Dawisu Reporters

Dawisu Reporters

Share

12/06/2026

Atiku Ya Zaɓi Amaechi a Matsayin Mataimakinsa a Takarar Shugaban Ƙasa ta ADC

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zaɓi tsohon Ministan Sufuri kuma tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takararsa a ƙarƙashin jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) gabanin zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairu, 2027.

Rahotanni sun ce an cimma wannan matsaya ne bayan makonni na tattaunawa da sasanta ra'ayoyi a cikin haɗakar jam'iyyun adawa, musamman bayan saɓani da ya biyo bayan zaɓen fidda gwani da kuma sauya sheƙar wasu fitattun 'yan siyasa zuwa wasu jam'iyyu.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin zaɓin Amaechi wata dabara ce ta ƙarfafa karɓuwar ADC a faɗin ƙasar, inda aka haɗa ɗan takara daga Arewa maso Gabas da mataimaki daga Kudu maso Kudu, abin da ake kira tikitin “AA”.

An ce Amaechi, wanda ya taɓa nuna rashin sha'awar karɓar kujerar mataimakin shugaban ƙasa, ya amince ne bayan roƙon wasu manyan jagororin siyasa. Atiku ya kuma tabbatar da cewa Amaechi zai taka muhimmiyar rawa a yaƙin neman zaɓe da kuma gwamnatin ADC idan jam'iyyar ta samu nasara.

Har ila yau, Atiku ya zargi gwamnatin tarayya ƙarƙashin APC da yunƙurin raunana jam'iyyun adawa kafin zaɓen 2027, tare da kira ga 'yan Najeriya da su kare dimokuraɗiyya da 'yancin siyasa.

12/06/2026

DA ƊUMI ƊUMI: Nijar Ta Saka Dokar Hukuncin Ɗaurin Shekaru 20 a Kurkuku Kan Masu Hulɗa ko Auren Jinsi

Mahukunta a ƙasar Niger sun amince da wata doka da ta tanadi hukuncin zaman gidan yari har na shekaru 20 ga duk wanda aka samu da laifin hulɗar soyayya ko jima'i tsakanin masu jinsi ɗaya.

Rahotanni sun ce sabuwar dokar na daga cikin matakan da gwamnatin ƙasar ta ce tana ɗauka domin kare abin da ta bayyana a matsayin ƙimomin al’umma da al’adun ƙasar.

Sai dai masu fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam sun dade suna nuna damuwa kan irin waɗannan dokoki, suna masu cewa suna iya shafar wasu 'yancin jama'a.

Har yanzu dai ana ci gaba da muhawara kan dokar a cikin ƙasar da ma a matakin ƙasa da ƙasa.

12/06/2026

EFCC ta k**a jami’in tsaron filin jirgin sama da wasu mutane biyu kan safarar gwal a Kano

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta k**a wani jami’in tsaron jiragen sama (AVSEC), Ali Baffa, tare da wasu mutane biyu bisa zargin safarar zinari da kuɗaɗen ƙasashen waje ta haramtacciyar hanya a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa, EFCC ta ce an k**a mutanen ne a ranar 11 ga Yuni, 2026, bayan wani samame da jami’anta s**a gudanar a filin jirgin. Binciken farko ya nuna cewa Ali Baffa ya ɓoye kilo 22.2 na ɗanyen zinari mai darajar sama da naira biliyan 4.4 a cikin wando domin kauce wa binciken tsaro da fitar da shi ƙasar waje.

Binciken ya kuma kai ga k**a Aushabu Nasidi, wanda ake zargin shi ne ya samar da zinariyar, inda aka samu kuɗaɗen ƙasashen waje iri-iri a hannunsa. Daga bisani an k**a Mukhtar Muhammad Dan Zaria, wanda ake zargin ya miƙa zinariyar ga Nasidi domin a fitar da ita.

A cewar EFCC, Dan Zaria ya amsa cewa ya yi safarar kusan kilo 40.2 na zinari tsakanin 1 zuwa 11 ga Yuni, 2026, ta irin wannan hanya.

Hukumar ta ce har yanzu ana ci gaba da bincike kan lamarin, yayin da ake tsare da waɗanda ake zargin kafin gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.

12/06/2026

Duk dan majalisar da ba zai iyawa shugaban kasa gyara idan yayi Kuskure ba, Ba dan Majalisa bane, dan Amshin shata ne.

Inji Tsohon kakakin majalisar Dattijai, Sanata Bukola Saraki

Photos from Dawisu Reporters's post 12/06/2026

Kanone Asalin Dangote da BUA ba Lagos ba: Sarkin Kano Muhammad Sanusi II yawa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima Martani

Karin bayani a comment

Want your business to be the top-listed Media Company in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Katsina