Queen luba

Queen luba

Share

Photos from Queen luba's post 14/06/2026

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta samu nasarar dakile wani mummunan hari bayan ta gano tare da lalata wata na’urar fashewa (IED) da ake zargin ’yan bindiga sun binne a hanyar Kunchin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe.

An gano bam din ne sak**akon sahihan bayanan sirri da hadin kan al’umma, lamarin da ya bai wa jami’an VCRU da EOD damar gaggauta kai dauki tare da kawar da barazanar kafin ta jawo asarar rayuka.

Rundunar ta yaba wa mazauna yankin bisa hadin kai da bayar da bayanai kan lokaci, tare da tabbatar da cewa tana ci gaba da farautar wadanda s**a shirya wannan aika-aika. Haka kuma an kara yawan sintiri a yankunan domin tabbatar da tsaron matafiya da mazauna jihar.

14/06/2026

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Wallahi halin da al'ummar Dandume ke ciki a yau abin tausayi ne da takaici.

Ana rasa rayuka, ana sace dukiyoyi, ana kuma yin garkuwa da bayin Allah marasa laifi. Al'umma sun gaji da rayuwa cikin tsoro. Iyaye sun gaji da zaman ɗar-ɗar kan 'ya'yansu, mata sun gaji da zaman jimami, yara kuma sun taso suna ganin tashin hankali a matsayin wani ɓangare na rayuwa. 😭

Ya Allah, Kai ne Mai iko a kan komai. Ka kawo mana mafita, Ka kare rayukanmu da dukiyoyinmu, Ka yaye mana wannan fitina. Ka sa zaman lafiya ya dawo a Dandume, Katsina da Najeriya baki ɗaya.

Mun gaji da kuka, mun gaji da zaman fargaba, mun gaji da rasa 'yan uwa da abokan arziki. Allah Ka kawo mana ɗauki.

Ameen summa Ameen 🤲

Photos from Queen luba's post 14/06/2026

Ƴan Sanda Sun Ceto Mutane Uku da Aka Yi Garkuwa da Su a Hanyar Gurusu–Anka

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta samu wani gagarumin nasara a yaƙi da miyagun laifuka bayan jami’anta na Sashen Yaƙi da Manyan Laifuka (VCRU) sun ceto mutane uku da ’yan bindiga s**a yi garkuwa da su a hanyar Gurusu–Anka.

Lamarin ya faru ne ranar 13 ga Yuni, 2026, lokacin da ’yan bindiga masu ɗauke da manyan mak**ai s**a tare hanya tare da sace matafiya uku da ke kan hanyarsu daga Bukuyum zuwa Talata Mafara.

Bayan samun rahoto, jami’an ’yan sanda sun bi sawun maharan zuwa cikin daji inda aka yi musayar wuta mai zafi. Sak**akon dabarun aiki da jarumtakar jami’an, an fatattaki ’yan bindigar tare da jikkata wasu daga cikinsu, yayin da s**a tsere cikin daji.

An yi nasarar ceto dukkan waɗanda aka sace ba tare da sun ji rauni ba. Sai dai maharan sun gudu da wayar Android ta ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, CP Ahmad Muhammad Bello, ya yaba da ƙwazon jami’an da s**a gudanar da aikin, tare da tabbatar wa al’umma cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Kano