Tubless Media Concepts
Par 3 Na so shi tsawon shekaru 10… amma daga ƙarshe ya ci amanata.
Fitacciyar mawakiya mai basira Shamsiyya Sadi ta bayyana mana yadda ta sadaukar da soyayyarta tsawon shekaru sama da 10 ga mutumin da take shirin aura… amma daga ƙarshe ya juya mata baya ya zaɓi rabuwa da ita. 😢
Ta bayyana irin kaɗaicin da ta shiga bayan ta rabu da kowa saboda shi… amma duk da haka ta tsaya da ƙafafunta, ta maida raɗaɗin rayuwarta zuwa waƙoƙin soyayya da yaudara da suke shiga zuciyar mutane.
A cikin wannan hira mai cike da gaskiya da tausayi, Shamsiyya Sadi ta bayyana:
💔 Dalilin da yasa take yin wakokin soyayya da yaudara
💔 Yadda cin amana ya canza rayuwarta
💔 Kalubalen da ta fuskanta a rayuwa
💔 Kasuwancin da take yi har ta samu tallafin ₦250,000 daga Rayuwata Talkshow
Ku kasance tare da mu domin kallon cikakken shirin nan bada jimawa ba.
YouTube Channel: Tubless Media Concept
🎥 Rayuwata Talkshow
Part 1 Na so shi tsawon shekaru 10… amma daga ƙarshe ya ci amanata.

07/06/2026
Mun samu tattaunawa ta musamman da Alhaji Sammani Fatihu — fitaccen ɗan kasuwar da ya yi suna sosai a kasuwar Kwari, wanda daga baya mutane s**a daina jin duriyarsa a harkar kasuwanci.
A wannan hira mai cike da darasi da ilimantarwa, ya bayyana mana dalilin da yasa ya hakura da kasuwa duk da irin nasarar da ya samu, tare da wasu bayanai masu ratsa zuciya akan neman kuɗi, rayuwar kasuwanci, da kalubalen da matasa ke fuskanta a yau.
Zaku ji yadda ya bayyana cewa ba kowace nasara ce take zuwa da nutsuwa ba, da kuma irin darussan rayuwa da ya koya bayan daukaka da jarabawa, darasi ne ga matasa, ‘yan kasuwa, da masu neman nasara a rayuwa.
Ku kasance tare da mu a cikin Rayuwata domin jin cikakken wannan tattaunawa mai matuƙar muhimmanci. A cikin YouTube channel dinmu mai suna Tubless Media Concept 🎥✨
11/05/2026
Cikin yardar Allah a yau nasaka Fatima Nafi'u Yusuf( Dahira) a makarantar sakandire ta Sheikh Bashir El Rayyah dake unguwar Goron Dutse,na biya mata kudin Makaranta tun daga SSS 1 har zuwa ta gama,na kuma siya mata litattatafan karatu da uniform,kazalika na damkawa mahaifiyar Dahira amanar Naira dubu 300 da al'umma s**a turo a matsayin tallafi.
Dahira itace wadda muka tattauna da ita, ta kuma bayyana cewar Marigayi Alhaji Aminu Dantata ya dauki nauyinsu ita da mahaifiyar ta zuwa aikin hajji,bayan tasamu lambar sa a internet.
Dahira ta bayyana min cewar bata da wani buri daya wuce cigaba da karatu,a madadin Shirin Rayuwata muna mika godiya ga Allah SWT daya bamu wannan iko.
Alhamdulillah Mungodewa Allah 😍🙏🏻
lamari mai ban al’ajabi tsakanin Fatima Nafiu da Alhaji Aminu Dantata, Labarin Rayuwar Fatima Nafiu Yusuf Dahira—yarinya da Allah Ya nuna ikonSa a rayuwarta ta hanya mai ban mamaki. Bayan rasuwar mahaifinta, ta fuskanci ƙalubale masu tsanani; rayuwa tsakanin jarrabawa, ya’u da gobe. Amma duk da haka, ta zaɓi farin cikin mahaifiyarta fiye da komai, ta jajirce da haƙuri da imani.
Wani abu mai girma da ya faru tsakaninsa da Fatima Nafiu Dahira wanda ya sauya wani ɓangare na rayuwarta, inda zaku ji yadda ya biya musu kuɗin aikin Hajji ita da mahaifiyarta da ƙanwarta, ba tare da sun sani ba.
Wannan labari cike yake da darasi, tausayi da ƙarfafa gwiwa—irin wanda ba ku taɓa gani ba a Rayuwata Talk Show.
🎬 Ku kasance tare da mu, sannan kuyi subscribe & follow na YouTube channel ɗinmu Tubless Media Concept domin kallon cikakken shirin.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Address
Zoo Road, Kano
Kano