Barca Hausa

Barca Hausa

Share

12/07/2026

🚨✅️|Fermín López na ci gaba da samun gagarumin ci gaba a shirin murmurewarsa karkashin kulawar ƙwararren mai jinya José Cortés.

⏳ Fermín yana samun sauƙi cikin sauri sosai, wanda ya sa Barcelona ke sa ran zai koma atisayen gama-gari tare da sauran 'yan wasa nan ba da jimawa ba.

🔜 Hasashen kulob ɗin shi ne zai iya komawa horo tare da tawaga cikin kusan makonni biyu.

⚽ Har ma akwai yiwuwar ya samu wasu mintuna a wasan sada zumunci da Birmingham City a ranar 31 ga Yuli.

✅ A cikin Barcelona akwai babban fata cewa Hansi Flick zai samu damar amfani da Fermín tun daga farkon kakar wasa.

12/07/2026

💰 Barça na neman yuro miliyan 50 a kan Ferran, Inda take kafa hujja da ƙwarewarsa ta cin ƙwallaye da kuma darajarsa a matakin ƙasa da ƙasa.

❌ PSG na ganin kuɗin sun yi yawa, kuma tana son ta biya ƙasa da €40 million. ~ Diario Sport

12/07/2026

✍️ Cikakken Bayani:

"Da farko, Alƙalin wasa ya bai wa Leandro Paredes katin gargadi (Yellow Card) saboda ƙetar (Foul) da aka ce ya yi wa Embolo.

Sai dai daga baya, VAR ta sanar da alƙalin wasa ya sake duba lamarin, Bayan an gano cewa Embolo ya yi faɗuwar ƙarya ne (simulation) domin ya yaudari alƙali.

Bayan kallon hoton da aka maimaita, Alkalin ya soke katin gargadin da aka bai wa Paredes, Sannan ya bai wa Embolo katin gargadi saboda faɗuwar ƙarya da yayi domin yaudara.

Tun da Embolo ya riga ya samu katin gargadi a baya, Wannan ya zama katinsa na biyu, Wanda haka ya sa aka ba shi jan kati kuma aka kore shi daga wasan. 🟥

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address


Kano