Duniyar Littatafai
D🅰️G🅰️ T🅰️IMAKO
TRUE LIFE STORY
PAGE 3
K'aro s**a yi da Abdulmajeed daya taho band'akin a guje,kankameshi tayi
sosai tana nuna band'akin in banda rawa babu abinda jikinta ke yi, "ke Wai mai yake
damunki ne menene acikin ban dakin? Abdulmajeed yace yana kokarin raba jikinsa da
nata, k'ara kankameshi tayi tana nuna band'akin, gaba d'aya ta firgice, tsaki yayi
yace " wlh wani sa'in idan kika yi Abu k**ar na rufeki da duka, ni cikani inga abinda
yake cikin band'akin, yace yana kokarin raba jikinsa da nata, ina ai k'ara
rungumeshi tayi gam tana kuka sai gumi take, haushi ne ya rufe Abdulmajeed daya ga
taki magana sai nuna mishi band'aki take,yakice ta yayi da k'arfi daga jikinsa ya
nufi band'akin Muhibba ta saki wani k'ara ta bishi aguje ta k'ara rungumeshi,adai
dai lokacin daya bud'e band'akin yana karewa ko ina kallo, babu abinda yagani daya
wuce butocin data dura Ruwa aciki, sai mudubin dake jikin bango,tsaki yayi ya d'auki
bokitin wankan, Muhibba kuwa tana makale abayansa, janyota yayi ta dawo gabansa yace
" Muhibba Wai yau mai yake damunki ne ko dai gamo kika yi? Yanzu menene a cikin
ban d'akin nan daya baki tsoro, banasan irin wannan wasan Sam ya k**ata ki sani,idan
ina cikin mode din wasa kin sani, idan bana cikin mode din wasa ma kinsani, dan
haka in wasa ma k**e min ki daina banaso"magana take sanyi amma inta tuna
murd'adden Halin Abdulmajeed sai ta fasa dan ita kanta wani sa'in tsoronshi take ji
dan har mamakin yanda akayi ta aureshi take, duk da yana da wuyan sha'ani wani sa'in
dan akwai shi da tsare gida,wuceta yayi yaje ya debo ruwan wankan yakai
band'akin,ganin yana kok'arin rufo k'ofar ne yasa tayi sauri ta k'arasa band'akin
dan wani irin tsoro ne ya rufeta, had'e rai yayi yace " menene?" Hawaye ne ya hau
zubo mata tace "dan Allah bari na jiraka a band'akin kayi wankan tsoro nakeji wlh"
ayanayin da tayi maganar ne yasa yaji tausayinta yace to "k'aro mana ruwan wankan
sai muyi wankan tare dan dama bakiyi wanka ba,ni yau bansan mai yake damunki ba" da
Sauri ta kinkinmo bokitin ruwan ta shiga band'akin dashi,jikinta sai rawa yake
Kalle kalle tafara yi dan gani take zata iya ganin wannan matar,Abdulmajeed brush ya
farayi,hakan data gani ne yasa itama ta matsa jikin mad'ubin dake rataye aband'akin
ta zura hannu a dan kwandon dake mak'ale ajikin mudubin dan ta d'auko brush d'inta
da MacLean itama tayi brush,k**ar cewa akayi ta kalli madubin,matar nan ta hango a
mudubi ta tsaya ajikin bango tana mata murmushi hakoranta amadadin farare jajaye
ne,wani irin gigitacen k'ara ta saki ta zube a band'akin a sume,sallati Abdulmajeed
yayi ya kinkimeta yayi waje da ita, a d'aki ya kwantar da ita, ya debo ruwa yazo
yana yayyafa mata,ajiyar zuciyar tayi ta bude idonta ahankali,kuka ta fashe dashi
ta rungume Abdulmajeed tana "Abdul na shiga uku na lalace D🅰️G🅰️ TAIMAKO, na janyo wa
kaina masifa laifine dan na taimaketa,meyesa take San cutar dani" duk maganar da
take kuka take jikinta na rawa,Abdulmajeed d'agota yayi yana share mata hawaye yace
" Muhibba mai ya faru wa kika taimakawa? Ki fad'amin gaskiyar abinda ya faru dan ni
