Mataimakiyar Darakta mai kula da Hulɗa da Jama'a da Ladabi, Misis Fatoke Folasade, da sauran manyan jami'an Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da na Hukumar NIMC.

Photos from AID Multimedia Hausa's post 08/07/2026

Gani Ya Kori Ji: Aikin bututun iskar gas na AKK ya kai kashi 95%, zai ƙarfafa masana'antu da tattalin arzikin Arewa

A rana ta uku na rangadin 'Gani Ya Kori Ji' na manyan ayyukan gwamnatin tarayya a Arewacin Najeriya, tawagar masu aikin jarida dake rangadi tare da Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ta kai ziyara zuwa aikin bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK), ɗaya daga cikin manyan ayyukan samar da makamashi da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa. Rangadin ya bai wa mahalarta damar ganin yadda aikin ke gudana da kuma samun cikakken bayani daga jami'an da ke kula da shi.

A yayin ziyarar, tawagar ta fara isa Block Valve Station 19 da ke ƙauyen Rahma Wali a Ƙaramar Hukumar Makarfi ta Jihar Kaduna, inda jami'an aikin s**a bayyana cewa aikin ya kai kusan kashi 95 cikin 100 na kammaluwa. Sun nuna kwarin gwiwar cewa da zarar an ƙaddamar da aikin, zai samar da iskar gas mai ɗorewa ga tashoshin samar da wutar lantarki da masana'antu, lamarin da zai rage kuɗin makamashi, ƙara samar da wutar lantarki da kuma buɗe ƙofofin kafa sabbin masana'antu a Arewacin ƙasar.

Jami'an sun bayyana cewa aikin, wanda aka fara a zamanin gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, ya ci gaba da samun cikakken goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda). Sun ce wannan ya nuna ƙudirin gwamnatin tarayya na kammala manyan ayyukan more rayuwa da ke da tasiri kai tsaye ga bunƙasar tattalin arziki da ci gaban ƙasa.

An kuma yi wa tawagar bayani cewa bututun iskar gas na AKK mai tsawon kusan kilomita 614 zai haɗa yankunan da ake da wadataccen iskar gas a kudancin Najeriya da jihohin Arewa, tare da samar da ingantaccen makamashi ga masana'antu, kamfanonin sarrafa kayayyaki da sauran harkokin kasuwanci. Baya ga haka, aikin ya samar da dubban guraben ayyukan yi kai tsaye da kuma a kaikaice a lokacin gini, kuma ana sa ran zai ƙara samar da ɗimbin ayyukan yi bayan fara aiki sakamakon sababbin masana'antu da harkokin kasuwancin da za su bunƙasa a yankunan da bututun ya ratsa.

Masu aikin jaridar da ke cikin shirin 'Gani Ya Kori Ji' sun bayyana cewa ziyartar aikin ta ƙara musu fahimtar muhimmancin shirin ga makomar tattalin arzikin Arewa. Sun ce aikin ba kawai bututun iskar gas ba ne, illa wata babbar gada ce ta bunƙasa masana'antu, ƙarfafa samar da makamashi, jawo masu zuba jari da samar da ci gaba mai ɗorewa. Sun kuma bayyana aikin a matsayin wata babbar shaida ta ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na amfani da manyan ayyukan more rayuwa wajen inganta rayuwar al'umma da gina tattalin arzikin Najeriya.

Photos from AID Multimedia Hausa's post 08/07/2026

Janar Rabe Ya bamu kwarin gwiwa, ya jahmu Sallah, ya karfafemu a addini, cewar Malam Abubakar, a hirarsa da DW Hausa, daya daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su tare da Marigayi Janar Rabe Abubakar, a jihar Katsina.

Want your business to be the top-listed Media Company in Lagos?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Lagos