Usman Shehu Jaa
Hakika an yiwa dimokradiya mahangurba, kuma an wulakantar da mutunci, kwarjini da karfin iKon judiciary a kasar nan.
Alkalai da kotuna sune dama ta karshe da mai hakki ko Wanda aka zalunta suke da ita domin Kai kokensu bisa tsammanin samun adalci. Amma Kash, a yau alkalai da duk wani tsari na shari'a an karya shi, martaba da tasirin alkalai ya fadi kasa warwas.
Hukuncin karshe na Shari'ar Kano babban misali ne ga mawuyacin halin da demokradiya ta fada ciki, tare da tauye duk wani yanci da kotunoni ko alkalai suke dashi don wanzuwar adalci.
Hukuncin Shari'ar Kano a yau cikakken misali ne da ke nuna gurbacewar al'amuran siyasa a kasar nan musamman ta fuskoki guda biyu:-
1. An budewa Jam'iyun siyasa a nan gaba kofar yin magudi da chusa kuri'un bogi a lokutan zabe,domin Koda anje kotu zasu iya tsira.
2. An tauye hakki da yancin masu zabe, domin anan gaba ma mutane zasu Dena wahalar da kansu fita yin zabe. Domin suna zabar abinda sukeso, wasu suna aringizo da chushen kuri'a ana basu.
3. A nan gaba mutane bazasu dinga damuwa da cika duk wasu ka'idoji na tsayawa takara ba, domin kuwa kotu da alkalai a hukuncin kotun koli sun tabbatar da hakan. Kuma sun yiwa duk wata dokar zabe Karan tsaye, Wanda hakan dabawa kansu wuka ne sukayi domin anan gaba basu Isa suyi hukunci da ya sabawa wannan ba. Suma zasu kuka da kansu.
4. Ba'ayi adalci ba a hukuncin Kano, domin kuwa mao sharia Babu wata doka ko reference da ya dogara dasu wajen yanke hukuncin Kano, kawai ya karanto bayanansa a matsayin raayi, kamar yadda ya bayyana kuma yayi mana hukunci da raayinsa duk da cewa alkali ne, Amma ya maida Kansa baya, ya yarda ya nuna.rashin kwarewa, ya lalata image na sharia saboda son zuciyarsu.
Daga karshe zamu zo da bayanai masu yawa kan duk wasu kulle kulle da akayi akan wannan sharia Wanda har yasa AKAI wannan danyen hukuncin.
yin hakan bazai haifar da kowace irin matsala ba domin Koda kotu akaje barawon kuri'u zai iya tsira de
tabbatar da irin halin innanillahi wa Inna ilaihir raji'un da aka samu Kai a ciki ta fuskar abubuwa guda biyu
10/12/2023
We voted for GAWUNA/GARO
27/11/2023
Kano Nowadays
Akwai wata karin magana da Hausawa ke cewa "mugun nufi baya kashe ɗan barewa"
daga 1999 zuwa ynx duk irin turin jeka ka mutu da bita da ƙulli da mutumin nan yake yiwa Ganduje saida Allah ya hayar dashi kuma ya bashi Nasara akan sa.
Baiso ya zama gwamna ba amma Allah ya hukunta kuma duk da cewa Ganduje yasan da hakan bai Dena yi masa biyayya ba.
idan ka ɗauki dalilan rabuwar su ɗaya bayan ɗaya babu inda zaka ce Ganduje ke neman sa da sharri, hasali baya iya mayar masa da martani, Saida tura takai bango.
Mutumin nan a hirar da yake ta awa 2 zuwa 3 minti 50 zuwa awa ɗaya yana ɓatasu ne a yarfe, ƙazafi, cin mutumci da yiwa Ganduje habaici. Kuma kowa yasan haka amma saboda Dattaku na Baba Ganduje yana matsayin number 1 citizen a jiha kamar Kano, amma baya iya tanka masa.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
No 7 Gama D
Kano