Vanguard Hausa
01/06/2026
Gwamnatin Tarayya Ta Fara Ƙarfafa Tsaron Dazuzzuka: Jihohi 10 Na Arewa Sun Riga Sun Dauki Masu Tsaron Daji 1,000-1,000
Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yada Labarai ga Shugaban Ƙasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya yi karin haske kan shirin ɗaukar masu tsaron daji (Forest Guards) 1,000 a Jihar Oyo, yana mai bayyana cewa wannan ba wani tsari ne na musamman ga yankin Kudu maso Yamma ba.
A cewarsa, tun kafin shirin na Oyo, jihohi 10 sun riga sun kafa rundunar masu tsaron daji, kuma mafi yawansu jihohin Arewa ne. Ya ce kowace jiha ta dauki kusan mutum 1,000 domin taimakawa wajen magance matsalolin tsaro, musamman satar mutane da hare-haren da ke faruwa a dazuzzuka.
Jihohin da s**a riga s**a kafa rundunar Forest Guards sun hada da Borno, Yobe, Adamawa, Kwara, Sokoto, Kebbi, Niger, Plateau da Benue.
Haka kuma, ya bayyana cewa jihohin Kaduna, Edo, Kogi da Bauchi suna kan hanyar aiwatar da irin wannan shiri.
Malam Abdulaziz ya jaddada cewa manufar shirin ita ce ƙarfafa tsaro a dazuzzuka da kuma taimakawa jami’an tsaro wajen dakile ayyukan masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka.
Zamu Bayanna Wanda Yayi Nasara a Zaben Shugaban Kasa na Gwaji da mukayi a jiya
Wanda Bai yi Zabe Ba Ga link 👇
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano