Arewa Daily Updates
20/02/2026
RAMADAN 03 🌙✨
SAƘON BARKA DA SHAN RUWA.
Daga Dan takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Funtua/Ɗandume,
Hon. A.A. Basheer Funtua.
Yana miƙa saƙon barka da shan ruwa ga daukacin al’ummar Musulmi, musamman al’ummar ƙananan hukumomin Funtua da Ɗandume, bisa nasarar kammala azumin yau cikin koshin lafiya, natsuwa da zaman lafiya.
Wannan wata mai alfarma wata ne na ibada, hakuri, tausayi da kyautatawa juna. Wata ne da muke ƙara kusantar Ubangijinmu ta hanyar azumi, salloli, addu’o’i da ayyukan alheri. Ina kira gare mu gaba ɗaya da mu ci gaba da dagewa wajen ibada, taimakon marasa galihu, da kuma ƙarfafa zumunci a tsakaninmu.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi azuminmu da sauran ibadunmu, Ya gafarta mana kura-kuranmu, Ya yafe mana zunubanmu, Ya azurta mu da rahamarsa da albarkar wannan wata mai girma.
Yana kuma addu’ar Allah Ya tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da cigaba a ƙasarmu baki ɗaya, musamman a Funtua da Ɗandume.
Allah Ya maimaita mana Yasa Muna cikin waɗan da Za'a ƴanta.
Ramadan Kareem.
01/02/2026
TAYA MURNA!
Hon. Basheer Abdullahi, wanda aka fi sani da A.A. Basheer Funtua, a ranar Assabar, 31 ga Janairu, 2026, ya halarci Bikin Kammala Karatu Karo na 45 Wanda Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya ta Gudanar, inda ya kasance a matsayin ɗaya daga cikin ɗaliban da s**a kammala digirin digirgir (MSc) a fannin Kimiyyar Siyasa da Nazarin Harkokin Kasa da Kasa.
An gudanar da bikin kammala karatun ne a babban harabar jami’ar da ke Zariya, wanda ya kasance wani muhimmin mataki a tafarkin ilimi, tare da nuna sakamakon shekaru na jajircewa, ladabi, da kwazo a harkar ilimi.
Nasarar kammala wannan karatun na digirin digirgir ta Hon. Basheer Abdullahi na kara tabbatar da jajircewars a ga neman ilimi, bunkasa basira da ilimi, da kuma gina kwarewa domin inganta shugabanci nagari da hidimar Al’umma.
Halartarsa a wannan biki na nuni da cikakken imani da yake da shi cewa ilimi ginshiki ne na ci gaban kai da kuma habakar al’umma baki daya.
Muna ƙara tayashi Murna tare da Addu'o'i Sosai akan Ubangiji Allah yasa Albarka a cikin wannan Karatu da yayi cikin Nasara tare da sakamako mai ƙyau.
20/12/2025
UWARGIDAN GWAMNAN JAHAR KATSINA
HAJIYA ZULAIHAT DIKKO UMAR RADDA TA YABAMA SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR FUNTUA BISA AYYUKAN RAYA ƘASA DA CIGABAN AL'UMMA.
Yau Assabar, 20 ga Disamba, 2025, Mai Girma (First Lady) Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina,Hajiya Zulaihat Dikko Umar Radda, PhD, ta kai ziyara ta aiki zuwa Garin Funtua, inda ta kaddamar da manyan ayyukan raya kasa guda biyu (2) da Gwamnatin Karamar Hukumar Funtua ta aiwatar domin amfanin al’umma a karkashin Jagorancin Hon Alh Abdulmutallab Jibrin Goya.
A yayin ziyarar, Uwargidan Gwamnan ta kaddamar da Babbar Cibiyar Lafiya ta Zamani (Primary Health Care – PHC) da ke Sabuwar Abuja, tsallaken Bye-pass Funtua, wadda aka sanya mata suna (Audu Goya Community Health Clinic). An bayyana cewa wannan katafariyar cibiyar lafiya za ta taimaka matuka wajen inganta kiwon lafiya, musamman ga mata, yara da mazauna yankin da kewaye.
Haka zalika, Hajiya Zulaihat Dikko Umar Radda ta kuma kaddamar da Katafaren Cibiyar Koyar da Sana’o’in Hannu ta Zamani, dake cikin farfajiyar Karamar Hukumar Mulki ta Funtua, wadda aka sanya mata suna Her Excellency Hajiya Zulaihat Dikko Umar Radda Skill Acquisition Centre. Cibiyar na da nufin bai wa matasa da mata horo a fannoni daban-daban na sana’o’in zamani domin dogaro da kai da rage zaman banza.
Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina ta bayyana matukar farin ciki da gamsuwa bisa ganin wadannan ayyuka na raya kasa, inda ta yabawa Shugaban Karamar Hukumar Funtua, Hon. Abdulmutallab Jibrin Goya, kan yadda yake gudanar da ayyukansa da jajircewa ba dare ba rana. Ta ce ayyukan da yake aiwatarwa ayyuka ne na zahiri a kasa, ba furuci kawai ba, tare da jaddada cewa ya zama abin koyi a tsakanin dukkan Shugabannin Kananan Hukumomi a Jihar Katsina.
A nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Funtua ya nuna matukar godiya bisa wannan ziyara ta aiki da kuma amsar gayyata da Uwargidan Gwamnan ta yi. Ya bayyana cewa kaddamar da wadannan ayyuka alama ce ta hadin kai da goyon bayan Gwamnatin Jihar Katsina ga ci gaban Karamar Hukumar Funtua.
A yayin taron, an kuma karrama Hon. Abdulmutallab Jibrin Goya (Audu Goya) da lambar yabo ta Gwarzon Ciyamomin Jahar Katsina, ciki har da lambar yabo zuwa ga His Excellency Gwamnan Jihar Katsina, Sai lambar yabo da Girmamawa Ga her Excellency Hajiya Zulaihat Dikko Umar Radda bisa gudunmawar da take bayar wajen ci gaban al’umma musamman Marayu da Marasa ƙarfi, da aiwatar da ayyukan raya kasa a cikin jahar Katsina.
Masu sharhi sun bayyana cewa wadannan ayyuka za su kara haɓɓaka ci gaban tattalin arziki, walwalar al’umma da samar da ingantaccen rayuwa ga al’ummar Funtua, tare da kara tabbatar da kudurin Gwamnatin Karamar Hukumar Funtua na aiwatar da manufofin raya kasa masu dorewa.
Taron ya samu halartar Manyan mutane daga ciki da wajen karamar Hukumar Funtua,Akwai matan Shuwagabannin kananan hukumomin Sabuwa, Faskari, Dandume da Danja, Akwai Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtua Alh Sambo Idris Sambo, Akwai Sardaunan Funtua Alh. Akilu Babai, Director (NAK) Alh Alaliya Funtua, Shugaban jamiyyar APC ta Funtua, Barr. Muhammadu Sani, Kansiloli na karamar Hukumar Funtua, Shuwagabannin Ma'aikatan lafiya na karamar Hukumar Funtua, Ma'aikatan karamar Hukuma, Alh Babangida BB Oil, Da sauran Dukkanin Shuwagabannin jam'iyya Maza da Mata, Shuwagabannin Addini, Shuwagabannin Al'umma da sauran Ilahirin Al'ummar yankin Sabuwar Abuja, dunbin Masoya da Masu Fatan Alkairee.
16/12/2025
FUNTUA LOCAL GOVERNMENT CHAIRMAN FLAGS OFF DISTRIBUTION OF RELIEF MATERIALS BY THE OFFICE OF S.A. YOUTH & SPORTS
On Tuesday, 16th December 2025, the Chairman of Funtua Local Government Area, Hon. Abdulmutallab Jibrin Goya, officially flagged off the distribution of relief materials provided by the Office of the Special Adviser on Youth & Sports, aimed at supporting vulnerable residents across Funtua Local Government Area.
The relief package comprised 500 large blankets, 22 cartons of Omo detergent, 10 cartons of bathing soap, as well as 250 cold-weather clothing items for both children and adults. The items were distributed to male and female beneficiaries, including the visually impaired, persons living with disabilities, orphans, the less privileged, and individuals with mental health challenges, drawn from the 11 wards of Funtua Local Government Area.
The intervention was implemented under the leadership of the Office of the Special Adviser on Youth & Sports to the Chairman of Funtua Local Government, who also serves as the Chairman of all S.As on Youth in Katsina State, Hon Aminu Khalil . The initiative forms part of ongoing efforts to alleviate hardship, improve welfare, and enhance the overall well-being of the people.
The event attracted a large turnout, particularly youths of both genders, and was graced by several dignitaries, including Hon. Bara’u Yusuf Maikwai Dukke, Supervisory Councilor for Health, Funtua Local Government Area. Also in attendance were leaders of Izala and Darika groups, the Director of E.S.D., Alhaji Hassan; Alhaji Nura Sani, Supervisory Councilor for E.S.D.; the Information Officer of Funtua Local Government Council; leaders of political parties; Supervisory Councilors; Special Advisers; and youth leaders.
In his address, Hon. Abdulmutallab Jibrin Goya expressed immense satisfaction at the joy and relief evident on the faces of the beneficiaries. He reaffirmed his administration’s commitment to sustained community support, with particular emphasis on assisting the most vulnerable members of society.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Katsina