Dandume Reporters
10/09/2024
Ubangiji Allah ya kawo sauki wa Alummar birnin Maiduguri da ambaliyar ruwa ta afka musu. Allah ya basu mafita na Alkhairi.
A karɓa da haƙuri...
Tsananin kaiwa Number 9 a munafurci ne wani azzalumi yace maka wai laifukanmu ne ya hanamu zaman lafiya kana ya kawo bala'in ta'addancin da ake mana...
Ba wai kuma ina nufin laifi ba zai zama fitina ba, a'a amma dai tsananin ƙin Allah ne wani wanda lokacin gwamnatin baya bai san ana laifin ba sai yanzu don ya kai almuri yace wai ai laifin mune...
Akwai ƙasashen duniya da duk wani laifi da kasan anayi a Nigeria to can an ninkashi (saurari wa'azizzikan Sheikh Bashir Ɗanfili Sokoto). Misali akwai ƙasashen da sun halarta auren jinsi da zina a fili da shan giya da rushe masallatai ma, kai da sauran nau'ikan laifukan da ba don Allah yasa munzo a zamanin fiyayyen halitta ba, da yanzu wani zancen ake, amma waɗannan ƙasashe sune kan gaba a zaman lafiya, saboda adalcin shuwagabanninsu.
Ya kamata mu sani cewa komin yadda kafirci yake yakan zama cikin salama inda adalci, akasin haka kuma kan faru da Musulunci ko shakka babu..
Ba wani ɗan iska a Nigeria da zaice wai laifinmu yasa ƴan ta'adda ke kashemu malam, Allah ya jarabcemu da asalin azzaluman shuwagabanni ne kawai a sama kana ya jarabcemu da azzaluman malamai da a bakinsu kaɗai Allah yake...
Kuma ai ya kamata mu sani shin su laifukan da ake cewa daga 2015 zuwa yanzu ne aka fara su don haka sai yanzu hukuncin yazo?
Allahumma dammirhum tadmira.🙏
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Sabon Gari
Katsina