Taskar Jaridu
03/07/2022
Ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya gargaɗi magoya bayansa da su rinƙa haƙuri da ra'ayoyi mabambanta na ƴan Najeriya don kada hakan ya hana yin maja da wasu jam'iyyu a nan gaba.
Mista Obi ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya gode wa magoya bayan nasa dangane da irin haɗin kan da suke ba shi.
Jan kunnen nasa na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa yunurinsu na yin haɗaka da jam'iyyar NNPP da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, bai yi nasara ba saboda sun kasa daddalewa kan wanda za a mara wa baya a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
Ya bayyana cewa duk da an san halin da ake ciki a Najeriya na fushi da takaici, "ya zama wajibi a yi amfani da kuzarin da ake da shi wurin samun goyon bayan wasu da kuma haɗin kai".
Obi ya yi kalaman ne bayan Rabiu Kwankwaso ya ce ba zai iya zama mataimakin wani ɗan takarar shugaban ƙasa ba a babban zaɓen 2023.
Waɗannan kalamai na Kwankwaso sun jawo ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta, inda magoyan Obi s**a dinga s**arsa da kalamai marasa daɗin ji.
Gimbiya Online ✍
21/06/2022
Dalilin Da Ya Sa INEC Ta Karɓi Sunan Sanata Ahmed Lawan Wanda Bai Shiga Takara Ba, Maimakon Na Shariff Machina Wanda Ya Lashe Zaɓe, Inji Kwamishinan Zaɓe
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana dalilan da ya sa ta aikata abin da wasu su ka yi wa fahimtar cewa kamar ta yi son kai wajen karɓar sunayen wasu 'yan takara da ake ganin cewa ba su shiga zaɓen fidda gwani ba.
Sunan Sanata Ahmad Lawan, wanda shi ne Shugaban Majalisar Dattawa, ya bayyana a jerin sunayen 'yan takarar da APC ta damƙa wa INEC alhali ko takarar zaɓen fidda gwani bai shiga ba.
Sai dai kuma INEC ta ƙi karɓar sunan tsohon Ministan Harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, wanda shi ma takarar shugaban ƙasa ya tafi kamar Lawan, sai daga baya ya garzaya neman takarar sanata a makare.
Lawan dai bai shiga takarar sanata ba, takarar shugaban ƙasa ya shiga, amma sai ga sunan sa APC ta bayar ga INEC a matsayin halastaccen ɗan takarar da ya ci zaɓen fidda gwani.
Yayin da Kwamishinan INEC na Tarayya da ke Jihar Akwa Ibom Mike Igini ya haramta wa Akpabio shiga jerin 'yan takara, shi kuwa Lawal ya samu shiga kai-tsaye, duk kuwa da ƙorafi da barazanar da wanda ya lashe zaɓen ya yi.
Wannan ne ya sa masu sharhi, lauyoyi da 'yan siyasa ke cewa INEC ta nuna son kai, ta ƙi yi wa Machina adalci, sannan ta fifita Lawan kan Akpabio.
A martanin da Mohammed Haruna na INEC ya yi wa marubuci Farooq Kperogi, ya bayyana cewa, "INEC ba ta da ikon ƙin karɓar ko ma sunan wanene jam'iyya ta kai mata.
"Jam'iyya ce ke da ikon gudanar da zaɓe, ita kuma INEC doka cewa kawai ta yi ta je ta sa ido ta ga yadda aka gudanar da zaɓe, ta kai rahoto a hedikwata, idan an bi ƙa'ida ko ba a bi ba.
"Ƙarfin INEC a nan shi ne duk wanda ya kai ƙara kotu cewa an yi masa rashin adalci a zaɓen, to da rahoton mu zai yi amfani ya kai ƙara, kotu ta ƙwatar masa takarar sa."
Kafafen yaɗa labarai sun ba da labarin yadda Akpabio ya shiga zaɓe a makare, da kuma yadda kotu ta haramta wa INEC ta haramta wa APC shiga zaɓen gwamna a Jihar Akwa Ibom.
Sannan kuma an buga labarin da Machina ya ce canja sunan sa da na Sanata Lawan rashin mutunci ne, zai garzaya kotu.
Bashir Machina, wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin APC na Sanatan Yobe ta Arewa, ya bayyana cewa ya yi mamakin ganin yadda APC ta maye sunan sa da na Lawan a jerin sunayen da ta miƙa wa INEC.
Ya ce ya yi mamaki, amma dai ya na fatan kuskure aka tafka, kuma shi ne halastaccen ɗan takarar, wanda ya shiga zaɓen fidda gwani, kuma ya samu ƙuri'u 280, alhalin Sanata Lawan ko takara bai shiga ba.
Machina, wanda tsohon shugaban Ƙungiyar Masu Harkokin Jiragen Ruwa ta Ƙasa ne, ya ce maye sunan sa da sunan Lawan rashin mutunci ne kuma tantagaryar rashin imani ne.
Lawan dai ya yi watsi da shiga takarar sanata, ya shiga takarar shugaban ƙasa. Sai bayan da ya janye a ranar zaɓen fidda gwani ne, bayan nasarar Bola Tinubu, sai ya zabura neman kujerar sanata, ko ta halin ƙaƙa, bayan an yi zaɓe, har Machina ya yi nasara.
Sashe na 31 na Dokar Zaɓe ya ce za a iya canja sunan ɗan takara idan ya mutu ko kuma ya janye don kan sa, ta hanyar rubuta wa INEC wasiƙar sanarwar janyewar.
Machina, wanda ya taɓa yin ɗan Majalisar Tarayya a Jamhuriya ta Uku, ya yi gargaɗin idan ba a mai da sunan sa ba, zai yi ƙara.
21/06/2022
An gwangwanje iyayen wacce tayi batanci ga Manzon Allah a jihar Sokoto Deborah da katafaren gidan cin abinci da jari mai nauyi.
Apostle chibuzer yace anyi hakan ne domin rage musu raɗadin kisan gillar da aka yiwa yar ta su Deborah wacce take daliba ce a jihar Sokoto.
Daga Comr Haidar Hasheem Kano
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Website
Address
No 25, Madatai Street
Kano
700151