NURA AHMAD

NURA AHMAD

Share

30/10/2025

Acigaban da wahalar mai da Mali tashiga Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Janar Abdurahmane Tchiani ya bayar da umarnin tura tankoki 100 shaƙe da man fetur zuwa Mali domin taimaka wa mahukuntan wannan ƙasar da ke cikin ƙawancensu na AES magance matsalar ƙarancin man da ta ke fuskanta a ƴan kwanakin nan.

Ƙarin bayani: https://www.facebook.com/profile.php?id=100080256788524

30/10/2025

Dadumi dumi shugaban ƙasar China Xi Jinping ya kammala gana wa da takwaransa na Amurka Donald Trump, a birnin Busan na Koriya ta kudu, inda s**a yi musanyar ra’ayoyi kan batutuwan da suke jawo rikice-rikicen kasuwanci tsakanin ɓangarorin biyu.

Karin bayani: https://www.facebook.com/profile.php?id=100080256788524

Photos from B S Y HAUSA's post 30/10/2025

Wani babban al'amari Donald Trump Ya Ba Da Umarnin Fara Gwajin Makaman Nukiliya Saboda Barazanar Rasha Da China.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarni ga Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar (Pentagon) ta fara sake gwajin makaman nukiliya, yana mai cewa ya dauki wannan mataki ne saboda gasa da ake yi da Rasha da China a fannin makaman kare dangi. Trump ya bayyana hakan ne kafin taronsa da Shugaban China Xi Jinping a Busan, Koriya ta Kudu, inda ya ce “Amurka tana da makaman nukiliya fiye da kowace ƙasa, kuma na sabunta su gaba ɗaya a wa’adina na farko.

Ban so yin hakan ba, amma babu wani zaɓi.” Ya kara da cewa saboda gwaje-gwajen da wasu ƙasashe ke yi, ya umarci Ma’aikatar Yaƙi ta fara gwaji nan take. Amurka ta dakatar da irin waɗannan gwaje-gwaje tun 1992, amma yanzu Trump na neman janye wannan moratorium.

Rahoton SIPRI ya nuna cewa Amurka tana da makaman nukiliya 5,177, Rasha 5,459, yayin da ake hasashen China za ta kai 1,500 nan da 2035. Wannan mataki na Trump ya dawo da tsoron sabon yarjejeniyar makaman nukiliya a duniya.

29/10/2025

Mai girma Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Maryam Sanda wadda ke zaman jiran hukuncin kisa bisa samun ta da laifin kashe maigidanta.

Wannan na ɗauke a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Tinubu kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar.

A farkon watan Oktoba ne dai shugaba Tinubu ya yi wa wasu mutum 175 afuwa da s**a haɗa da matattu da masu rai.

29/10/2025

Bayan kazamin harin Hukumomin lafiya a Gaza sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 63 ciki har da ƙananan Yara, a jerin hare-haren da dakarun Isra'ila s**a kai cikin dare, lamarin da ake ganin ya saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla ƙarashin jagorancin Amurka.

Karin bayani: https://www.facebook.com/profile.php?id=100080256788524

28/10/2025

B S Y HAUSA Duniyace Sahihin Labarai cikin gaskiya da Aminci Kuyi Following dinmu domin jaddada soyayyarku ga harshen Hausa
https://www.facebook.com/profile.php?id=100080256788524

Want your business to be the top-listed Food & Beverage Service in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Anuraddeen670@gmail. Com
Kano