Ah-Y
Falalar Watan Allah, Muharram
An tambayi Manzon Allah ๏ทบ:
"Wace sallah ce ta fi falala bayan sallolin farilla? Kuma wane azumi ne ya fi falala bayan azumin Ramadan?"
Sai Manzon Allah ๏ทบ ya ce:
"Mafi falalar sallah bayan sallolin farilla ita ce sallar dare (Tahajjud), kuma mafi falalar azumi bayan watan Ramadan shi ne azumin watan Allah, Muharram."
Sahih Muslim 1163 (2756)
Larabci:
ุนููู ุฃูุจูู ููุฑูููุฑูุฉู ุฑุถู ุงููู ุนูู ููุงูู: ููุงูู ุฑูุณูููู ุงูููููู ๏ทบ:
ยซุฃูููุถููู ุงูุตููููุงู
ู ุจูุนูุฏู ุฑูู
ูุถูุงูู ุดูููุฑู ุงูููููู ุงููู
ูุญูุฑููู
ูุ ููุฃูููุถููู ุงูุตููููุงุฉู ุจูุนูุฏู ุงููููุฑููุถูุฉู ุตูููุงุฉู ุงููููููููยป
Muharram yana daga cikin watanni huษu masu alfarma da Allah Ya ambata a cikin Al-Qur'ani. Manzon Allah ๏ทบ ya kira shi "Watan Allah", wanda ke nuna girman matsayinsa da falalarsa.
Daga cikin ayyukan alheri na wannan wata akwai:
โข Yawaita azumin nafila. โข Azumin Ashura (10 Muharram). โข Yawaita istigfari da zikiri. โข Karatun Al-Qur'ani. โข Sallar dare (Tahajjud).
๐คฒ Ya Allah, Ka ba mu ikon cin moriyar watan Muharram da ayyukan alheri, Ka gafarta mana zunubanmu, Ka karษi ibadunmu.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the place of worship
Telephone
Website
Address
Kano
700282