Prince24

Prince24

Share

Photos from Prince24's post 06/02/2023

DÁ ƊUMÍ ƊUMÍ: Bóla Tìnúbú Ya Ziyarci Mahaifiyar Tsohon Shúgaban Nájeriya Marigayì Umar Musa Ƴar'adua.

Wane fata zakuyi masa

Photos from Prince24's post 09/12/2021

A Rana Mai Kamar Ta Yau 9 Ga Watan Disamba A Shekarar 2014, Allah Ya Yiwa Shahararren Dan Wasan Barkwanci Rabilu Musa, wanda aka fi sani da Dan Ibro Rasuwa.

An haife shi: 12 Disamba 1971, A Danlasan Da Ke Kano

Ya rasu: 9 ga Disamba, 2014, A Kano

Ya Bar Ya'ya: 7

Da mata 3

Allah ya gafarta masa.

©: B Salia

08/12/2021

Ƙasar Saudiya ta haramtawa 'Yan Najeriya shiga ƙasar ta kai tsaye saboda sabuwar cutar Corona ta Omicron.

Gwamnatin ƙasar Saudi Arabiya tabi sahun wasu kasashen duniya wajen hana jiragen sama da s**a tashi daga Najeriya shiga kasar sak**akon samun wasu mutanen dake dauke da sabon nau’in cutar korona da ake kira Omicron.

Wannan mataki na zuwa ne kwana biyu bayan Birtaniya da Canada sun haramtawa baki daga Najeriya shiga ƙasar su sak**akon samun masu dauke da cutar.

Rahotanni daga birnin Kano sun ce yanzu haka maniyata Umrah da dama sun makale a birnin sak**akon wannan mataki da Saudiyar ta dauka, yayin da jami’an kula da tashohin jiragen saman Malam Aminu Kano s**a tabbatar da samun umurnin hana jirage tashi zuwa kasar.

Wata matafiya da yanzu haka take birnin Kano akan hanyar ta na zuwa Umrah Tabbatar da cewar gwamnatin Saudiya ta soke tafiyar su daga Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta jiyo ta bakin wani jami’in ofishin Jakadancin Saudiyar dake Kano na cewar tabbas sun samu umurnin hana jiragen sama daga Najeriya tafiya kasar.

Sai dai Jaridar ta ruwaito cewar duk da wannan umurnin, wani babban jami’in kamfanin jiragen sama ya shaida mata cewar jirage biyu sun tashi yau da safe daga Abuja zuwa Jeddah wadanda s**a hada da Qatar Air da Badar Air.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Getso Bakin Kasuwa Gwarzo LG Along Karaye Road
Kano