MASTV
21/11/2025
Mai girma Ma'adakin Zazzau, Alhaji Munir Jafaru ya ɗauke wa ɗalibai 4 da muka karrama a ƙarƙashin Sheikh Albaniy Zaria JAMB Excellence Award for Indigenes of Zaria and Sabon Gari Local Governments ɗawainiyar biyan kuɗin registration na shekaran karatunsu na farko.
Ɗaliban guda 2 ƴan ƙaramar hukumar Zaria biyu ƙaramar hukumar Sabon Gari duk sun samu admission a ABU, biyu Medicine, sauran Pharmacy da Computer Engineering.
Har ila yau, shi mai girma Ma'adakin Zazzau ne ya taimaka ɗaya daga cikinsu ya samu admission a Pharmacy a lokacin da Medicine yaƙi samuwa.
A madadin waɗannan ɗalibai da iyayensu, muna miƙa godiya ta musamman ga mai girma Ma'adakin Zazzau da fatan Allaah Ya ƙara maka ɗaukaka duniya da lahira, Ya jiƙan magabatanka, Ya sa ka gama da duniya lafiya. Aameen.
Daga shafin Prof Nafiu Abdu
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Nasarawa GRA
Kano
VERIFIED