Amintacciya

Amintacciya

Share

09/06/2026

Tunda bayan da Tijjani Gandu yayi waƙar Hayaniyan bana, tiri tirin bana, Matsaltsalun bana, banda mu, Har yau Kwankwasawa cikin matsala suke.

Ba su sake samun zaman nitsuwa ta watanni Uku masu kyau a jam'iyya ɗaya ba.

NNPP - Matsaltsalun Bana

ADC - Tiri - Tirin Bana

NDC - Hayaniyar Bana

Yanzu kuma ana tunanin cewar za su abka cikin Cakwalkalin cakwakiyar bana.

Daga Haj Shehu

08/06/2026

DA DUMI-DUMI: Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Kwankwasiyya da Jam'iyyar NDC Kan Rabon Tikitin Takara a Kano

An samu sabon saɓani tsakanin bangaren Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Jam'iyyar NDC bayan da jam'iyyar ta sauya sunayen wasu daga cikin 'yan takarar da bangaren Kwankwasiyya ya gabatar domin takara a jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa sauyin sunayen ya biyo bayan takaddamar da ta shafi yarjejeniyar rabon tikitin takara tsakanin bangaren Kwankwasiyya da shugabancin jam'iyyar. Yarjejeniyar ta tanadi cewa bangaren Kwankwasiyya zai samu kaso 60 cikin 100 na tikitin takara, yayin da bangaren jam'iyyar da aka tarar zai mallaki kaso 40 cikin 100.

A wata takarda da shugaban NDC na Kano, Hon. Hussaini Isah Mairiga, ya sanya wa hannu, jam'iyyar ta bayyana cewa ta amince da wasu sabbin sunaye domin wakiltar jam'iyyar a wasu mazabu na Majalisar Tarayya da ta Jiha. Jam'iyyar ta ce matakin ya zama dole ne domin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tun farko.

Sai dai bayanan da aka tattara sun nuna cewa bangaren Kwankwasiyya bai ba bangaren jam'iyyar damar samun kason da aka amince da shi ba, lamarin da ya haddasa rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu. Wannan ne ya sa jam'iyyar ta ɗauki matakin sauya wasu daga cikin sunayen 'yan takarar da aka gabatar.

A gefe guda kuma, majiyoyi sun bayyana cewa bangaren Kwankwasiyya bai amince da matakin da NDC ta dauka ba, kuma ana zargin tawagar Sanata Kwankwaso ta fara nazarin yiwuwar ficewa daga jam'iyyar domin komawa jam'iyyar PRP tare da mabiyanta domin samun damar shiga zaɓe ba tare da wata takaddama ba.

Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin wannan rikici na iya sauya yanayin siyasar Kano da ma tasirin Kwankwasiyya a zabukan da ke tafe, musamman idan har bangaren Kwankwaso ya yanke shawarar ficewa daga NDC zuwa wata jam'iyya.

Me za ku ce?

07/06/2026

Kun gane shi ?

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Kano