Ac Zaid Moha
09/03/2025
Shugaban addini na Iran, Ali Khamenei, ya yi watsi da tattaunawa da Amurka a karon farko tun bayan da Shugaba Donald Trump ya yi ikirarin tura masa wasika kan batun tattaunawar nukiliya.
Khamenei ya kuma soki kasashen Faransa, Jamus, da Birtaniya saboda s**a da s**a yi wa Iran kan rashin bin ka’idojin yarjejeniyar nukiliya ta 2015, yana mai cewa kasashen sun nuna rashin kunya.
Da yake jawabi a wajen wata ganawa da jami’an Iran a Tehran a ranar Asabar, Khamenei ya jaddada cewa Iran ba za ta amince da bukatun Amurka ba.
“Duk da cewa wasu gwamnatoci masu danniya na matsa lamba kan tattaunawa, ba don warware matsaloli suke so ba, sai don su nuna iko da kakabawa mutane bukatunsu,” in ji Khamenei. “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta amince da bukatunsu ba.”
Ya kara da cewa, “Wadannan kasashe uku—Faransa, Jamus, da Birtaniya—na fitar da sanarwa suna zargin Iran da rashin cika alkawuran yarjejeniyar JCPOA! Akwai bukatar a tambaye su: Ku kun cika alkawarinku kuwa? Tun farko ba ku cika ba! Daga nan sai ku yi wani ikirari sannan kuma ku karya wannan alkawarin na biyu. Ya kamata a samu iyaka ga rashin kunya! Ta yaya mutum zai gaza cika alkawuransa amma ya juya yana zargin daya bangaren da rashin bin ka’ida?”
Wannan furuci na Khamenei ya zo ne bayan Trump ya bayyana cewa ya aika wasika yana ba da tayin tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran, tare da gargadin cewa harin soja na daya daga cikin zabinsa.
10/09/2023
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Kano
Kano