ina dawowa nasan ba dai dai k**e ba,dan gabad'aya a firgice k**e, "tunani Muhibba
ta fara yi, na, ta fada mishi gaskiyar abinda ya faru,wani tunani tayi kwanakin
baya wasu 'yan mata sun zo lokacin Abdulmajeed yana nan, 'yan matan s**a ce ta
taimaka musu da ruwan sha,shigowa tace suyi tayi musu jagora har palo,ta debo musu
ruwan s**a sha daga nan kuma hira ta barke musu kasancewar mata akwai saurin
sabo,suna cikin hirar Abdulmajeed ya shigo yace su fita su bar mishi gida,jiki na
rawa s**a bar gidan,aranar Abdulmajeed kwana yayi yana mata fad'a k**ar ya
daketa,Ya kuma ce mata duk lokacin da ta k'ara barin bakon mutum ya shigo masa
gida,sai ya d'auki mumunan mataki akanta,da wannan tunanin tak'i gayawa Abdulmajeed
gaskiyar abinda ya faru,Abdulmajeed ganin tayi shiru tak'i magana ne yasa yaji
ransa na baci wani irin tsawa ya daka mata yana " ina tambayarki kin yi shiru wa
kika taimakawa yake Neman cutar dake" jikinta ne ya hau rawa tsoron Abdulmajeed ya
rufeta magana tafara yi tana kuka "wata tsohuwa ce dazu tazo bara tace na taimaka
mata da sadakar abinci,shine na bata,ta tafi,tunda ta tafi take tsoratani duk Inda
nayi sai na ganta"wani mugun tsaki yayi ya mik'e "Dana San abinda kika yi kenan wlh
ko saurarenki ba zanyi ba badai bakya jin magana ba ki cigaba watak'ila ma aljana
kika taimakawa,ke gaki uban yan San taimako,hanyar waje yayi ta bishi da gudu,tana
tsaye a band'akin yayi wankansa ko kallonta bai yi ba,itama cire kayanta tayi
dasauri ta watsa ruwan duk abinda take yi idonta a rufe dan gani take inta bud'e
idonta zata iya ganinta,a tsakar gida ta k'arasa sa towel dan Abdulmajeed fitowa
yayi ya barta a band'akin,alwala tayi tabi bayan Abdulmajeed daya shige d'akinsa
yana shimfid'a sallaya,doguwar Riga tasa ta zura hijabinta ta tsaya daga
bayansa,sai da s**a yi sallar magriba kafin s**a yi isha,Muhibba addua ta ringayi a
sujadar karshe tana addua'r Allah ya rabata da sharrin matar da ta taimaka
wa,Abdulmajeed Palo ya nufa bayan sun shafa,biyo shi tayi da sauri ko hijabin
jikinta bata cire ba, a tsakiyar palon ya zauna inda ta jera abincinsa,zama tayi ta
ta d'auki plate tafara zuba abincin jikinta sai rawa yake dan har yanzu tana ganin
fuskar matar a idonta,ajiye plate d'in tayi a gabansa bayan ta zuba mai
abincin,bismllah yayi,yafara cin abincinsa Muhibba kuma ta zauna tayi tagumi tana
hawaye,"ke bazaki ci abincin ba kenan"? Abdulmajeed yace batare da ya d'ago ya
kalleta ba,Share hawayen daya zubo mata tayi tace " a koshe nake bana jin yunwa"
Abdulmajeed d**owa yayi ya kalleta ya ajiye cokalin Hanunsa,yace," Wai Muhibba
kukan mai k**e yine,wani ne ya aike ki bawa tsohuwa abinci,ke kika fi kowa San
kiyi taimako,haka kika ga sauran makotanki nayi,ban hanaki taimako ba amma na fad'a
miki kinsan irin wayanda zaki na taimakawa dan tun daga lokacin da Aunty Ainau
(yayarsa) ta bawa Almajiri sadaka ta kamu da rashin lafiya mai tsanani sai da akayi
dagaske aka gano Ashe almajirin nan ba mutum bane Aljani ne, Ashe kudin nan da ta
bashi sadaqa dashi ya ringa cutarta sai da aka runga adduoi ana sauk'ar qurani
