H. Sarina

H. Sarina

Share

16/03/2026
19/02/2026

Dukanmu mun san sallah, azumi, da zakka farillai ne akan kowa. Abin da ake nufi da darika ko sufanci shi ne mutum ya ji cewar zai kara da wasu nafiloli, wuridai, istigfari, da sauran ibadu domin kyautatawa kansa. Duk wani abu da ba a kan haka aka dorashi ba to ba shi ne sufanci ko darikar ba a asali.

Ta fuskar halayya. Wajibi ne mabiyin sufanci ko dan darika ya cirewa kansa duk wani yarda da kai. Kada ya sake ya ji shi salihi ne, mai tsoron Allah, kubutacce, dan aljanna da zunubansa s**a yi karanci.

A koda yaushe ya dinga jin yana da aibuka da suke bukatar ya gyara zuciyarsa kuma kada ya taba ganin wasu masu sabo a kaskantattu, domin ta iya yiwuwa sun fi shi kusanci da Allah.

يا أيها الذين آمنوا لا يسخر قوم من قوم عسى أن يكونوا خيرا منهم ولا نساء من نساء عسى أن يكن خيرا منهن

"Ya ku muminai, kada wasu su dinga yi wa wasu izgilanci kuma su zo su zama sun fi su alkhairi..."

Wannan shi zai sa mutum ya shagala da gyara aibukansa don ya hadu da Allah salin-alin, maimaikon ya matsa sai ya dinga cin zarafin wani mai sabo har ya dinga jin shi ne shugaban masu tsoron Allah wanin kuma dan wuta ne.

فَلَا تُزَكُّوا أَنْفُسَكُمْ هُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ اتَّقَى

"Kada ku tsarkake kanku, Shi (Allah) ya fi kowa sanin masu tsoronsa."

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address


Sarina
Kano