Iambello143

Iambello143

Share

12/02/2026

Abu biyar (5) da zaka bincika alokacin zaɓar matar aure:

1. Gwajin aminci alokacin talauci:

Kafin ka aure ta, ka gwada amincinta a lokacin da kake da arziƙi da kuma lokacin da arziƙinka yayi ƙasa

Wasu matan zasu zauna dakai idan kanada arziƙi, dagabaya idan ka haɗu da jarrabawar karayar arziƙi sai su kasa jurewa

Shin tana iya jure matsin rayuwa ko ƙalubale?

Idan bata iya jure sauyin yanayi, ƙalubale ko jarrabawa, to kar ka aure ta.

Hanyar da zaka jarraba budurwarka:

Ka ɗauki tsawon lokaci batare da bata kyauta ba, idan tayi magana sai kace bakada zarafi. Ka nuna cewa kana cikin yanayin karayar tattalin arziƙi domin ganin yadda halayenta zasu sauya agareka.

2. Gwajin fushi:

Dole kasan yadda take sarrafa fushi

Idan mai saurin fushi ce, to karka aureta.

Ka motsa motsin zuciyarta. Ka ƙirƙiri ƙaramin rikici.

Ba don cutarwa ba, sai don lura.

Shin tana zagin ka?
Shin tana raina ka?
Shin tana ƙoƙarin rushe ka?
Ko kuwa tana nutsuwa acikin fushi?

3. Gwajin son kai:

Kana buƙatar sanin tana kula da kai da gaske, ko kuma abin da take samu daga gare ka kawai take baiwa muhimmanci

Ka dogara da ita na wani lokaci
Ka riƙa neman taimakonta akai akai

Mace mai tausayi zatayi ƙoƙarin nema maka mafuta idan kana acikin halin neman taimako ko ƙunci

Mace mai son kai zata janye maka idan kana neman taimakonta

Tausayi ba daga kalamai bane, tausayi yana cikin kyautatawa da hidimtawa miji.

4. Gwajin biyayya:

Biyayya ba rauni ba ce, amincewa ce

Shin tana yimaka biyayya idan ka yanke hukunci?

Shin tana jayayya da hukuncinka?

5. Ladabi da tsari:

Shin tana taimakonka wurin kula da dukiyarka, da hanaka almubazzaranci?

Wasu mata suna almubazzaranci da dukiyar miji, abinci da sutura

Mace mai almubazzaranci ba zata iya taimakawa miji ba, sai dai ta rosa mijin

Kuma mafiyawansu basa godewa miji bisa ɗawainiyar da yakeyi dasu. Kullum cikin kuka da yawan ƙorafi.

⚠️ Wallahi ku san matan da kuke aura, mafiyawan matasa su ke ɗebowa kansu wahala.

Iambello143

16/09/2025

Free your mind with any rubish focus your dream

Want your business to be the top-listed Media Company in delta state?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Delta State