ROGO Reporters Media

ROGO Reporters Media

Share

26/11/2022

Muji tsoran Allah mutaimaki nakasa damu yan uwa

22/10/2022

Wata Sabuwa • Shugaban kungiyar matasan Arewa da ya wakilci matasa a taron dattawan Arewa da Kwankwaso baije ba don kaucewa rikici tsakanin mabiyan sa dana wani ɗan takara Nastura Ashir Sherif yace takarar Atiku da Tinubu kawai ta 'yan jari hujja ce, ta karar Peter Obi kuma ta addini da ɓangaren cine yace takarar Kwankwaso ne kawai mai ingantacciyar manufa ga Nigeria da matasan cikin ta.
=fbl

18/10/2022

JERIN SHAGUL GULAN BIKIN CIKAR JAGORA KWANKWASO SHEKARU 66

RANA TA FARKO JUMA'A 21/10/2022

1. Bude masallacin juma'a da Islamic center wadanda kwankwaso ya gina a kusa da gidansa dake Miller road.

2. Shagalin bikin murnar cikar sa shekara 66 da misalin karfe 4 na yamma a gidansa dake Miller road.

RANA TA BIYU ASABAR 22/10/2022

1. Bude makarantar amana leadership institute a birnin kwankwasiyya city da misalin karfe 10 na safe.

2. Shagalin Bikin murnar cikar gidan Rediyon nasara fm Mita 98.5 shekara biyu da budewa da misalin karfe 1:00pm na rana.

3. Gwajin cututtuka kyauta da bada magani a asibitin amana dake Miller road da misalin 12:00pm na rana.

RANA TA UKU LAHADI 23/10/2022

1. Bude makarantar firamare da kuma bada gudunmawar taransifoma ga jama'ar garin dorawa, karamar hukumar karu jihar Nassarawa da misalin karfe 10 na safe.

2. Taron karawa juna sani da bada tarihin rayuwar Rabiu Musa Kwankwaso a class park event centre dake wuse zone II Abuja da misalin karfe bakwai na dare.

Da akwai ziyarar makabartu, gidajen marayu, gidajen masu rangwamen hankali, gidajen yari da asibitoci da sauran muhimman wurare daga ranar Alhamis 20/10/2022 har zuwa ranar Lahadi. 23/10/2022.

ABIN LURA

Kwankwaso ya samar da makarantar firamare tare inganta ta da kayan aiki a kauyen dorawa dage jihar Nassarawa wanda wannan kauyen ya shafe sama da Shekaru 30 babu makarantar firamare in banda yanzu da senator Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya samar musu da'ita.

Sannan kuma an samar da makarantar amana leadership ne domin horar da matasan mu yadda zasu goge a gobe yayin da s**a hau wata turba ta shugabanci.

Da fatan allah ya karawa rayuwar kwankwaso albarka ya bashi shigabancin Kasar nigeria
Ya cika masa dukkannin burinsa ya biya masa bukatunsa na alkhairi duniya da lahira.

12/09/2022

ZAMAN KOTUN YAU (LITININ) TSAKANIN GWAMNATIN TARAYYA DA ƘUNGIYAR ASUU.

A yau Litinin ne kotun ɗa'ar Ma'aikata, ƙarƙashin jagorancin mai shari'a, Justice Polycarf Hamman, ta fara sauraron ƙarar da Gwamnatin tarayya ta maka ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta ƙasa (ASUU) a gaban ta, tana neman kotun ta tilastawa Malaman komawa bakin Ayyukan su (a yayin da ake cigaba da sauraron shari'ar), tare da buƙatar kotun ta tantance mata ko Yajin Aikin da ASUU ɗin take gudanarwa halastacce ne a idon doka ?, da sauran buƙatu.

Sai dai Jim kaɗan da fara sauraron shari'ar ne , sai ƙungiyar SERAP ta bayyana sha'awar ta ta kasance wa a cikin shari'ar, ta bakin lauyan da ke wakiltar ƙungiyar, Ebun-Olu Adegnoruwa (SAN), yana mai cewar su ma ƙungiyar su ta shigar da ƙara makamanciyar wannan a gaban kotun, inda take buƙatar kotun ta tilastawa Gwamnatin tarayya cika yarjejeniyar da s**a cimma da ƙungiyar ta ASUU, tun a shekarar 2009.

Inda yace SERAP tana buƙatar shiga cikin shari'ar ne domin sauƙaƙawa Kotun sauraron shari'a iri daban-daban, da s**a shafi lamari guda.

Sai dai kuma, Lauyan Gwamnatin tarayya, Tijjani Gazali (SAN), ya soki buƙatar ta SERAP na shiga shari'ar, yana mai bayyana cewar bai kamata waɗanda sunayen su basa daga cikin ƙunshin shari'a, a hange su a cikin shari'ar tsundum ba.

A nasa ɓangaren, fitaccen Lauyan nan, Femi Falana (SAN), da ke wakiltar ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta ƙasa (ASUU), roƙar kotun ya yi da ta ɗage shari'ar zuwa wata rana, domin basu damar gabatarwa da kotun ƙunshin bayanan su, inda shi ma lauyan Gwamnati bai yi s**a ba, ya buƙaci kotun da ta ɗage shari'ar.

Inda anan ne kuma, kotun ta bayyana matsayarta na ƙin amincewa da buƙatar SERAP na shiga cikin Shari'ar, tare da ɗage shari'ar zuwa ranar Juma'a 16 ga watan Satumbar da muke ciki, domin fara gabatarwa da kotun bayanai daga kowanne ɓangare.

✍️Miftahu Ahmad Panda

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


ROGO
Kano
09060314880