Sen.Sankara For Senator 2019

Sen.Sankara For Senator 2019

Share

10/06/2019

MUHIMMIYAR SANARWA

Mai girma zababben sanatan shiyyar Jigawa arewa Maso Yamma jihar Jigawa, Sen.Dr.Danladi Abdullahi Sankara, na godiya dangane da irin goyon baya da fatan alheri da dumbin masoya daga Shiyarsa suke nuna masa.

Zababben sanatan na baiwa dumbin magoya baya masu sha'awar zuwa bukin rantsar da sabbin yan majalisun kasa a Abuja, hakuri don ganin cewa hukumomin da abun ya shafa basu fadada daman goron gaiyata don samun shigar magoya bayan zababbun da zaa rantsar da yawa ba, ranar talata 11/6/2019.

A sanadiyar hakan za'a ware wata rana ta musamman don bukin taya murna da masoya zasu samu daman nuna farin ciki da fatan alheri, bayan rantsarwa bada jimawa ba In Sha Allah .

Sanarwa Daga

Comr.Talib Abubakar Gumel

©Dallatun Ringim Media Team

Want your organization to be the top-listed Government Service in Lagos?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


27th Floor, Pearl Towers, Eko Atlantic City, Lagos
Lagos