Kabo Reporters
29/05/2026
Sen. Kwankwaso ya Amince da Comr Aminu Abdussalam Gwarzo A matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar NDC
Dr Nasiru Gawuna Kuma Dan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya.
_Saifullahi Hassan
21/05/2026
YANZU-YANZU: Fubara ya janye neman kujerar Gwamnan Rivers karo na biyu
Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na kujerar gwamna na jam’iyyar APC da aka shirya gudanarwa ranar Alhamis.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a daren Laraba, Fubara ya ce ya dauki matakin ne bayan dogon nazari da tuntuba da iyalansa da makusantansa.
Ya bayyana cewa zai mara wa duk wanda ya fito takarar jam’iyyar baya domin tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a jihar.
Fubara ya ce shugabanci yana bukatar sadaukarwa, yana mai cewa akwai lokacin da buri na kai dole ya ba muradun jama’a gaba.
“Jihar Rivers ta fi karfin kowane mutum guda, kuma a wannan lokaci mai muhimmanci, zaman lafiya, kwanciyar hankali da hadin kan jihar su ne ya k**ata su fi kowanne buri muhimmanci,” in ji shi.
Ya kuma gode wa magoya bayansa bisa goyon bayan da s**a ba shi tun daga farkon tafiyar siyasarsa, duk da cewa ya fahimci takaicin da wasu daga cikinsu za su iya ji bayan janyewar tasa.
Fubara ya ce shiru da ya yi a baya-bayan nan ya kasance ne bisa dabarar siyasa da kuma kare muradun jihar.
Har ila yau, ya gode wa jam’iyyar APC bisa damar da ta ba shi tare da nuna godiya ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan goyon baya da karfafa masa gwiwa.
Gwamnan ya jaddada cewa janyewarsa daga takarar ba alamar tsoro ko gazawa ba ce, illa sadaukarwa domin tabbatar da ci gaban jihar Rivers cikin hadin kai da zaman lafiya.
Ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da yi wa al’ummar jihar Rivers hidima har zuwa karshen wa’adinsa.
Daily Nigerian Hausa
20/05/2026
Kotu ta bada umarnin kamo dan majalisar tarayya na Kumbotso, Idris Dankawu
Wata kotun majistare da ke Bwari a babban birnin tarayya Abuja ta bayar da sammacin k**a dan majalisar wakilai mai wakiltar ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano, Hon. Idris Dankawu, bisa zargin damfara wanda hakan ya saba wa sashe na 312 na kundin dokar laifuka( Penal Code).
Kotun tana ba da umarnin kamo dan majalisar ne nbayan wani korafi da kamfanin BAMZ Multi Essential Services ya shigar ta hannun lauyansa, Barrista Ahmad Umar Faroukh, yana neman a kamo dan majalisar saboda kin bayyana a gaban kotu.
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin Dankawu da karbar kudin da s**a kai N77,035,069 ta hannun hadiminsa, Isma’il Yakubu Abubakar, wanda ake zargin ya karbi kudin bisa umarninsa.
A cikin korafin da lauyan mai kara, Barrista Ali Jamilu, ya gabatar, ya bayyana cewa Hon. Dankawu ya tuntubi kamfanin a ranar 18 ga Satumban 2025, inda ya yi alkawarin ba su kwangilar girka fitilu masu amfani da hasken rana da kudinta ya kai N77,035,069.
Lauyan ya ce an tura kudin zuwa asusun hadiminsa, Isma’il Yakubu Abubakar, amma ba a aiwatar da yarjejeniyar ba.
Korafin ya kuma bayyana cewa watanni takwas kafin hakan, Dankawu ya shaida wa kamfanin cewa ya samu kwangilar mazaba ta sany fitilun hasken rana kan tituna da kudinta ya kai N770,000,000, inda ya bukaci a biya kaso 10 cikin 100 na kudin kwangilar, wato N77,000,000, kafin a bayar da takardar kwangilar.
An ce an biya kudin ne a ranar 2 ga Oktoban 2025 zuwa asusun Access Bank na hadiminsa.
Sai dai bayan sama da watanni bakwai, ana zargin dan majalisar da hadimansa sun kasa bayar da kwangilar, suna ta bayar da dalilai mabambanta.
Lauyan mai kara ya kara da cewa bincike ya nuna babu wata irin kwangilar da aka bayar, kuma babu wata hujjar kashe kudin da za ta tabbatar da karbar kudaden.
An yi kokarin tuntubar Hon. Dankawu ko hadiminsa ya ci tura, domin wayoyinsu ba sa shiga.
Daily Nigerian Hausa
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Address
Kano