Arewa page
Allah ya kara tona asirin azzalimai
23/05/2020
NASIHA: Ba Zagin Shugabanni Ne Maslaha Gare Mu Ba
Daga Comr Abba Sani Pantami
Ina mamakin halayyarmu mu 'yan arewa, da zaran an samu mas'ala guda shike nan sai ka yi ta jin ana ta zagin shugabanni, ba ma tsayawa mu duba menene ya jawo sanadin samun matsalar, ta wace hanya za a bi domin a samu a shawo kan matsalar, kada hakan ta sake faruwa!!
Amma duk babu wannan tunanin a ranmu, yawan cin sai yan kadan daga cikin mu, muna da karancin hakuri da zarbabiya kan al'ummar mu, mu tsaya mu yi ta zagin shugabanninmu hakan fa ba shine zai kawo mana mafita ba, illa ma ya jawo mana wata fitina ta daban da Allah ka iya jarabar mu kuma mu sha wahala cikinta.
Sanarwar rashin ganin wata an riga da anyi, duk da an samu rahotonnin ganin watan a wasu sassan arewa cin Nijeriya, hakan ba ya rasa nasaba da rashin Isar da sakon nin ganin watan zuwa ga Sarkin musulmi ta hanyar da ya dace, idan kuka yi duba da sanarwar da ya fitar a jiya da dare.
Idan kuskure aka yi ma an riga da anyi shi, idan daidai ma aka yi shima duk an riga da anyi, kawai abunda ya k**ata a gare mu muyi ta addua, Allah Ubangiji ya karbi ibadunmu bawai mu zo soshiyal midiya mu yi ta zage-zage ba, wannan ba tarbiyar koyarwar addinin musulunci ba ce, don Allah 'yan uwa na al'ummar musulmi mu kiyaye zagin shugabanninmu.
Muna rokon Allah Ya karba mana ibadunmu. Amin
23/05/2020
Yadda Aka Cika Makil A Yayin Sallar Idin Da Sheik Dahiru Bauchi Ya Jagoranta A Safiyar Yau A Gidansa Dake Jihar Bauchi.
menene ra'ayin ku
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Lafia