G2 Times Post

G2 Times Post

Share

06/06/2026

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah-wadai da hare-haren da Amurka ta kai a gaɓar tekun yankin Sirik da tsibirin Qeshm,” inda ta bayyana hakan a matsayin “keta yarjejeniyar tsagaita wuta ta 10 ga Afrilu da aka cimma.

A cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar ta ce “ci gaba da nuna ƙiyayya da tsokana daga gwamnatin Amurka” na nuna rashin bin dokokin ƙasa da ƙasa da kuma Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ta ƙara da cewa hakan na nuna cewa “Amurka ba ta da niyyar rage tashin hankali ko komawa hanyar zaman lafiya mai ɗorewa.”

Sanarwar ta jaddada cewa Iran na da cikakken haƙƙin kare kanta, tare da kira ga ƙasashen yankin da su mutunta ƙa’idar kyakkyawar makwabtaka, tare da gargaɗin kada su bari “ɓangarorin da ke da mugun nufi” su yi amfani da “ƙasashensu ko wuraren aikinsu” wajen kai hare-hare.

A gefe guda, dakarun juyin juya halin Iran sun ce sun kai hari kan sansanin sojin Amurka da ke Kuwait da kuma hedikwatar Rukuni na Biyar na rundunar sojin ruwa ta Amurka a Bahrain da makamai masu linzami da jiragen marasa matuƙa.

Sai dai sojojin Amurka, Kuwait da Bahrain sun ce sun yi nasarar kakkao dukkanin makaman da aka harba.

Kuwait da Bahrain sun kuma yi allawadai da harin da Iran ta kai.

05/06/2026

Rashin halartar Mai Shari'a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Juma'a nan, ya sanya jinkirin yanke hukuncin da aka tsara yi a kan ƙarar da ke neman soke rajistar jam'iyyun siyasa da dama, ciki har da jam'iyyar ADC (African Democratic Congress) da Accord Party, da kuma wasu jam'iyyu guda uku, saboda zargin keta dokokin tsarin mulki.

Tun da fari dai an tsara yau Juma’a matsayin ranar da ake sa ran Babbar kotu tarayya zata yanke hukunci kan tuhumar da ake yiwa jamíyyun siyasa biyar a Nijeriya na sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya da ak yiwa gyaran fuska a 1999 kan ko akwai damar fafatawa da su a kakar zaben 2027.

Damar ci gaba da kasancewarsu matsayin jam’iyyun siyasa masu rijista wadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta san da zamansu na hannun mai shari’a Peter Odo Lifu na babbar kotun tarayyar dake zamanta a birnin tarayya Abuja.

Jam’iyyun siyasar dake fuskantar yiwuwar soke rijistarsu matsayin jam’iyya wanda wani gundun masana shari’a a kasar s**a shigar da kara gaban kotu sun hadar da Jam’iyyar African Democratic Congress ADC wadda David Mark ke jagoranta, Action People’s Party (APP), Accord Party, (AP) Zenith Labour Party, (ZLP) da kuma Action Alliance Party, (AAP).

Kungiyoyin sa kai hadin gwiwa da kungiyar tsaffin wakilan Al’umma a majalisun kasar, sun shigara da hukumar INEC kara gaban kotun wanda suke bukatar ta haramtawa jam’iyyun siyasar guda biyar shiga dukkan wasu harkokin siyasa a kasar tare da soki rijistar jam’iyyun

05/06/2026

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da cewa mutane bakwai ne s**a rasa rayukansu sakamakon wani sabon rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Darazo.

Wannan rikici na ɗaya daga cikin jerin tashe-tashen hankula da ke sanya mazauna yankunan karkara a jihar Bauchi cikin tsoro da fargaba, musamman a daidai wannan lokaci da ruwan sama ya fara sauka.

Hukumomin tsaro sun bayyana cewa suna kokarin shawo kan lamarin domin dawo da doka da oda da kuma hana sake faruwar hakan.

Rikicin manoma da makiyaya wadda ta samo asali daga taƙaddama kan filayen noma da hanyoyin burtali, ta jefa yankin arewacin Najeriya cikin mawuyacin hali.

Manoma da dama suna rasa rayukansu ko kuma su samu munanan raunuka sakamakon hare-haren sari-ka-noke ko fada na ba-ta-kashi da ke ɓarkewa tsakanin bangarorin biyu.

Sau tari ana ƙone garuruwa da ƙauyukan manoma kurmus, lamarin da ke barin dubban iyalai cikin halin ƙunci da matsuguni.

Shanu kan shiga gonaki su cinye ko su tattake amfanin gona da aka zuba miliyoyin naira kafin lokacin girbi.

Rikicin ya kawo ƙarshen yadda da amana ta ɗaruruwan shekaru da ke tsakanin ƙabilun manoma da makiyaya, lamarin da ke raba kawunan al’ummomin ɓangarorin biyu.

05/06/2026

Yau ake sa ran Babbar kotu tarayya zata yanke hukunci kan tuhumar da ake yiwa jamíyyun siyasa biyar a Nijeriya na sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya da ak yiwa gyaran fuska a 1999 kan ko akwai damar fafatawa da su a kakar zaben 2027.

Damar ci gaba da kasancewarsu matsayin jam’iyyun siyasa masu rijista wadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta san da zamansu na hannun mai shari’a Peter Odo Lifu na babbar kotun tarayyar dake zamanta a birnin tarayya Abuja.

