Arewa computer library. Kaduna chapter

Arewa computer library. Kaduna chapter

Share

12/10/2022

AREWA COMPUTER LIBRARY

Arewa Computer Library Rashen Jihar kaduna Karkashin Jagorancin Mubarak Hamisu Sun Fitarda Wani Tsari na Musamman Wanda ze Amfani Yan Jihar ta hanyar samarda Wani Kasaitaccen Online Class Wanda Za,a kiyarda Courses k**ar haka,

(1) WebDesign
(2) Graphic Design
(3) ICT
(4) Digital Marketing

Da Sauransu Zakuyi Registration da Wannan Online Class Akan 500 Naira Only

Domin Neman Karin Bayani ku nemi wannan Nomber Kamar haka: 08080185388

State Arewa Computer Library

08/10/2022

Shawarwari ga duk matashin da ya tunkari shekaru 30 zuwa sama!

1. Kayi iya yinka wajen gujewa bashi, sai in ya zama dole, kuma da zarar ka samu sukunin biya to kayi hakan da wurwuri. "Bashi ba karamar barazana bace ga cigaba"

2. Idan Allah ya h**e maka aiki ko sana'a, ka dinga aje wani kaso komai ƙarancinsa, a asusun ajiyarka. "Ajiya maganin wata rana"

3. Aƙalla ka samu abin yi fiye da ɗaya, "Gida biyu maganin gobara"

4. A kowace safiya kamin rana ta faɗi, yi ƙoƙari ka iya wani sabon abu. Wayar da kake riƙewa makaranta ce babba "Ilmi kogi ne"

5. Aƙalla kowane mako ɗaya, ka yi ƙoƙarin karanta wani littafi. Akwai darussa da dama ƙunshe acikin littafai. "Ilmi haske"

6. Ka dinga motsa jiki aƙalla sa'a ɗaya a rana. " mafi yawan ciwarwata/cututtuka nada alaƙa da rashin motsa jiki.

7. Ahir, kashe dinka da zaman majalisa, amadadin haka yi wani abin da zai amfaneka da wannan lokaci, ko dai koyon wani abu ko neman ilmi. "Zaman kashe wando illa ce babba, kuma hurumi ne na wanzuwar giba da annamimanci" Ba zaka gane muhimmancin lokaci ba sai girma ya sameka.

8. Ka dinga tashi tunda safe domin tunkarar ayukan ka na wannan rana. "Da sassafe ake k**a fara"

9. Kowane yini kamin rana ta faɗi, yi ƙoƙari ka taimaki wani, ko da sadaka koda shawara kai koda da baiwa ƙadangaru ruwan sha ne. "Kar ka manta, wata karuwa ta samu gafarar Allah sak**akon yin taimako irin wannan"

10. Tallafi iyayenka da komai ƙanƙantar abin da Allah ya h**e maka, ko da kuwa suna da sukuni. "Akwai albaka sosai a taimakawa iyaye da yi masu biyayya"

Duka waɗannan matakan nasara ne!

Allah yataimakemu baki daya.

✍️ Mubarak Hamisu

15/09/2022

Alhamdulillah.
Yanzu haka Arewa Computer Library (ACL) ta samu wani babban bango da yaketa kokari da fadi tashin ganin Certificate din ACL ya samu karbuwar da za'a iya neman HND dashi InshaAllah..

Allah Ya Tabbatar Mana Da Alkhairi..🙏

Want your business to be the top-listed Computer & Electronics Service in Kawo?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Kawo