kafin ta samu lafiya, wlh tun daga lokacin nake tsoron in taimakawa Wanda bansani
ba, dan kai da zuciya d'aya za kayi taimakon amma akarshe Wanda ka taimakawa ne yake
cutarka shiyasa nake hanaki kwashe kwashe," tunda ya fara magana taji wani tsoro
ya kuma rufeta, matsawa tayi kusa dashi da sauri tana " Abdul yanzu ya zanyi wlh
bansan ba mutum bace "tace tana fashewa da kuka,"ki kwantar da hankalinki kiyi Addu'a
insha Allahu,Allah bazai bata ikon cutar dake ba,this would serve you a lesson
next time zaki San irin wayanda zaki ringa taimaka wa, yanzu dai ki zuba abincin
nan kici sai na raka ki kiyi alwala kizo ki kwanta, "Abdulmajeed yace yana bud'e
kular abincin, dakyar taci cokali uku ta ce mishi ta koshi, kwashe kwanukan yayi da
kansa ya kai kitchen, yace mata tazo tayi alwalar, alwala tayi a tsakar gidan kanta
a sunkuye dan gani take inta d'ago zata iya ganin Matan nan, dakinsa ta nufa
dasauri ta rufo kofar, dan Abdulmajeed har ya kwanta,
shiryawa tayi cikin kayan
bacci, ta fesa turare ta kwanta agefensa k**ar zata shige jikinsa sabida har yanzun
a tsorace take, tashi yayi zai kashe fitilar dakin tayi sauri ta riko shi "dan
Allah Abdul karka kashe wutan dakin wlh tsoro nake ji" wani kallo ya watsa mata
yace " kin tab'a ganin nayi bacci fitila a kunne, kashewa zanyi dan bazan iya bacci
ba inna barshi a kunne, ke kika sa tsoro aranki amma ina gefenki mai zai tsorata
ki, "sauka yayi ya kashe fitilar dakin tayi sauri ta runtse idonta da karfi dan
tuni duhu ya mamaye dakin, yana kwanciya ta rungumeshi gam,shi kuwa ya lalubo
bakinta ya fara k'issing d'inta,duk abinda yake idonta a rufe yake gam,ko kwakwaran
motsi bata yi,shi kadai yayi kidansa yayi rawansa,sai wajen k'arfe biyu ya
k'yalleta aikuwa nan da nan barci yayi awon gaba da ita, wajen k'arfe hud'u ta juya
da zumar ta gyara kwanciyarta,ji tayi hanunta ya sauk'a akan Abu k**ar
gashi,shafawa tayi dan ta gaskata gashin ne, ji tayi gashi ne mai tsayin gaske, bud'e
idonta tayi a hankali tayi tozali da wanan matar a kwance a gefenta ta kura mata
ido bakinta a bud'e jajjayen hakoranta kuwa awaje, wani mugun ihu ta saki ta rufe
idonta gam
Idan Bamga 1k React Ba bazamuci Gabaa😏
AUREN SADAKA
NA
Allah ka yi mana gafara ka jiƙan iyayenmu da duk Al'ummar Musulmi
*1&2*.........................Sa'adatu shi ne asalin sunana amma ba a kirana da shi haka sai ɗai aikun mutane ne suke kirana da hakan amma yawanci anfi kirana da Sa'ade saboda ɓata suna irin na mutanen gari ma sai aka daina kirana da Sa'aden ake cemin Ade kawai haruffan ƙarshen sunan kenan don haka duk ragowar sunayen Sa'adatun da Sa'adah da Sa'aden da Sa'a duk sai s**a ɓata aka koma Ade kawai saidai kawai wanda na tsira a gunsu Mamana da ƴan uwana sune suke faɗamin sunana mai daɗi amma even haka bazasu faɗi ba tun ina faɗa da fishi bare da nake mai zafi har na gaji na sallama musu,
Ƴan asalin garin Kano ne mu ta dabo timbin giwa ko da mai kazo an fika tsakiyar Birni cikin Unguwar Ƙofar Na'isa Mahaifina kenan shi ne haifafffen nan Mahaifiyata kuma ƴar asalin jihar kaduna ce cikin garin zaria kenan a nan ya Aurota ya kawota kano cikin ahinsa.
