VR Hausa

VR Hausa

Share

Photos from VR Hausa's post 06/08/2023

Alhamdulillah.
Bayan samun taimakon ku na yaɗa sanarwar ɓacewar waɗannan yara, Allah Ya nufe mu da samun ƴan uwan su, tare da miƙa Yaren gare su.
Mun samu damar damƙa yaran wa ƴan uwan su ne a chaji ofis ɗin ƴan sanda na Unguwar Rogo a gaban DPO da kuma Hajiya Kaltume Auwal, wato Amirar FOMWAN ta jihar Plateau.
Allah saka mu ku da alkairi a bisa taya mu yaɗa cikiyar da kuka yi.
Na gode.
Daga Harun Umar

Photos from Arewa Radio 93.1's post 04/08/2023
04/08/2023

Tashin Hankali: Kasar Nijar ta katse hulɗa da Najeriya

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yanke hulɗa da Najeriya da Togo da Amurka da kuma wadda ta raine ta, Faransa bayan tawagar da Ecowas ta tura don tattaunawa da sojojin da s**a hamɓarar da shugaba Bazoum ta gaza samun matsaya da sojojin.

A wani jawabi da ya yi ta kafar yaɗa labaran ƙasar ta Nijar, jagoran juyin mulkin, Kanar Amadou Abdramane ne ya sanar da matakin da ma wasu matakan da s**a ɗauka.

Ya ce “Mun kawo ƙarshen duk wata hulɗar jakadanci da Najeriya da Faransa da Togo da kuma Amurka. Duk wata matsaya da aka cimma a baya ta rushe.”

Tawagar da Ecowas ta tura don tattaunawa da sojojin Nijar ɗin a ƙarƙashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar ta gana da wasu daga cikin sojojin a ranar Alhamis amma ba a cimma wata matsaya ba, rahoton BBC

Manyan hafsoshin sojin ƙasashen Ecowas sun kammala wani taro a birnin Abuja, inda s**a tattauna yiyuwar ɗaukar matakin soji a kan Nijar idan sasanci ya gagara.

Daga Katsina Daily News

Photos from VR Hausa's post 04/08/2023

Ko ba komai duk wanda ya san Maryam Shetty ya san mutuniyar kirki ce. Ko mu da muke jam'iyyar adawa tana mutuntamu cikin nishadi da dariya. Ni ko sunana ba ta fada sai dai ta ce "kanina". Amma yan bakin ciki kuka dinga surutu karshe sai da s**a samu damar canjata da matar da a shekara hudunta tana kwamishiniya a karkashinta ba abin da aka yi sai rufe makarantu da gine gefunansu. A lokacin ilimi ya yi lalacewar da bai taba yi ba a tarihin jihar Kano. Yanzu sai ku ji dadi tun da ku matasa ku ne makiyan kanku.
Daga Aliyu Dahiru Aliyu

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Kano