Blueprint Hausa
19/04/2026
Gudunmawar Pantami wajen Sabunta Hanyar Gombe–Kumo–Billiri–Kaltungo zuwa Cham–Numan (Yola)
A ranar 26/08/2022, an ƙaddamar da muhimmin aikin hanyar Gwamnatin Tarayya a garin Gombe wacce ta haɗa Gombe–Kumo–Billiri–Kaltungo zuwa Cham–Numan (Yola), a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, GCFR, wanda Professor Isa Ali Pantami ya wakilta. Wannan nasara ta biyo bayan ƙoƙari da jajircewarsa wajen bibiyar matsalolin hanyoyin Gombe, musamman hanyar Cham zuwa Numan, wadda ta daɗe tana tafiyar hawainiya tun bayan bayar da aikin a shekarar 2017.
Ta hanyar tuntuba da Ministocin Ayyuka tare da gabatar da hujjoji kan matsalolin fasaha da s**a haɗa da Black Cotton Soil da buƙatar sake gina gada, an samu amincewar ƙarin kuɗi sama da Naira biliyan 7.6 domin tabbatar da ingantaccen kammala aikin.
Titin ya haɗa muhimman yankuna da s**a haɗa da Gombe, Kumo, Billiri da Kaltungo, tare da ƙarfafa alaƙa tsakanin jihohin Gombe, Adamawa da Taraba. Wannan haɗin kai ya sauƙaƙa zirga-zirga, ya bunƙasa kasuwanci, tare da inganta rayuwar al’umma, musamman manoma da ‘yan kasuwa da ke anfani da hanyar a kullum. Hanyar na daga cikin muhimman ayyukan more rayuwa da ke ƙara tabbatar da tasirin wakilci da himmar Pantami wajen jawo ayyukan ci gaba zuwa jiharsa.
Maigirma Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, da Lamido Akko na daga cikin manyan baƙi da s**a halarci bikin ƙaddamarwar. Kasancewar su ya nuna muhimmancin aikin da kuma yadda haɗin gwiwar gwamnati ke samar da ci gaba mai ɗorewa ga al’umma. Wannan aiki ya zama shaida a fili cewa nagartaccen wakilci da hangen nesa na iya haifar da ainihin sauyi a rayuwar jama’a.
Akwai wasiƙar da tsohon Ministan Sadarwa, Prof. Isa Ali Pantami, ya rubutawa Ministan Ayyuka na wancan lokaci, Raji Fashola (SAN), a ranar 16 ga Satumba, 2019, kan buƙatar ƙarin tallafi domin kammala wannan muhimmin aikin hanya a yankin Arewa maso Gabas. Za a kawo cikakken bayani kan wannan wasiƙa nan ba da jimawa ba, in sha Allah.
Dole Elrufa'i Ya Rufewa Mutane Baki Ya Fuskanci Tuhume-tuhumen Da Ake Masa ~ Inji Kungiyar DWI
Kungiyar Democracy Watch Initiative (DWI) ta yi kira dangane da binciken da ake yi wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai. A halin yanzu yana fuskantar bincike daga hukumomin yaki da cin hanci da kuma hukumomin tsaro da dama, ciki har da Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) da Department of State Services (DSS). Kungiyar ta ce kokarinsa na karkatar da hankalin jama’a daga wadannan manyan zarge-zarge ba gaskiya ba ne, kuma hakan na iya zama barazana ga tsaron kasa.
El-Rufai ya amince cewa sun kutsa cikin hanyoyin sadarwa wayar National Security Adviser (NSA), abin da ya nuna rashin mutunta dokoki da tsarin tsaron kasa. DWI ta ce wannan ba siyasa ba ce kawai, illa keta doka da kuma cin amana da aka dora wa shugabanni.
A wani bayani da ya fitar, El-Rufai ya ce ya nemi karin haske daga NSA kan rahotannin shigo da sinadarin thallium sulphate mai matukar hadari. Duk da cewa gaskiya da rikon amana suna da muhimmanci, hanyar da ya bi ta jawo tambayoyi maimakon bayar da amsoshi. Maimakon ya maida hankali kan tuhumar da ake masa, sai ya nemi sauya labari domin ya nuna kansa a matsayin mai kishin kasa, alhali yana karkashin bincike.
DWI ta jaddada cewa babu wanda ya fi karfin doka, komai mukaminsa ko tsohon matsayinsa. Ta bukaci El-Rufai ya fuskanci doka domin tabbatar da adalci da kare tsaron kasa. Doka ita ce ginshikin dimokuradiyya, kuma dole ne kowa ya dauki alhakin ayyukansa.
