APA Hausa
27/05/2026
Dan Takarar Gwamnan Jihar Gombe A Karkashin Jam’iyyar PDP, Professor Isa Ali Pantami CON (Majidadin Daular Usmaniyya), Ya Jagoranci Sallar Idi A Masallacin Al-Ahfad Nasarawo Dake cikin Kwaryar Jihar Gombe
27/05/2026
Yayin Da Sarki Sanusi II Ya Jagoranci Gwamna Abba Kabir Da Mataimakinsa, Murtala Sule Garo Yin Sallar Idi A Kano
27/05/2026
Jarumin Finafainan Hausa, Ali Rabi'u Ali (Daddy) Tare Da Iyalansa A Ranar Sallah
24/05/2026
Tinubu ya lashe zaɓen fitar da ɗan takarar shugabancin Najeriya da ƙuri'u fiye da miliyan 47.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasar a zaɓen watan Janairun 2027 bayan da ya lashe zaɓen fitar da gwanin jam'iyyarsa ta APC da kuri'u miliyan 47,654,907
Nan gaba a yau ne jam'iyyar za ta gabatar da Shugaba Tinubu a matsayin ɗantakararta na zaɓen 2027 bayan da ya doke abokin karawarsa, Stanley Ofiso a zaɓen fitar da gwanin da aka gudanar ranar Asabar a faɗin ƙasar.
Tinubu mai shekara 74 na kafa hujjar sake neman takara kan sauye-sauyen tattalin arziki da ya samar, to amma masu s**arsa na cewa matsalar rashin tsaro a arewacin ƙasar na iya zame masa babban ƙalubale a zaɓen.
A 2023 ne aka zaɓi Tinubu matsayin shugaban Najeriya, ƙasa mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka.
A nasu ɓangare su ma abokan hamayyarsa na shirin gudanar da nasu zaɓukan fitar da gwanin jam'iyyunsu domin tunkararsa a zaɓen an 2027.
24/05/2026
Trump yace shugabannin Iran a ranar yau sun dawo masa da kundin buƙatun yarjejeniyar dakatar da yaƙi a tsakaninsu, inda a cikin martanin data mayar Iran tace ko Duniya zata tashi ba zata miƙawa Amurka sinadarin Uranium ɗin data riga ta tace ba saboda hakan raini ni a gareta.
24/05/2026
"Motata ta taɓa ƙonewa lokacin da za mu tafi aikin wa’azi a Azare. Na rantse da girman Allah, kafin na isa garin har na manta cewa motata ta ƙone. Kuma ko minti 10 ba a yi da ƙonewar ba, bacci ya kwashe ni. Mota, riga ko gida ba sa burge ni. Babu abin da ke faranta mini rai face ganin an shirya aikin da’awa kuma ya yi nasara. Wannan Duniyar da kuke gani ba komai ba ce".
In ji Shaik Kabiru Gombe.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano
880000