Matasan DABO

Matasan  DABO

Share

19/02/2026

Assalamu Alaikum! A madadin shugaban wannan kungiya mai albarka Abdul Wahab Dayyabu tare da mambobin sa muna yin jaje tare da alhinin gobara da ta afku a kasuwar Singa dake jihar Kano. Allah ya mayar musu da alkhairi ya kiyaye afkuwar hakan a gaba. Muna kira ga gwamnatin tarayya ta jiha da shugabancin kasuwar Singa su fitar da tsare- tsare k**ar haka don kiyaye afkuwar hakan a gaba:
1) rage cinkoso a cikin kasuwa.
2) samar da hanyoyi masu fadi a cikin kasuwa.
3) samar da hukuma ta kashe gobara a kasuwanni da kayan aiki na zamani.
4) sa ido akan abin da ya shafi wutar lantarki ko wutar solar a ko ina na kasuwar.
Muna ganin idan aka yi amfani da wadannan shawarwari zasu taimaka sosai.
A karshe muna kira ga masu hannu da shuni dasu taimakawa yan kasuwar da abin ya shafa. Ita kuma gwamnati da sauran hukumomi su tabbatar duk taimakon da aka bayar yaje wurin wadanda ya dace. Allah ya kiyaye gaba ya mayar da alkhairi.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address


Zoo Road
Kano