Gidanmu Babban Gida ne Family house da kakarmu wadda ta haifi mahaifinmu da yayyen mahaifinmu da ƙannensa su da matansu facaloli duk haka ake cakuɗe a gidan ana zaune kowa da sasanta amma kasancewar gidan k**ar na gado tun da cancan tun mahaifinsu yana da rai ya bar musu gidan ya ce kowa yayi Aure ya sa matarsa a ciki bai yadda wani ya fita waje ya zama bare ba bayan babu ransa duk wanda ya fita to bai yafe ba, shi ne s**a gyara gidan akai masa gyare gyare sosai kasan cewarsa Baban nasu mutum ne mai arziƙi na gaske tun a zamanin da yana zuwa fatauci gari gari ya tara arziƙi da dukiya mai yawa ya mutu ya bar musu Gado Da s**a girma kuma sai arziƙinsu ya daɗa faɗaɗa don kaf cikinsu babu wanda bai bawa miliyoyi baya ba, kowa yayi Aure da matansu da ƴaƴansu
Mahaifinmu Shi ne ƙaramin cikinsu Baba Abdulhadi shine Babbansu ana kiransa da Alhaji Hadi, Sai na biyun Baba Musa ana cemasa Alhaji Kalla sai na ukunsu Alaji Isuhu, muna kiransa da Baba Isuhu sai na Huɗunsu Baba Maigida ni ban ma san sunansa na Gaskiya ba don haka na taso naji ana cemasa sai ɗan Autansu Abbanmu Salahu shi kansa baya son sunan Har yana faɗama Kaka mahaifiyarsa ta ce to in bayaso yana iya zuwa ya sayo sabon rago ya yanka amma ita bazaya zo ya dameta ba saboda ya sha faɗa mata haka ya kance Kaka bazan canza ba amma zan daina amfani da shi ba don da yawa ma bazasu sanshi ba Ya koma Alajin kawai sak**akon sauran ƴan uwansa da sai an haɗa da sunayensu Alhaji wane to har yai Aure mu ƴaƴansa muke cemasa Abba don haka ma ko a makaranta sunan muke amfani dashi k**ar ni Sa'adah Abba, don kowa da haka yasan ni indai ƴan makarantarmu ne to Sa'adah Abba mutan gari Kuma Ade.
Ƴaƴan Mamanmu mu huɗu ne maza uku nice Auta ta huɗu Yaya Auwalu shi ne na farko sai na biyu Yaya Sani sai na ukunsu Yaya Salisu sai ni Auta Ade dukansu sun gama karatu suna taɓa kasuwanci kafin Allah yasa aikin ya zo ni kuma ina University yanzu Level one hundred ban daɗe da shiga ba,
Wan Abbanmu na farko Baba Hadi shima ƴaƴa huɗu gareshi duk maza kusan saanin su Yaya Auwal ne saboda bai samu haihuwa da wuri ba Yaya Mahmoud sai na biyunsu Yaya Amin sai na Uku Yaya Umar da Yaya Walid,
Sai Baba kalla shima duk maza Yaya ishaq, Yaya Abdul hadi me sunan Baba Hadi ana cemasa Abdul, sai Yaya zakariyya,sai karaminsu mai sunan Abbanmu salahu Ana cemasa Yaya Deen,
Sai Baba isuhu da Baba mai gida suma maza kowa biyu su Allah bai basu haihuwa da wuri ba yayan Baba mai gida Yaya Junaid da Yaya Ubaid, Sai Baba Isuhu Yaya Safullahi da Yaya Abbas,
Wadannan sune rankatakaf yan uwana na gidan sai uban yawa kusan mu ashirin da biyar a gida daya bataliya guda kenan gashi duk maza, kaf yayan gidan maza ne dukkansu ni kadaice mace a yaran gidan, shiyasa na taso rayuwata k**ar irin ta maza a tsaye nake babu alamun raini sam a tattare dani Babu wanda zai ganni ya kawo min raini don ni mace ce mai k**a da maza Mamana tayi tayi ta gyarani na daina Halina amma ina na kasa to dakinmu maza duk yan gidanmu maza a cikinsu na taso tun ina yarinya cin abinci dasu zuwa makaranta dasu wasa dasu komai na, Mamata babu irin fadan da ban sha ba a wajenta ta ce Babu kyau wasa da maza Sa'ada duk wanda yake wasa da maza Allah zai konashi a wuta amma cikin ikon Allah ina fita wasa maganarnan zata zirare ta bayan kunnena, .
