Imran Rimee
08/07/2026
Wannar maganar haka take oga sir Ayatullahi Tage indai akan Professor Isa Ali Pantami insha Allah bazamu baka kunya ba 🙌
Mafitarmu Jama’ar Gombe Pantami Ne Bazaici Amanarmu Ba. Bazaiyi Almubazzaramci Da Kudinmu Ba, Inada Yakinin Zai Inganta Rayuwarmu Da Yardar Allah,
Akwai Jinin Gombe Mai Tarin Yawa a Jikina.
Babban Sashen Zuciyata Yana Gombe.
Ni Dan Gombe Ne Halastacce, kada a Min Gorin Gari a Gombe Ni Dan Jaha Ne Ba Agola Bane Ni a Jahar, Allah Ka Kaddara Pantami a Matsayin Sabon Gwamnan Jahar Gombe a 2027
07/07/2026
SAƘON TAYA MURNA
Daga Professor Isa Ali Pantami, MajidaÉ—in Daular Usmaniyya
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.
Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam), da iyalansa, da sahabbansa, da duk waɗanda s**a bi tafarkinsa har zuwa Ranar Alƙiyama.
Ina matuƙar farin cikin miƙa saƙon taya murna na ga shugabanci, malamai, ma'aikata, ɗalibai, iyaye da daukacin al'ummar Imam Asim Integrated School, Gombe, bisa nasarar gudanar da bikin yaye ɗaliban da s**a sauke karatun Alƙur'ani Mai Girma.
Wannan gagarumar nasara shaida ce ta jajircewarku wajen koyarwa da haddar Alƙur'ani Mai Girma, bunƙasa ilimin addinin Musulunci, da kuma tarbiyyar al'umma ta gari. Ina roƙon Allah (Subhanahu wa Ta'ala) Ya albarkaci ɗaliban da aka yaye, Ya sanya Alƙur'ani ya zama hasken zukatansu, jagoran rayuwarsu, Ya kuma ba su ikhlasi, hikima da tsayin daka wajen kiyayewa da aiki da koyarwarsa.
Ina miƙa godiya ta musamman ga Mamallakin makarantar, Sheikh Ibrahim Siddi Hamma, da Shugaban Hukumar Gudanarwa, Sheikh Tahir Elyasin, bisa hangen nesansu, jajircewarsu da kuma sadaukarwar da suke yi wajen bunƙasa karatun Alƙur'ani da ilimin zamani cikin tsarin haɗaka. Allah Ya saka musu da mafificin alheri, Ya albarkaci ƙoƙarinsu, Ya kuma ci gaba da ba makarantar nasara da ɗaukaka.
Haka kuma, ina miƙa godiyata ga Dr. Umar Garba Dokaji da Dr. Yahya Bello, waɗanda s**a wakilce ni cikin karamci a wannan muhimmin taro. Ina matuƙar godiya da irin sadaukarwa da shirinsu na hidima, kuma ina addu'ar Allah Ya saka musu da alheri mai yawa, Ya ƙara musu ilimi, hikima da albarka.
Ina roƙon Allah (Subhanahu wa Ta'ala) Ya ci gaba da ɗaukaka Imam Asim Integrated School, Ya albarkaci shugabanninta, malamanta, ma'aikatanta da ɗalibanta, Ya kuma sanya makarantar ta ci gaba da zama fitilar ilimi mai amfani, kyawawan ɗabi'u da nagarta ga al'ummomi masu zuwa.
Ina sake taya É—aukacin É—aliban da aka yaye, malamansu, iyayensu da duk waÉ—anda s**a ba da gudunmawa wajen samun nasarar wannan biki mai albarka murna.
Jazakumullahu Khayran.
Professor Isa Ali Pantami
MajidaÉ—in Daular Usmaniyya
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Address
Kano