Sunnatur RASUL
HANYOYIN SAMUN ILIMI
FASALI NA BIYU
DARASI NA BAKWAI
*LADDUBAN DALIBI GA MALAMINSA*
Ya kai dalibi cin ribarka yana ga malamin ka
1- Kiyaye mutuncin Malaminka.
2- Girmama Malaminka.
3- Tausayawa Malaminka.
4- Ka zauna tare da Malaminka.
5- Ka kyautata sauraro da tambaya ga Malaminka.
6- Kayi hira da Malaminka don kyautatawa.
7- Kyawun ladabi wajen bude littafi a gaban Malaminka.
8- Karka gabace shi wajan yin magana (shisshigi) ko wajan tafiya.
9- Karka yawaita magana a gaban Malaminka.
10- Karka nace sai ya baka wata amsa.
11- Karka kirashi da sunnan shi kaitsaye.
12- Karka kira shi da "Kai!"
13- Karka kira shi daga nesa.
14- Yin koyi da kyawawan aiyyukansa da manyan dabi'unsa.
15- Kyautata masa (Yi masa kyauta).
16- Yi masa addu'a ta alkhairi.
17- Karka mike kafafuwanka a gaba gareshi.
LADDUBAN ZAMA DA ABOKIN KARATU
Sai a darasi nagaba in shaa ALLAHU.
Rubutawa: Dan Uwanku: Abdullah A Abdullah Assalafeey
ku tayamu yadawa ta hanyar shire (fatanmu mu gudu tare mu tsira tare)
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the university
Telephone
Website
Address
Katsina