AP Hausa
09/01/2022
Maganin hana daukar ciki ya yi karanci a Zariya
Rahotanni sun bayyana cewa, mata masu zaman kansu na kokawa kan rashin samun maganin hana haihuwa na zamani a wasu sassan birnin Zariya, lamarin da ya tilasta wa mata amfani da kwaroron roba na kai tsaye.
07/01/2022
INNALILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI'UN
Allah Madaukakin Sarki Ya karbi rayuwar Sheikh Dr Ahmad BUK a yau juma'a
Duniyar Hadisi tayi rashin kwararren Likitan Hadisi wanda akayi ittafakin babu wanda ya kaishi sanin ilmin Hadisi a Malaman Afirka
Marigayi Sheikh Dr Ahmad BUK ya karantar da manyan Malamai ilmin Hadisi a Nigeria da wasu kasashen Afirka
Daga cikin Dalibansa da ya karantar Hadisi akwai marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Kano, Sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar lemo, Sheikh Dr Idris Abdul-aziz Bauchi da sauransu
Hakika anyi mana babban rashi ALLAHU AKBAR!
Yaa Allah Ka jikan bawanKa, Allah Ka yafe masa laifukansa, Allah Ka hada fuskokinmu da nashi a cikin Aljannah
04/01/2022
Korona ta k**a mutum 199 a Kaduna
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce an samu karin mutum 670 da s**a kamu da cutar korona a faɗin ƙasar.
Daga cikin sabbin wadanda s**a kamu jihar Legas ce ta fi yawan mutane inda ta ke da 277.
Korona ta kuma k**a mutum 199 a Kaduna daga farkon Janairu zuwa ranar Litinin.
A babban birnin Najeriya Abuja mutum 120, sai kwara mai 20 yayin da Abia ke da 14.
A Katsina da Gombe mutum tara tara cutar ta k**a a jihohin, a Bauchi mutum shida
Yawan masu kamuwa da cutar na ƙaruwa a Najeriya, tun ɓullar sabon nau’in cutar korona na Omicron a ƙasar
Nigerian Daily Hausa
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano