Kano Observer Hausa
18/09/2021
Cututtukan da Malamai ke fesawa jama'ar Kano sun fi HIV illa. -Baba Impossible.
Kwamishinan harkokin addinai na jihar Kano Dr Tahar Baba Impossible ya ce za a yi doka ta musamman da zata dinga duba ƙwaƙwalwar malamai kafin su fara gabatar da wa'azi.
Kwamishina ya bayyana haka ne ga sashen BBC Hausa cewa, zasu rubuta ƙuduri na musamman zuwa ga majalisar dokokin jihar kano ta bada damar duba ƙwaƙwalwar malamai kafin fara wa'azi a jihar Kano.
Baba Impossible ya Kara da cewa: Cututtukan da Malamai ke fesawa jama'ar Kano sun fi HIV illa".
Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata ne majalisar malamai ta Kano ta mayar da martani kan cewa za a duba ƙwaƙwalwar malamai, inda s**a ce saidai a duba ƙwaƙwalwar yan siyasa.
Zuwa yanzu an cigaba da taƙaddama akan wannan ƙuduri na gwamnatin jihar Kano.
18/09/2021
YANZU YANZU...
Dantakarar Shugabancin Jamiyyar APC a Jihar Kano Alh. Ahmadu Haruna Zago kenan yayin dayakai ziyara ga Mai Martaba Sarkin Rano, Alh. Kabiru Muhammad Inuwa a Fadarsa.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano