Idris m yahaya

Idris m yahaya

Share

11/04/2023

Aƙalla ita Ɗariƙa, in ka riƙa ta, Kanā Azkāran ta, Zã ta wanke Zuciyar ka, ta ɗebe maka Nafsu, Kamar yadda Aka sani Halarori Biyar nẹ, to haka Muqãmin Ruhi shi ma Biyar ne, da SIRRU, Sai RUHU, sai QALBU, sai AQLU, sai NAFSU. Kamar Ace HAHUTU, LÃHUTU, JABARUTU, MALAKUTU DA NÃSUTU..

Saboda Haka, Ta Hanyar Kãma Azkārai, ayi tarbiyya, shi ɗai Kãsa kayi Fanā'i, Fanā'i cikin Halarar Farko ta Afālu, Kayi Fanā'i cikin Halara ta Biyu Halarar Sifãtu, ta Muhammadiyya, kayi Fanā'i cikin Halarata Ukku,ta Asmã'u, Halarar Ahmadiyya, sai kayi Fanā'i cikin Halarar Zãti, Halara ta Huɗu, Halara ta Ubudiyya, har kayi Fanā'i cikin Halara ta Biyar, Halarar Qudsiyya..

In ka Gama Waɗannan Halarorin, ka kãma Azkāran da ya kamãta, kullum Sirrin su Zai rinƙa Bayyana cikin Zuciyar ka, Amma da Sharaɗin, Halarar da Kake Ciki ta Zãmanin ka, Kayi Fanā'i cikin ta, in Baka yi Fanā'i cikin ta ba, to waɗancan Bãsu da Amfani gareka, in Kayi Fanā'i cikin ta, Sai ta jãwo ma waɗancan Halarorin, ta Gwada maka Sirrin su, ka ƙãru, Sannan ka Cigaba da Tafiya... Tafiya Cikin Allah Bata da Iyãkã.

Shehu Aliyu Bunza Sokoto قدس الله سر

Sufi path: Qudsiyya Aliyya Sufiyya

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Fambegua
Kano