Yeti digital
It's Friday
20/04/2025
Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya shawarci Kanawa kan muhimmancin zaman lafiya, inda ya nanata rawar da jihar ke takawa a ci gaban arewa.
Ya faɗi hakan ne a jawabinsa lokacin da ya je yi wa shugaban APC a Kano Abdullahi Abbas ta'aziyar rasuwar mahaifinsa.
13/04/2025
DA ƊUMI-ƊUMINSA: An Sace Motar Nuhu Ribadu A Wani Masallacin Juma'a
An sace mota kirar Toyota Hilux, mallakin ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a masallacin juma'a.
Rundunar ‘yan sanda ta babban birnin tarayya (FCT) ta kaddamar da bincike kan satar wata mota kirar Toyota Hilux mallakin Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro NSA, Malam Nuhu Ribadu, wadda aka sace yayin da jami’an ke halartar sallar Juma’a a birnin Abuja.
Wani masanin tsaro, mai suna Zagazola Makama, ya wallafa rahoton satar a shafin X wato Twitter, inda ya bayyana cewa an kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda na Garki da misalin ƙarfe 2:00 na rana, lamarin da ya sa hukumomin tsaro s**a ɗauki mataki cikin gaggawa.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Lagos