Labarai24
27/01/2026
APC ta musanta yi wa Bello Turji rajista a Zamfara
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya reshen jihar Zamfara, ta musanta yi wa riƙaƙƙen ɗanbindigar nan Bello Turji rajista a matsayin mamban jam'iyyar.
Wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar a Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya ce ɓata-gari ne s**a kirkiro da katin na bogi domin ɓata wa jam'iyyar suna.
"Hankalin mu ya kai ga wani katin jam'iyyar mu na bogi da ake yaɗa wa ɗauke da hoton Bello Turji, inda ake cewa an yi masa rajista a jam'iyyar mu. Wannan ba gaskiya bane," in ji sanarwar.
Yusuf ya ce idan aka yi duba na tsanaki za a iya gane cewa katin na bogi ne.
"Babu wani mutum da za a iya yi wa rajista ba tare da lambar katin ɗan ƙasa ba wanda shi kuma Turji ba shi da ita. Don haka koƙari da wasu ke yi na shafa wa jam'iyyar bakin fenti bai yi nasara ba," in ji kakakin jam'iyyar ta APC a jihar Zamfara.
Binciken farlko da aka gudanar ya nuna cewa wannan kati na bogi da ake yaɗa wa na alaƙa da wani Babangida Aliyu Shinkafi wanda aka dakatar a baya bayan-nan daga shiga shirin yin katin laturoni na jam'iyyar a jihar saboda wasu ɗabi'u mara kyau da yake nuna wa.
An kuma alaƙanta shi da katin ne saboda a shafinsa na Facebook a fara ganin katin jam'iyyar.
02/01/2026
Da Dumi Dumi: Wata Babbar Kotu a Kano ta tabbatar da nadin Hon Abdullahi Zubairu Abiya a matsayin mukaddashin Shugaban Jam'iyyar NNPP na Jahar Kano
Kotun ta amince da dakatarwar da aka yiwa tsohin shugaban jam'iyyar Dr. Hashimu Dungurawa yayin da ta umarce shi da kar ya kara shiga cikin lamarin ta har sai an saurari karar.
Shugabannin jam'iyyar daga Karamar Hukumar sa ne dai s**a dakatar da shi a cikin wannan satin, kuma s**a shigar da kara in da kotun ta sanya ranar 19 ga watan Janairu domin fara sauraron karar.
09/06/2025
Mijina bai yi sata ba kuma duk kudin da ya tara wa Nijeriya sun yi ɓatan-dabo - Maryam Abacha
Maryam Abacha, matar marigayi Janar Sani Abacha, tsohon shugaban soja na Najeriya, ta ce mijinta ya ajiye wa Najeriya kudi, amma aka wawashe su bayan rasuwarsa.
A wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin na TVC, wacce jaridar TheCable ta rawaito, Maryam ta bukaci a kawo hujja da ke nuna cewa mijinta ya boye kudaden sata a kasashen waje.
Abacha ya mulki Najeriya a matsayin shugaban soja da kuma kwamandan rundunar sojin kasa daga 1993 zuwa 1998, kafin rasuwarsa a ranar 8 ga Yuni, 1998.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kwato wasu kaso-kaso na kudaden da ake zargin Abacha ya boye a bankunan kasashen waje.
A cewar rahotanni, daga shekarar 2020, an kwato sama da dala biliyan 3.624 daga cikin kudaden da Abacha ya boye.
“Wa ne shaida na kudaden da ake cewa an boye?” in ji Maryam.
“Ka ga hannu ko shaida cewa kudin na waje ne? Kuma kudin da mijina ya adana wa Najeriya, cikin 'yan watanni sun bace. Babu wanda ke magana a kan hakan.”
Ta ce yadda ake ci gaba da zargin mijinta alamar wani mummunan hali ne da ke addabar al’umma.
“Me yasa kuke dora wa wani laifi? Ko kabilanci ne ko bambancin addini ne ko me ke damun 'yan Najeriya?” in ji ta.
26/05/2025
Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da rasuwar babban baturan yan sanda na karamar hukumar Rano sakamakon wata hatsaniyar da ta faru da safiyar wannan ranar ta litinin bayan da wasu fustattuan matasa s**a afkawa babban baturan yan sandan.
Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan ya fitar SP Abdullahi Haruna ya ce babban baturan yan sandan na karamar hukumar ta Rano CSP Muhammad Baba Ali ya rasu ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano
700104