Dambe kam babu irin wadda ban iya ba tamkar yar rustling da harbi da kafa da naushi ga iya hawa bishiya tamkar yar biri to da na girma ne ma na dan samu na rage da rokon Allah da Adduar Mama don lokacin na fara zama yan mata amma dai ina nan yadda nake,
Da na shiga secondary school banada kawaye mata sam sai Abokai maza kala kala daga wannan sai wannan bana tsoron malamai b***e kuma ajega prepet in tamun cin ubanta nake babu abinda ya shafeni akai karata wajen malamai iyakaci nai kneldown ko tsallen kwado wannan ko ba sabona bane bana tsoron ta mutu Ballantana tai rai na fita sanda nakeso nashiga class sanda nakeso Babu mai sani b***e ya hanani raina fes, school bus ma hanani shiga akai saboda masifata ake aiko driver daga gida ya tafi dani,
★★★ ★★★ ★★★
Bayan na dawo a makarantar Boko nai wanka a gurguje naci abinci nai sallah nashiga dakina nai wanka nasa JC kayan Ball dina nadau school bag katuwa na saba nasa cambers dina a ciki da Pcap na zura katon hijab na har kasa ruwan madara na zura slifas na fice falo,
Kamar yadda na zata Mama ita kadai na tarar a falo tana kallo nai mata sallama na ce " Mama na tafi makaranta" ta ce "to yar Albarka yau da wuri hakam"? Na ce "Eh Mama zan bada hadda ne inaso kafin ya sayyadi yazo naje nayi murajia", ta ce "To Allah yayi miki Albarka ya kareminke a duk inda k**e ya shiryaki ya baki ilimi mai Amfani", na Amsa da "Amin Mamata" kamin nasa kaina na wuce,
Ina fita na tarar da Yaya Deen tsaye kan mashin dinsa yana jirana yana ta faman duba Agogo yana doka uban tsaki na karaso zai faramin fada "na dakatar dashi as kaga Yaya Deen dakatamin bakasan da yaya ma na samu na fito ba kasan Mama na nan zaka faramin Bala'i, sanin halina da yayi da naci da mita ya ce "hau hau ni mu tafi ana can an fara muna nan", na ce "to tsaya na cire wannan shegen hijabin kasandai bazan tafi da shi ba naje ya buga ni da kasa Babu gaira babu dalili", na cireshi na cukuikuye na danna a jaka nasa slifas din shima a jakar na dauko booth din takalmina da P-cap na sanya na goya school back din badon gashina da ya leko ba da kirjina da cewa zaayi namiji ce sak, na dare kan mashin din ya tayarda shi yai juyi ya zana kwabo da tayar da kura sananna ya fananoshi a dari da sittin sai filin kwallo na Abacha Youths Center.
Ba mu muka dawo ba sai magriba kuma yayi daidai da lokacin tashinmu makaranta, muna shigowa layin nace ya ajiyeni a bayan gida ya zagaya ya ajiyeni ya nufi masallaci nikuma na sanya hijabina na cire booth din da P-cap na maida slifas din nai bakin get, na tarar ma sun shiga sallah na wuce Sasanmu na leka dakin Mamana tana sallah na maza na shige dakina na kwabe kayan na canza wasu sannan hankalina ya dawo jikina nima nai Alwala nai sallah na,
Na janyo wayata na bude data na hau online, Group dinmu na yan Ball K/Na'isa United na shiga na dudduba sakonni ana ta nemana ma zanyi Adding mutane bana online saboda ni kadaice a group din mace yasa s**a bani Admin, Sallamar Yayyena da naji yasa nai maza na boye wayar karkashin filon katifata na mike na fita nasan halinsu yanzu zaa fara ina nake ana kwadamin Kiran da babu dalili.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Kano
700421