Jam’iyyun siyasar dake fuskantar yiwuwar soke rijistarsu matsayin jam’iyya wanda wani gundun masana shari’a a kasar s**a shigar da kara gaban kotu sun hadar da Jam’iyyar African Democratic Congress ADC wadda David Mark ke jagoranta, Action People’s Party (APP), Accord Party, (AP) Zenith Labour Party, (ZLP) da kuma Action Alliance Party, (AAP).

Kungiyoyin sa kai hadin gwiwa da kungiyar tsaffin wakilan Al’umma a majalisun kasar, sun shigara da hukumar INEC kara gaban kotun wanda suke bukatar ta haramtawa jam’iyyun siyasar guda biyar shiga dukkan wasu harkokin siyasa a kasar tare da soki rijistar jam’iyyun.
G2 Times Post Mr. Peter Obi

05/06/2026

Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci a gaggauta sakin ɗalibai da malaman da aka sace a jihohin Oyo da Borno da ke Najeriya.

Mai kula da sashen ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya Mohamed Malick Fall, ya bayyana damuwarsa bayan wata ganawa da ya yi da jami'an hukumar tsaron makarantu a Abuja.

Mohamed Malick Fall ya jaddada cewa ya kamata makarantu su kasance wuraren neman ilimi cikin aminci, ba wuraren firgici ba, tare da cewa bai kamata yara su zama abin farmaki ba.

‘Ƴan bindiga sun kai hari makarantu uku a Ƙaramar Hukumar Oriire ta jihar Oyo, inda s**a sace ɗalibai da malamai sama da 40, haɗi da jariri ɗan shekara biyu.

Haka zalika, mayaƙan Boko Haram sun kai farmaki makarantar firamare da sakandare ta M***a da ke Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a jihar Borno, inda s**a sace ɗalibai 42.

Al'umma sun fusata bayan da aka bayyana cewa maharan sun kashe wani malamin lissafi mai suna Michael Oyedokun.

Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro na fuskantar ƙalubale, musamman ma a yankuna masu wuyar sha'ani da fargabar asarar rayuka, wanda hakan ya jinkirta aikin ceto ɗaliban da ke tsare.

05/06/2026

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensk, ya wallafa wata buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga takwara aikinsa na Rasha, Vladimir Putin, inda ya gayyace shi zuwa ganawar ido-da-ido domin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi.

Wasiƙar, wadda aka wallafa a shafin intanet na shugaban Ukraine, ta ce a daidai lokacin da hankalin Amurka ya karkata gaba ɗaya kan rikicin Iran, ba zai dace a ci gaba da jiran lokacin da yaƙin Turai zai sake zama babban abin da Amurka za ta mayar da hankali a kai ba.

Zelensky ya kuma ce ƴan Rasha sun fara gajiya da hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da Ukraine ke kaiwa, da kuma matsalar hauhawar farashin kaya da ƙarancin man fetur, don haka a shirye suke su ga an samar da zaman lafiya.

Sa'o'i kaɗan bayan fitar da wasikar, fadar mulkin Kremlin ta Rasha, ta yi martani da cewa ana maraba da Mista Zelensky a birnin Moscow, idan har da gaske yana son ganawa ne da shugaba Putin.

04/06/2026

Majalisar Amurka ta bukaci Donald Trump ya kawo karshen yakin da kasar ke yi da Iran.

04/06/2026

Rundunar ƴansanda a jihar Oyo ta musanta rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta inda ake zargin cewa ƴanbindiga suk sako ɗalibai da malaman da s**a sace a ƙaramar hukumar Orire a jihar Oyo.

Rundunar ta bayyana haka a sanarwar da kakakinta, DSP Ayanlade Olayinka ya sanyawa hannu inda ta ce rahoton ƙarya ce tsagwaranta.

Cikin sanarwar, rundunar ta kuma bai wa al'ummar jihar ta Oyo tabbaci cewa ana ci gaba da ƙoƙari na ganin an kuɓutar da ɗaliban da malaman.

Rundunar ta kuma yi kira ga mazauna jihar da su guji jita-jita su kuma nemi sahihan labarai daga ƴansanda.

Lamarin hare-haren 'yan bindiga da satar mutane don neman kuɗin fansa sun fi ƙamari ne a yankin arewacin Najeriya, inda ba kasafai aka saba ganin hakan ba a kudancin ƙasar, wadda ke fama da matsaloli na tsaro.

A baya-bayan nan ita ma dai jihar ta Oyo na fuskantar matsalar tsaron daga gungun masu aikata laifi

04/06/2026

Abin da Mujaheed Zaitawa yace kan Abba Hikima bayan da ya zargi ya dauko Tallan Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin Inuwar NDC Mr. Peter Obi

03/06/2026

Ma’aikatar Lafiyar Kuwait ta ce aƙalla mutum 63 ne s**a jikkata, ciki har da ma’aikatan filin jirgin sama da fasinjoji, sakamakon harin da Iran ta kai kan Filin Jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Kuwait.

Tun da farko, ma’aikatar harkokin wajen Kuwait ta sanar da cewa mutum ɗaya ya mutu a harin.

Rahotanni sun ce harin ya yi sanadin lalacewar ginin Terminal 1 na filin jirgin saman da kuma wasu wuraren jakadanci.

Iran ta ce Amurka na amfani da ƙasar Kuwait wajen kai hare-hare a kan ƙasarta, kuma tana ɗora alhakin hakan kan shugabannin Kuwait.

A nata ɓangaren, ƙasashen Kuwait da Qatar sun yi allawadai da hare-haren da Iran ta kai, tare da bayyana su a matsayin abin da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


NO. 80 ALI SHUGABA Street
Kano