Alkalami

Alkalami

Share

Photos from Alkalami's post 15/07/2026

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Rajiun...

Mutane sha hudu (14) kenan da Allah ya dauki ran-su yau a Jere hanyar Abuja, sanadiyyar hadarin mota.
Mutanen sun taso daga Mashi zuwa Abuja don neman kudi.
An ruwaito cewa mutanen Yan garin Isfawa ne, mazabar Bujawa dake karamar hukumar Mani a Jihar Katsina.
Allah ya jikansu da gafara.

15/07/2026

ABIN MAMAKI A HANYAR KATSINA–ƘANKARA:

Imam Maleek Auwal Warure

'Yan Bindiga Sun Tsayar da Motar Fasinja, Amma Abin da S**a Yi Ya Ba Kowa Mamaki

Wani bawan Allah mai suna Aliyu Ammani, U/Shanu Kaduna ya bayyana wani abin mamaki da ya faru da su yayin tafiya daga Katsina zuwa Kaduna, lamarin da ya bar fasinjojin motar cikin tsananin fargaba da rudani.

A cewarsa, direban motar ya yanke shawarar bi ta hanyar Katsina–Ƙankara, duk da cewa an san hanyar da fama da hare-haren 'yan bindiga. Wasu daga cikin fasinjojin sun nuna rashin amincewarsu, amma direban ya dage cewa babu wata matsala.

Ana cikin tafiya ne ba zato ba tsammani s**a hango wasu mutane dauke da makamai, tare da baburansu a gefen hanya, kamar yadda jami'an tsaro kan kafa shingen bincike.

Direban ya yi ƙoƙarin juyawa, amma ya makara. Sai mutanen s**a yi masa alamar ya ƙaraso inda suke.
Da motar ta tsaya, wani daga cikinsu ya tambayi direban:

"Daga ina kuke?"
Direban ya amsa: "Daga Katsina."
Sai ya sake tambaya: "Ina za ku?"
Direban ya ce: "Kaduna."
Daga nan mutumin ya ce:
"Muna neman fetur. Kuna da shi?"
Direban ya amsa da cewa babu.
Sai mutumin ya ce:
"To, ku wuce. Allah Ya kai ku lafiya."

Motar ta ci gaba da tafiya cikin shiru, kowa na mamakin abin da ya faru. Bayan sun yi nisa, wani fasinja ya yi barkwanci da direban yana cewa:
"Oga direba, idan za ka sake bi wannan hanya, ka tabbata kana ɗauke da gallon ɗaya na fetur. Zai iya zama 'rigakafin' tafiyarka!"

Mekike Tunanin ya faru a nan kuwa? Ku bayyana ra'ayinku a sashin sharhi, sannan ku bi shafinmu domin samun irin waɗannan labarai.

13/07/2026

🚨 AN KAMMALA! Besiktas ta cimma yarjejeniya domin ɗaukar Leandro Trossard daga Arsenal. ⚪️⚫️🦅

Arsenal za ta karɓi Yuro miliyan 20 gaba ɗaya: Yuro miliyan 18 a matsayin kuɗin cinikin farko, sannan Yuro miliyan 2 a matsayin ƙarin kuɗaɗe bisa sharuɗɗa. Haka kuma, Leandro Trossard ya amince da komawa ƙungiyar mintuna kaɗan da s**a wuce. 🇧🇪

Besiktas ta shafe shekara guda tana ƙoƙarin kammala wannan ciniki, kuma yanzu Trossard ya amince da tayin. Ana sa ran zai tashi zuwa Istanbul gobe da dare.

Yaya za ka ba wannan ɗaukar ɗan wasan maki daga 1 zuwa 10? 💣

13/07/2026

Arsenal na matsa lamba domin kammala ɗaukar ɗan wasan gaba na Atletico Madrid, Julian Alvarez, kafin fara shirye-shiryen kakar wasanni ta bana wato (pre-season). 🏟️🔜

Gasa daga sauran ƙungiyoyi wajen neman ɗan wasan na Argentina ta ragu, kuma Alvarez a shirye yake ya koma Arsenal, duk da cewa tun farko ya fi son ci gaba da fafata wasan sa a Sifaniya.

Sai dai Arsenal ba ta son ta wuce biyan fam miliyan (£90m) a wannan ciniki, yayin da Atletico Madrid ke neman fiye da fam miliyan (£100m) domin sakin ɗan wasan.

12/07/2026

😅😧 Fuskar Eberechi Eze lokacin da ya ga Martin Ødegaard yana matsa masa lamba domin ya ƙwace masa ƙwallo.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Kano
700221