Kungiyar ta kuma roki hukumomi su hanzarta bincike ba tare da tsangwama ba, tare da kare mutuncin cibiyoyin kasa. Ta gargadi jama’a da kada su bari siyasa ta dauke musu hankali daga manyan batutuwan tsaro da adalci.
A karshe, DWI ta sake jaddada bukatar a binciki dukkan matakan da El-Rufai ya dauka tare da tabbatar da ya amsa tambayoyi kan sak**akon ayyukansa. Ta ce sai an tabbatar da gaskiya da rikon amana ne kawai za a samu Najeriya mafi tsaro da dimokuradiyya ga kowa.
01/02/2026
Ɗaruruwan matasa magoya bayan Professor Isa Ali Pantami (Majidadin Daular Usmaniyya kuma Wazirin Pantami) sun gudanar da taro a karamar hukumar Funakaye, jihar Gombe.
A yayin gudanar da taron an kara wayar da kan matasan kan abunda ya shafi harkar rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta da wayar da kansu.
Haka zalika matasan Funakaye sunyi kira tare da roko ga Professor Isa Ali Pantami da ya daure ya fito takarar Gwamnan jihar Gombe a zaben 2027.
Mutanen Funakaye sunyi dan-dazo Mazansu da matansu sun fito daga kowane yanki na fadin karamar hukumar, domin nuna soyayya da kaunarsu ga Majidadin Daular Usmaniyya.
Wannan yake kara nunawa da tabbatar da cewa mutanen jihar Gombe na kowane yanki a shirye suke domin bada gudummuwarsu na ganin Professor Isa Ali Pantami, ya zama Gwamnan jihar Gombe a zaben 2027.
02/01/2026
GWAMNAN JIHAR BAUCHI BALA MUHAMMAD YA FALLASA ASIRIN MINISTAN ABUJA NYESOM WIKE
Maigirma Gwamnan jihar mu na Bauchi Senator Bala Abdulkadir Mohammed (Kauran Daular Usmaniyyah) ya fallasa asiri na makircin da Ministan Abuja Nyesom Wike yake kulla masa da jihar Bauchi gaba daya
Maigirma Gwamna yayi wannan fallasa ne a cikin shirin Sunrise Daily na Channels TV dazu da safe, yace akwai wanda yake shirya min makirci, kuma na san shi, shine Ministan Abuja na yanzu Nyesom Wike, ya fada wa duniya cewa zai kunna wuta a jihata na Bauchi
Kauran Daular Usmaniyyah yaci gaba da cewa; na fahimci Wike ne yake bada umarni wa hukuma irin na EFCC wajen batani, yana bawa mutane cin hanci, yana sayar da filayen Abuja yana amfani dasu wajen cimma burinsa, ba sabon abu bane a gareni saboda na taba rike mukamin Ministan Abuja na shekaru 6 na san komai
Gwamnan Bauchi yaci gaba da cewa; yana da hujjoji daga majiyarsa na sirri dake EFCC wanda s**a tabbatar masa da cewa Wike ne yake tsara duk abinda yake faruwa da ‘yan adawar siyasa a Nigeria
Kaura yace tsohon Accountant General dinsa na jihar Bauchi yaci amanata, ni na kaishi Kotu da kaina domin a masa hukunci, daga bisani Kotu ta bada belinsa, to a yanzu Wike ne yake aiki dashi a Kotu wajen bada shaida na karya akan mukarrabaina da aka k**a
A matsayina na Gwamna wanda na rike manyan muk**ai tun daga Sanata har Minista, ina shugaban al'ummah ta ya zai kasance ina daukar nauyin ta'addanci, ana min wannan sharri ne saboda ina cikin manyan 'yan adawa
Zan bi duk matakan da s**a dace domin na kare kaina, na rubuta wa Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya takardan korafi, tare da sanar da hukumomin tsaro, kuma zan kai korafina zuwa ga hukumonin Majalisar dinkin duniya, inji Maigirma Gwamna
Sannan Gwamna Bala yace Shugaban Kasa Tinubu yana kewaye da 'yan daba, 'yan damfara wadanda suke son ha||akashi a siyasance irinsu Wike
Muna rokon Allah Ya kare jihar Bauchi daga wadanda suke neman jingina mana ta'addanci, Allah Ya sa mugun nufinsu ya kare a kansu da iyalansu kadai.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Katsina